ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 57( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Musulmi Sun Jure Wahala
Wadanda muka fadi a baya ba su
kadai ne suka sha wahala ba. Kusan
duk wanda ya shiga musulunci a
wancan lokaci kome matsayinsa sai
da ya dandani wahala kuma ya jure
ma ta. Kafin mu karkare wannan
zance sai mun kara kawo wasu
misalai:
1. Khabbab bn Al-Arat:
Makeri ne da yake karkashin wata
muguwar mata ana ce da ita Ummu
Anmar daga kabilar Khuza’ata. Taron
dangi aka yi a kan sa ana azabta shi
har sukan kwantar da shi rairan
(bayansa na kasa kirjinsa da
fuskarsa na sama) a kan duwatsu
masu zafi. Da wannan matakin ya
kasa yi masu amfani sai Ummu
Anmar ta dauko wani karfe mai zafi a
makerarsa ta yi masa lalas da shi a
ka. A nan ne fa ya je ya kai kara
wajen ma’aiki (SAW). Manzon Allah
(SAW) babu abinda zai iya yi masa a
wannan lokaci sai addua. Addu’arsa
kuwa ba ta faduwa a kas. Da Allah ya
karbi addu’ar manzonsa sai wannan
mata ta fara ciwon kai. Wasa-wasa
ciwon yai ma ta tsanani har ya fara
sa ta hauka. Duk maganin da aka ba
ta sai ta ji shi kamar garwashi a
kanta. Ta rinka hafshi irin na karnuka
har ta fara damun mutane. Sai aka ba
ta shawarar ta yi lalas!
Ka ga ikon Allah! Da kanta ta kira
Khabbab ta ce ya taimake ta da
wannan magani. Khabbab ya dauko
karfen nan ya hasa wuta ya gasa shi
yadda ya kamata. Sannan ya dauko
shi ya rinka dadara ma ta shi a ka
tana ihu.
Ya kake zaton imanin Khabbab game
da Allah da manzonsa bayan faruwar
wannan abin al’ajabi mai nuna cikar
ikon Allah? Za ka yarda Khabbab da
ire-irensa da suka rungumi
musulunci a irin wannan lokaci
munafukai ne? To, wa zasu
munafurta? Kuma don su cim ma
me?
Kafirci bala’i! Faruwar wannan aya
bai sa musulmi suka samu sararawa
daga kunci da azaba ba. Watarana
sai da Khabbab ya je ya samu
manzon Allah (SAW) ya ce, ya
manzon Allah! Me zai hana ka nema
mana taimakon Allah, ka yi mana
addu’a? Wannan roko na nuna
matukar damuwa da raki wanda bai
dace da matsayin makusantan
annabin Allah ba. Kuma ita sunnar
Allah ba ta canzawa. Don haka
Manzon Allah (SAW) ya bata rai
matuka. Yana kishingide a inwar
Ka’aba sai ya tashi zaune. Sannan ya
ce ma sa: “A can baya, an yi lokacin
da ake zuwa da mutum a tona masa
kabari a kafe shi sannan a zo da
zarto a tsaga jikinsa daga tsakiyar
kansa zuwa karkashin kafafunsa.
Wani kuma a yi mashaci da karfe
tsakanin tsokarsa da qashinsa. Duk
wannan bai hana su yin addini ba.
Wallahi, Allah zai cika addinin nan
nasa har matafiyi ya bar San’a’a ya je
Hadramaut bai jin tsoron kowa sai
Allah, sai kuma tsoron kura ta kama
awakinsa ba dai mutum ba. Amma ku
kun cika gaggawa”.
Da haka aka kafa addini a kowace
al’umma. Dole ne a samu masu
sadaukar da rayukansu da lafiyarsu
da jin dadinsu don daukaka addini a
farkon lamarinsa. Wadannan kuma
Allah da kansa ne yake zabar su.
A zamanin khalifancin Umar (R.A) an
taba tada zancen wahalhalun da aka
sha a baya sai sayyidina Umar ya ce
a kira Khabbab ya nuna ma mutane
bayansa. Sai suka ga abin kuka
musamman bayan da ya rinka hikaito
masu yadda ake hasa wuta a
makerarsa, a kwantar da bayansa a
kanta har sai ta huce.
Duba: Ar-Raud Al-Unuf na Suhaili,
2/98 da Sahih Al-Bukhari, 3612 da
Mihnat Al-muslimeen Fi Al-Ahd Al-
Makkee, na Dr. Sulaiman As-
Suwaikit, shafi na 95.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories