ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 60( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tsakanin Musulmi Da Kafiran Makka:
Tura Ta Kai Bango
Wani abin ban sha’awa ga wadannan
bayin Allah shi ne, dukkaninsu suna
jin zafin abinda ke faruwa ga ‘yan
uwansu ko da kuwa kome bai same
su ba. Abinda zai nuna maka wannan
shi ne, labarin Usman bn Maz’un
(R.A) wanda aka hana shi shiga
Makka sai da izni da garkuwar Walid
bn Mughirah. Bayan haka ya wayi
gari yana shiga duk inda ya ga dama
a cikin Makka babu wanda yake ce
ma sa uffan albarkacin wannan
garkuwa da Walid ya ba shi. Amma
kuma zuciyarsa na konuwa a kan
abinda ‘yan uwansa suke sha na
wahala da azaba. Har sai ya fara
tuhumar imaninsa. “Ta ya ya musulmi
duk suke shan wahala, ni kadai ina
sakewa? Kuma wai a kan garkuwar
arne, makiyin Allah da manzo?” Haka
zuciyarsa da rinka cewa. Daga nan ya
dauki alwashin rayuwa ba za ta ci
gaba a haka ba. Ganin ba zai iya
dakatar da azabar da ake yi ma
musulmi ba sai kawai ya je wajen
Walid bn Mughirah ya ce ma sa, ya
baban Abd Shams! Duk yadda ake
taimako ka yi, kuma na gode. Amma
garkuwarka ka janye kawai ba ni
bukata. Walid ya ce, me ya faru? Ko
wani ne ya tunzura ka, ko ya taba
mutuncinka? Usman ya ce, sam.
Kawai dai haka nake so, domin
garkuwar Allah ta ishe ni. Abin ka da
maketaci, sai Walid ya ce ma sa to,
mu je can mahadar jama’a mana a
daidai dakin Ka’aba sai ka shelanta
ma mutane ka wadatu daga
garkuwata. Usman ya shiga gaba
Walid yana bin sa. Da suka je kuwa
ba wani haufi Usman ya gaya ma
jama’a shi ya nemi Walid ya janye
garkuwarsa.
Ba a dauki wani dogon lokaci ba sai
‘yar gardama ta shiga tsakaninsa da
Labid bn Rabi’ah, wani fitaccen
mawaki kuma bako a garin makka.
Labid ya nemi agaji ga mutane. Wani
ya ce ma sa ka yi hakuri. Wannan na
cikin wawayen gari wadanda suka yi
tawaye ma addinin iyaye. A nan ne fa
rigima ta kaure. A cikin haka har
wani ya dauke Usman mari sai da
fuskarsa ta yi ja wur. Walid ya ce ma
Usman ka ga irin abinda nake gaya
ma. Ka halaka idonka a banza. Ka
dawo kawai a in sake yi maka
garkuwa. A cikin fushi Usman ya ce
ma sa, wallahi ba ni bukata. Kuma
daya idona ma na da bukatar abinda
ya sami yar uwarta saboda Allah.
Wannan yana nuna karfin imaninsa
da kwadayinsa ga lada. Babu shakka
kuwa ya same ta. Domin ko bayan
mutuwarsa Ummul Ala’i ta yi mafarkin
ta gan shi da wata korama ta ruwa
mai gudana. Sai ta fada ma ma’aiki
Sallallahu Alaihi Wasallam. Ya ce
“wannan aikinsa ne”. Sahih Al-
Bukhari, hadisi na 7004.
Duba kuma Al-Asas Fis Sunnah na
Sa’id Hawa (4/2010-2012) da Tarikh
Al-Islam na Dhahabi (1/112) da
Mausu’at As-Siyar na Sallabi, shafi
na 160-161.
Yanzu kam misali daya ya rage mu
kawo sai mu cira zuwa wani fasali.
Mun tsawaita wannan bayani ne don
masu hankali su san girman
wadannan mutane da Allah ya zaba
ma manzonsa. Mai tunanin cewa,
wani abin duniya na karkata zukatan
wadannan bayin Allah daga bin Allah
da manzo bai yi nazarin tarihinsu ba.
Allah ya yi muna dace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 60( Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Abdullahi Yakubu Avatar
    Abdullahi Yakubu

    Allahu akbar

Leave a Reply

Latest updates
Categories