ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wasallam
Fitowa ta 11
Matsayin Birnin Makka da Darajarsa
Kamar yadda Allah ya zabi wasu
mutane ya ba su fifiko a kan wasu,
haka su ma garuruwa da birane Allah
ya fifita wasu a kan wasu. Idan kuwa
ana maganar kasashe da manyan
biranensu to, Makka ita ce “Ummul
Qura” uwar birane da nassin Alqur’ani.
(Suratul An’am: 92 da Suratus Shura:7)
Gari ne da Allah ya sanya aminci da
kwanciyar hankali a cikinsa. Alkibla ce
ta musulmi a duk inda suke a duniya.
Zukatan muminai a ko ina suna karkata
zuwa ziyarar sa, kuma idan sun koma
gidajensu nan take sai su bukaci
komawa. (Suratul Baqarah:125) A nan
ne dakin Allah na farko da aka gina
don ibada yake. A jikinsa akwai
“Hajarul Aswad” daga cikin duwatsun
aljanna.
{ ﺇﻥ ﺃﻭﻝ ﺑﻴﺖ ﻭﺿﻊ ﻟﻠﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻱ ﺑﺒﻜﺔ ﻣﺒﺎﺭﻛﺎ
ﻭﻫﺪﻯ ﻟﻠﻌﺎﻟﻤﻴﻦ * ﻓﻴﻪ ﺁﻳﺎﺕ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻣﻘﺎﻡ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ
ﻭﻣﻦ ﺩﺧﻠﻪ ﻛﺎﻥ ﺁﻣﻨﺎ { )ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ: 97،96 )
Shi ne kadaitaccen wuri da aka amince
ma musulmi ya shafa da sunan ibada.
Sallah a wannan gari tana da karin
matsayi sama da ninki 100,000 a kan
wani gari duk da ba shi ba.
Ba a zubar da jini a birnin Makka, ba a
farauta ko tada hankalin tsuntsu balle
bil-Adama. Ba a cire ganye daga
bishiya, ba a daukar tsintuwa sai idan
za a cigita. (Suratun Naml:91).
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi
daga Ibnu Abbas (RA) daga manzon
Allah (S) cewa, Allah ya haramta
Makka, bai taba halalta ma kowa yaki
a cikinta ba gabani na, haka ma ba zai
halalta ma kowa ita ba a baya na. Ni
ma awa daya ce daga cikin wuni aka
halalta ma ni. Don haka, ba a tsinke
ganyenta, ba a yanke bishiyarta, ba a
korar dabbar farauta a cikinta, ba a
daukar tsintuwarta sai ga wanda zai yi
cigiya”. Sai Abbas (RA) ya ce “ban da
Idhkhir; bishiyar da muke yin rini da
ita, kuma muke amfani da ita wajen
rufe gawawwakinmu”. Sai manzon
Allah (S) ya ce, to ban da ita.
Albarkacin addu’ar annabi Ibrahim
(AS) a kullum ana samun kowane
nau’in abinci da kayan marmari a birnin
Makka. (Suratul Baqarah:126) A
karshen zamani kuwa idan Dujal ya
bayyana, Allah zai tsare wannan birnin
daga kazantar takon kafafunsa kamar
yadda ya tsare shi daga sharrin
rundunar giwaye (Zamu yi maganar
wannan runduna a nan gaba kadan in
Allah ya so).
Bukhari da Muslim sun karbo hadisi
daga Anas dan Malik (RA) daga
manzon Allah Sallallahu alaihi
Wasallam cewa, “Babu wani gari da
Dujjal ba zai shiga ba sai Makka da
Madina. A lokacin bayyanarsa babu
wata kafa a cikinsu (Makka da
Madina) sai Mala’iku sun yi sahu a kai
suna kare su. Sannan Madina ta yi
girgiza uku da mutanen da ke cikin ta.
Duk wani munafiki ko kafiri sai ya
fita”.
A wannan tsarkakakken gari ne aka
haifi shugabanmu kuma shugaban
ma’aika Muhammadu dan Amina,
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates