ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 18
Damana ta Kusa Kamawa
Shaiba (wanda aka fi sani da
Abdulmuttalib) ya haifi ‘ya’ya goma
sha shida; Goma maza, shida mata. Ga
jerin sunayensu:
1. ‘Ya’ya maza
– Harisu
– Zubairu
– Abu Talib
– Abdullahi
– Hamza
– Abu Lahabi
– Gaidaqu
– Muqawwam
– Safari
– Abbas
2. ‘Ya’ya mata:
– Ummu Hakim
(Ana ce ma ta Baidha’u. Kuma ita ce
tagwan Abdullahi mahaifin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam).
– Barratu
– Atika
– Safiyyah
– Arwa
– Umaima
An ba da labarin cewa, a lokacin da
Abdulmuttalib ya tona rijiyar Zamzam
ya sha wahala kwarai da gaske. Ba
domin ma hakuri da juriyar da ya yi ba
da aikin bai kammala ba. Saboda haka
ya yi ma Allah alkawali cewa, idan ya
samu ‘ya’ya goma mazaje kuma duk
suka girma suka isa taimakon sa zai
sadaukar da daya daga cikin su ya
yanka shi saboda Allah. Allah kuwa
cikin hikimarsa sai ya ba shi abin da ya
yi guri na samun ‘ya’ya maza goma har
da karin ‘ya’ya mata guda shida don ya
jaraba shi. Da mazajen suka girma sai
ya tara su gaba daya ya sanar da su
wannan alwashi da ke kansa, suka ce
ma sa to, bismillah. Abdulmuttalib ya
dauke su gaba daya ya je da su wurin
da suke kuri’a domin a fitar da wanda
za a sadaukar da shi a yanka. Kuri’a
kuwa sai ta fada kan Abdullahi. Don
haka ya dauki wuka ya janyo dan nasa
zuwa wurin Ka’aba. Abinka da fitaccen
mutum mai halin kirki, ganin haka sai
duk mutanen Makka suka fito suka ce
sam ba su amince ba. Ya zaka dubi dan
da ya fi kowa biyayya gare ka, ya fi
sanyaya ma mutane sannan ka ce zaka
yanka shi? Abdulmuttalib ya ce to, ya
zan yi da alwashina?! Ala tilas aka
nemi fatawa daga wurin wata bokanya
(kamar yadda yake a al’adarsu can
zamanin jahiliyyah) sai ta ce, a je ayi
kuri’a tsakanin Abdullahi da adadin
rakuman da ake bayarwa diyya idan an
yi kisan kai bisa kuskure. Idan kuri’a ta
fada a kan rakuma shikenan sai a
yanke su a madadinsa. Abdulmuttalib
kuwa ya ba da rakuma goma cif aka yi
kuri’a sai ta fada kan wannan bawan
Allah; Abdullahi. Aka ce a kara wasu
goma, ta sake fadawa a kan sa. Ba su
gushe ba suna kara rakuma goma goma
har sai da suka kammala rakuma dari
cif sannan kuri’a ta fada a kan su. To,
ka ji yadda aka yi diyya ta tashi daga
rakumi goma zuwa rakumi dari tun
kafin bayyanar musulunci. Addinin
musulunci kuwa da ya zo sai ya sa
hannu a kan haka.
Zamu ci gaba in Allah ya so.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates