ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 65( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Majalisi Na 65
Musulmi Sun Kaura Zuwa Habasha
Kamar yadda muka gani a baya, tura
ta kai bango; hakurin musulmi ya
kusa karewa, kuma babu wata alama
da ke nuna mushrikai za su karkato
su bari ayi addini ba tare da takura
ba. Don haka Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam sai ya fara
tunanin mafita ita ce, musulmi su
nemi wani waje da za su sarara; su
yi bautar Allah a cikin natsuwa. A
cikin watan Rajab na shekara ta biyar
ne manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya umurci wasu kadan
daga cikin sahabbansa da su yi kaura
zuwa kasar Habasha, kasar da teku
ya raba ta da tsibirin larabawa.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce da su, ku je can ku
bauta ma Allah, domin sarkinsu adili
ne; wanda bai bari a ci zalun kowa a
kasarsa. Sun fita su goma mazaje.
Hudu daga cikin su suna tare da
matansu, a karkashin jagorancin
Usman dan Affan wanda shi ma yana
tare da matarsa; Ruqayya ‘yar
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Da jin labarin fitar su sai
mushrikai suka yi sauri suka tura
runduna ta musamman domin a dawo
da su. Amma ina! Allah ya taimake
su. Domin kuwa isar su ke da wuya
sai suka tarar wani jirgi ya iso gabar
teku yana jiran fasinja. Sai suka
dauki hayar sa gaba daya a kan rabin
dinari, suka biya. Nan take aka
sukwanya da su kafin isowar
rundunar Quraishawa. Fathul Bari
(7/187-188).
Abin mamaki shi ne wannan ayari na
farko da manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya tura su gudun
hijira a Habasha, da ma babban ayari
da zamu gani a nan gaba ba mutane
ne masu rauni wadanda keshan
wahalar ta sosai ba. Misali babu
bawa ko karamin yaro ko sauran
wadanda muka fadi an azabta su a
can baya cikin wannan ayari, sai fa
Ibnu Mas’ud. Amma a cikin su babu
irin su Bilal da Suhaib da Khabbab
da Ammar da makamantan su.
Wadanda ke cikin ayarin galibi
manyan mutane ne masu dangi
kamar Usman bn Maz’un da Zubair
bn Awwam da Abdurrahman bn Auf
da Abu Salamata da sauran su. Haka
ma shi kansa jagoran tafiyar; Usman
bn Affan. Daga bisani Abubakar
Siddiq shi ma ya yi azmar zai cim
ma su har sai da ya kai “Bark Al-
Gimad” wani babban mutum ana ce
da shi Ibn Ad-Dighinnah ya hakurtar
da shi, ya dawo da shi Makka da
sharadin zai ba shi kariya. Dalilin da
ya sa kenan wasu manazarta ke
ganin ba an tura su ne kawai gudun
hijira don su tsira da addininsu ba.
A’a, akwai wannan dalili. Amma akwai
kuma wasu manufofi na siyasa da na
da’awa. Ma’ana dai ana son a isar da
sakon musulunci zuwa kasar waje.
Sannan kuma a samo bayanai da
zasu taimaka wajen gano in da za a
kafa daular musulunci ta nan gaba.
Fi Dhilal Al-Qur’an na Sayyid Qutb
(1/29).
Babu wani abin mamaki a cikin
wannan idan muka yi la’akari da
cewa, Habasha na cikin wuraren
kasuwancin Quraishawa, kuma a
dalilin wannan hijirar ne sarkin kasar
tare da wasu mutane da dama suka
musulunta. Kuma ko bayan da aka
samu aminci ta hanyar kafa birnin
musulunci a Madina manzon Allah ya
bar wadannan mutane a can Habasha
suna yada addini har sai da aka zo
yakin Khaibar a shekara ta shida
bayan hijira. Abin da ya sanya da
yawan wadanda suka yi hijira ta biyu
ba su halarci manyan yakoka irin su
Badar da Uhud da Khandaq da
Hudaibiyyah ba saboda suna can a
fagen yada da’awa a waccan kasa.
Al-Manhaj Al-Haraki Lis-Sirah na
Munir Al-Ghadban (1/67-68).
Bugu da kari kuma, Habasha ita ce
kasa tilo wadda annabi Sallallahu
Alaihi Wasallam yake so Allah ya ba
shi damar yin kaura zuwa gare ta. Ko
don yana da dadaddiyar masaniya ne
a kan kasar? Ummu Aiman – wacce
ta yi renon sa – ‘yar kasar Habasha
ce. Ko kuma don labarin sarki adili
da ke mulkin can a wancan lokaci?
Ko kuma don kasar tana kan addinin
kirista ne? Duka wadannan dalilai
suna iya kasancewa. Domin Allah ya
fada mana cewa, kiristoci sun fi kowa
saukin jawuwa zuwa ga gaskiya idan
suka ji ta kuma suka fahimce ta.
Suratul Ma’ida: 82. To, ko da yake
can din ne annabi yake so, amma
kuma madaukakin sarki ba haka ya
tsara ba. Hijirar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam da kafa
gwamnatinsa ta farko gwanin sarki
Allah ya tsara su ne a Madina, kuma
har ya wasafta wannan birnin a cikin
At-Taura, Yahudu suka tare can suna
dakon zuwan sa. A can ne Allah ya
kai manzonsa, Yahudu suka yi iya
jayayyar da suke iyawa da kulle-
kullen makircinsu, amma Allah ya
rinjayar da manzonsa a kan su. Daga
karshe aka kore su ga baki daya
daga cikin ta.
Bayan tafiyar wannan ayari na farko
da muke magana a kan sa, kwatsam
sai aka samu sassafcin yanayi a
birnin Makka. Domin kuwa jarumawa
biyu daga cikin wadanda ake tsoro
Allah ya karkato da zukatansu sun
karbi musulunci. Su ne; Sayyidi
Hamza – baffan manzon Allah – da
sayyidi Umar dan Khattabi. Don haka
ala-tilas aka fara sakar ma musulmi
mara, har ma ya kasance a yanzu
suna sallah a fili a cikin masallaci.
Jin wannan sauyi da aka samu sai
ayarin Usmanu dan Affana – bayan
watanni uku da suka share a can –
suka juyo suka dawo gida. Amma
kuma tsugunnen dai ba ta kare ba.
Zamu yi magana a kan musuluntar
wadannan jarumawa da muka fada,
sannan mu koma kan abin da ya
sake tilasta yin hijira ta biyu zuwa
birnin Habasha.
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 65( Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Allah ya saka da alkhairi malam

  2. me ake nufi da badar dawa

Leave a Reply

Latest updates
Categories