Azumin Ashura A Littafan Shi'a(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Bismillahir Rahmanir Rahim
Jiya na bibiyi muhawarori masu dinbin
yawa da aka tafka a shafuka daban
daban tare da ‘yan Shi’a masu musun
azumin wannan rana. Kuma suna
da’awar cewa, Ahlussunna ne suka
kirkiro shi don su rufe makokin da su
‘yan Shi’a suke yi a wannan rana. Don
haka nake so in tabbatar masu da cewa,
wannan azumi ya tabbata har a cikin
littafansu ba tare da wani kokwanto ba.
Bismillah:
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺒﺪ ﻟﻠﻪ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﺃﻥ ﻋﻠﻴﺎ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ
ﻗﺎﻝ: ) ﺻﻮﻣﻮﺍ ﺍﻟﻌﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﺍﻟﺘﺎﺳﻊ ﻭﺍﻟﻌﺎﺷﺮ ﻓﺈﻧﻪ
ﻳﻜﻔﺮ ﺫﻧﻮﺏ ﺳﻨﺔ (
1. Daga Abu Abdillah (Ja’afar As-
Sadiq A.S) daga babansa (Muhammad
bn Ali bn Husain) daga Ali (AS) ya ce:
“Ku yi azumin Ashura shi ne tara da
kuma goma ga wata, domin hakika
yana kankare zunuban shekara. Duba:
Al- Istibsar 2/134.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ) ﺻﺎﻡ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ (
2. Daga Abul Hassan (AS) ya ce:
Manzon Allah da iyalansa sun yi
azumin Ashura. Duba: Tahdhibul
Ahkam 4/29 da Al-Wafi 7/13 da
Wasa’ilus Shi’ah 7/337 da Al-Hadi’iq
An-Naadhira 13/370-371.
ﻋﻦ ﺟﻌﻔﺮ ﻋﻦ ﺃﺑﻴﻪ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ: ) ﺻﻴﺎﻡ
ﻳﻮﻡ ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﻛﻔﺎﺭﺓ ﺳﻨﺔ ( ﺍﻻﺳﺘﺒﺼﺎﺭ 2/134.
3. Daga Abu Jafar daga babansa (AS)
ya ce: Azumin Ashura yana kaffarar
(zunuban) shekara daya. Duba: Jami’
Ahadith As- Shi’ah 9/475 da Siyam
Ashura, shafi na 112
ﻋﻦ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ : ﻣﻦ ﺃﻣﻜﻨﻪ ﺻﻮﻡ
ﺍﻟﻤﺤﺮﻡ ﻓﺈﻧﻪ ﻳﻌﺼﻢ ﺻﺎﺣﺒﻪ ﻣﻦ ﻛﻞ ﺳﻴﺌﺔ ”
4. Daga As-Sadiq (AS) ya ce: Wanda
ya samu ikon azumin Muharram to, ya
yi shi. Domin yana kare mai yin sa
daga kowane laifi. Duba: Wasa’il As-
Shi’ah 7/347 da Al-Hadi’iq An-
Naadhira 13/377 da Jami’u Ahadith
As-Shi’ah 9/474
ﻋﻦ ﻋﻠﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻗﺎﻝ ” : ﺻﻮﻣﻮﺍ ﻳﻮﻡ
ﻋﺎﺷﻮﺭﺍﺀ ﺍﻟﺘﺎﺳﻊ ﻭﺍﻟﻌﺎﺷﺮ ﺍﺣﺘﻴﺎﻃﺎ ﻓﺈﻧﻪ ﻛﻔﺎﺭﺓ
ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﺘﻲ ﻗﺒﻠﻪ ، ﻭﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﻌﻠﻢ ﺑﻪ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺣﺘﻰ ﻳﺄﻛﻞ
ﻓﻠﻴﺘﻢ ﺻﻮﻣﻪ ”
5. Daga Ali (AS) ya ce: Ku yi azumin
Ashura na tara da na goma don
kewayewa. Saboda (azumin) yana
kaffarar zunuban shekarar da ta gabata.
Ko da dayanku bai sani ba har ya fara
cin abinci to, ya kammala azuminsa.
Duba: Mustadrak Al-Wasa’il 9/475
Wadannan littafan magabatan Shi’ah
kenan.
A wannan zamanin ma Sheikh As-
Sayyid Ridha Al- Husaini Al-Ha’iry ya
tabbatar da wadannan hadisan da
ingancinsu a cikin littafinsa “Najatul
Ummah Fi Iqaamatil Aza’i Alal Husain
Wal A’immah, bugun birnin Qum,
Iran, shafi na 145.
Haka shi ma Khu’i a cikin “Mustanad
al- Urwatul Wathqa” ya tabbatar da su.
Kuma ya ce akwai ruwayoyin da suka
hana yin azumin amma ba su inganta
ba kakaf.
Don haka ya ku ‘yan Shi’a idan ba zaku
yi abinda manzon Allah (SAWW) ya
yi umurni da shi ba ku kama mana
bakinku, ku je ku yi ta abinda son
zukatanku ya umurce ku. Amma kada
ku sake daga mana baki kuna cewa, an
kirkira hadisan wannan azumi mai
falala da daraja.
Allah ya kare mu daga bin son zuciya.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: