RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 07( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
RAYUWAR ANANBI SALLALLAHU
ALAIHI WASALLAMA TSAKANINSA DA
UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN
RAMALANA (3)
iii- Wayuwar Gari Da Janaba:
Ya tabbata cewa Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama kan wayi gari a cikin
watan Azumi yana mai janaba, ba tare
da hakan ta bata Azumin nasa ba.
Sayyida A’isha Raliyallahu Anha ta ce:
“Wani lokaci gari kan waye wa Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin
watan Ramalana yana kuma Azumi,
alhali yana cikin halin janaba, ba kuma
ta mafarki ba. Sai kawai ya yi wanka
ya ci gaba da Azuminsa”.
To, wannan hukunci ya shafi har mace
mai janaba ko haila ko jinni biqi. Irin
wadannan mata sun samu su dauki
Azumi da dare, matuqar sun tabbatar
da tsarkin su, idan gari ya waye su yi
wanka kamar yadda wani Hadisi na
Ummu Salamata Raliyallahu Anha ke
cewa: “Haqiqa gari kan waye wa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama yana cikin janabar saduwa
da iyali, sannan ya yi wanka ya ci
gaba da Azuminsa.”
iv- Watsa Ruwan Sanyi:
A duk lokacin da zafin rana ya
tsananta a lokacin Azumi, Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama kan xan
watsa ruwan sanyi a jikinsa, don ya
rage wa tafasar jininsa kaifi, ba tare da
la’akari da yana Azumin ba. Abubakar
dan Abdurrahman na cewa: “Na ji
wani Sahabin Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama na cewa: “Na ga Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a
wani wuri da ake ce wa Arju yana
zuba ruwa a kansa a lokacin Azumi,
saboda tsananin qishirwa da zafin
rana.”
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
kan yi haka ne, don ya tausaya wa jiki
da rayuwarsa, ta yadda zai sami
damar gudanar da wannan ibada cikin
dadin rai da kuzari. Domin ba manufar
Azumi ba ce, a tirsasa tare da azabtar
da jiki, a kuma cutar da shi. An dai
wajabta wa musulmi shi ne don a
gane yadda umurnin Allah Ta’ala ke
da qima a cikin zuciyarsu, wanda har
za su iya barin ababen da ransu ke
sha’awa, don qoqarin cika umurninsa.
Babu laifi bisa wannan hukunci, na
halaccin watsa ruwa, mutum ya yi
wanka na gaba daya, ko ya jiqe
tufafinsa da ruwa, ko ya yi ninqaya a
cikinsu, kamar yadda Buhari ya
bayyana a cikin ingantaccen littafinsa,
a babin da ya rada wa suna: Babin da
ya Tabbatar da Sahabbai da Tabi’ai na
Yin Wankan Jin Sanyi Suna Kuma
Azumi, a matsayinsu na masu
tsananin son yin koyi da Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama. Buhari ya
ce: “Dan Umar Raliyallahu Anhu ya
taba jiqe wani mayafi nasa da ruwa ya
yaba wa wani sahabi, alhali yana
Azumi. Kuma Malam Sha’abi ya taba
shiga makewayi ya yi wanka, shi ma
yana Azumi…. Kuma AlHasan – Al-
Basri – kan ce: “Babu laifi ga mai
Azumi don ya gunda ruwa ya kurkura,
ko ya yi wanka don ya dan ji sanyi.”
An kuma riwaito dan Mas’udu na
cewa, mai Azumi ya gadi wayuwar gari
yana gajiyayye kuma kasasshe”. Sai
Anas ya ce masa: “Ai ni ba ni da
matsala, don ina da wani kwami da
nake shiga in yi wanka ko ina Azumi.”
To, a shar’ance, bisa wannan dalili, ya
halatta ga mai Azumi ya sha sanyin
Iyakwandishin, don rage zafin rana. Ba
wannan kawai ba, a dunqule, mutum
na iya amfani da duk abin da zai
taimaka masa ga gudanar da wannan
ibada ko wata, a cikin nishadi da
karsashi. Kai! An so ma ya yi haka.
Kuma duk wata wahala da mutum ke
iya tsere wa a cikin sha’anin ibada, to
Shari’a ba ta son ya saurara mata ko
kadan. Amma duk wahalar da ba haka
ba, kamar arwalla a lokacin hunturu,
ko tafiya aikin Hajji, ko tattaki zuwa
masallaci don Sallar jam’i a lokacin
tsananin zafin rana, ko sanyi. Duk
wadannan wahalhalu ne da ba za a iya
kauce masu ba. Saboda haka ma har
lada suke qara wa mutum ta
musamman.
A kan haka ne Malam Ibnu Taimiyya
ke cewa: “Ya kamata musulmi su san
cewa, ba nufin Allah ba ne, ya ga ana
azabtar da rayuwa, ta hanyar dora
mata wahalhalu , balle a ce a duk
lokacin da wata ibada ta fi tsanani a
kan mutum, a lokacin ne ya fi samun
lada, kamar yadda jahilai da yawa ke
zato. Ko alama ba haka abin yake ba.
Mutum na samun lada ne a kan aiki,
gwargwadon yadda aikin nan yake da
amfani, tare kuma da kasancewarsa
abin da Allah da Manzonsa suka yi
umurni da shi. Saboda haka duk aikin
da aka fi biyar tafarkin Shari’a a
cikinsa, to ya fi inganci ya kuma fi
lada. Ba yawan aiki ko wuyarsa Allah
ke dubi ba, a’a niyya dai. Allah shi ne
mafi sani.”
Shari’a abu ce mai yalwa, ta kuma
hukunta mana cewa, mafificin al’amari
shi ne mafi sauqi. Amma tsananta wa
kai a cikin sha’anin ibada, musamman
Azumi, abu ne da ya saba wa koyarwar
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.
v- Kurkura Baki Da Shaqa Ruwa:
Haka kuma ya tabbata Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama kan
kurkure bakinsa, ya kuma shaqa ruwa
a cikin halin Azumi, amma duk ba tare
da ya tsananta a cikin yin hakan ba.
Laqidu dan Saburata Raliyallahu Anhu
na cewa: “Wata rana na ce wa Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba
ni labarin yadda ya kamata a yi
arwalla. Sai ya ce: “Ka kyautata ta ta
hanyar tsetstsefe ‘yan yatsunka, da
kai matuqa a cikin shaqa ruwa, sai fa
idan kana Azumi”.
Ka ga iyakar tsakaitawa kenan, a
lokaci daya Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya hori al’ummarsa da
tsare tsafta, tare kuma da kiyaye
alfarmar Azumi; wato ya ba wa kowane
bangare nasa haqqi.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates