RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 05( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
BABI NA BIYU
2.0 Rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama Tsakaninsa da Ubangijinsa
a Lokacin Azumin Ramalana:
Wannan babi zai yi bayani ne a kan
yadda rayuwar Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ke kasancewa tsakaninsa
da Ubangijinsa a wannan lokaci na
Azumin Ramalana, ta hanyar kallon
siga da yanayin Azuminsa tun daga
sahur har zuwa shan ruwa, da irin
yadda yake raya dare da ibada a
lokacin, da makamantansu.
2.1 Shimfixa:
Kasancewar babu wani mahaluki da ya
kai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
sanin girman Allah Subhanahu Wa
Ta’ala da kiyaye alfarmarsa, hakan ta
sa babu wani mataki na kai wa
matuqa, a cikin bautar Allah da bai
taka ba, ta yadda ko qurarsa wani ba
zai iya hangowa ba a fagen. A
sakamakon haka sai Allah Subhanahu
Wa Ta’ala ya gafarta masa zunubansa
na farko da na qarshe.
Amma duk da haka, maimakon ya
miqe qafafu, Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama bai fasa raya dare tsaye ba,
har qafafunsa suka rinqa yin kumburi
suna tsatstsagewa. Wannan abu ya ba
Nana Aisha (RA) matuqar mamaki,
tare da daure ma ta kai, har ta kasa
haquri, ta tambaye shi dalili. Shi kuwa
Sallallahu Alaihi Wasallama ya karba
mata da cewa: “Ashe ba kamata ya yi
in zama bawa mai godiya ba?”
Bayan wannan irin doguwar tsayuwa
kuma, Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama har hadawa yake yi da
kuka mai tsanani da dua’i irin na mai
matsananciyar buqata zuwa ga
Ubangijinsa. Abdullahi dan Shukhairu
(RA) na cewa: “Na ga Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama yana
Sallah wata rana, qirjinsa na gurnani
kamar tafasar tukunya saboda
tsananin kuka.” Haka kuma Uwar
Muminai Aisha (RA) ta bayar da
labarin wani abun mamaki da ta gani
ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama tana mai cewa: “Wata rana
da dare ya ce mani: “Ya ke Aisha ki
dan ba ni dama in bauta wa
Ubangjina.” Sai na ce masa: “Wallahi
yau ina sha’awar in kusance ka,
amma kuma ba ni son abinda zai
sosa ranka, Allah ya karba.” Ta ce:
“Sai kuwa ya tashi ya yi tsarki
(arwalla) ya kama Sallah. Daga nan fa
ya fashe da kuka har hawaye suka jiqa
cinansa. Yana yi yana qara qamari har
gemunsa ya yi sharkat da hawaye, kai,
har sai da qasar wurin ita ma ta san
ana yi. Ana haka sai ga Bilal ya shigo,
lokacin Sallar Subahin ya yi. Da ya ga
irin yadda Annabi ke ta faman kuka,
sai ya tambaye shi; “Kukan me kake yi
haka ya Manzon Allah, alhali Allah ya
riga ya gafarta maka zunubanka na
farko da na qarshe? Sai ya karba masa
da cewa: “Ina godiya ga Allah ne a
kan haka. Kuma ga shi an saukar mani
da wata aya a wannan dare, wadda
bone ke tabbata a kan duk wanda ya
karanta ta bai yi nazarin ta ba, ita ce:
“Haqiqa a cikin halittar sammai da
qasa………….”
Dubi irin yadda Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ke
qasqantar da kansa, tare da kai
matuqa a cikin tukewa da narkewa
gaban Allah Madaukakin Sarki, tattare
da kasancewarsa shugaban ’yan Adam
baki daya. Kuma limamin sahun bayin
Allah masu madaukakiyar daraja, yana
mai hada tsoron azabar Allah da fatar
samun ludufi da jinqayinsa a lokaci
daya. Sabanin yadda muke a yau. Sai
ka ga mutum ya yi wa addini riqon
sakainar kashi, ya mayar da
hankalinsa kacokan ga masha’a da
sharholiya. Babu lokacin da
hankalinsa zai tashi ya tuna ranar
haduwarsa da Allah, ya yi la’asar.
Babu abin da ke gabansa sai hidimar
duniya, ta lahira ko, ko aho! Komai
take tafasa ta qone. A yayin da wani
ma, sai ka ga kamar an aiko masa da
takardar shedar gafara; hankalinsa
kwance, zuciyarsa zaune. Ka kuwa
san mai irin wannan hali, ko ya yi
iqirarin kasancewa mai koyi da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama sai dai a saurare shi
kawai. Domin idan mafadi ba ya da
hankali, majiyi yana da shi. Allah ka
jiqan mu ka gafarta mana ka saka mu
cikin bayinka managarta, amin.
Yanayin rayuwar AnnabiSallallahu
Alaihi Wasallama tsakaninsa da
Ubangijinsa a wannan lokaci na
Azumin Ramalana, hoto ne qarara na
yadda ibadarsa da tawali’unsa suka
kasance wanda kuma ya hada da:
2.2 Sigar Azuminsa:
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
kan gudanar da Azumi a wannan wata
na Ramalana ta hanyar tabbatar da ya
yi sahur, ya kuma yi budin baki a cikin
lokaci da yanayin da ya dace, wato ta
hanyar gaggauta budin baki. Ba yakan
bari sai ya yi Sallar magariba ba. Shi
kuwa sahur yakan yi shi ne gab da
kiran Sallar Asuba na biyu. Budin
bakin kuwa yakan yi shi ne da wani
abu na ‘ya’yan itace danyu, wato
ababen marmari ko dabino ko ruwa
kawai. Amma ya fi yi da dabino, ya
kuma kwadaitar da al’ummarsa yi da
shi. Bayan wannan kuma duk wani
abu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama zai yi sahur ko budin baki
da shi, abu ne mai matsakaiciyar
daraja, wato kadaran-kadahan.
Hadissan da ke magana a kan yanayin
sahur da budin bakin Manzon Allah,
suna da yawa. Ga kadan daga ciki:
Anas Raliyallahu Anhu na cewa:
“Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
kan yi budin baki ne kafin ya yi Sallah,
ta hanyar amfani da ababen marmari.
Idan bai same su ba, sai ya nemi ‘yan
qwarorin dabino. Idan shi ma ya
faskara, sai ya dan kukkurba ruwa
kawai”. Shi kuwa Ibnu Adiyyata Allah
ya jiqan sa cewa ya yi: “Ni da Malam
Masruqu mun shiga wurin Nana Aisha
Raliyallahu Anha. Masruqu ya ce
mata: “Abokan Muhammadu ne
Sallallahu Alaihi Wasallama guda biyu,
da kowanen su ba ya qasa a guiwa a
kan aikin alheri. Daya daga cikin su na
gaggauta yin buxin baki da Sallar
magariba, dayan kuwa yana jinkirta
su. Me za ki ce?” Sai ta ce: “Waye
daga cikin su ke gaggautawa?” Ya ce
mata: “Abdullahi”. Sai ta ce: “To, haka
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ke yi”
Haka kuma Abdullahi dan Abu Aufa
Raliyallahu Anhu na cewa: “Wata rana
muna tare da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama a cikin halin tafiya,
kuma a lokacin Azumin Ramalana.
Rana na faduwa kawai, sai ya umurci
wani daga cikin Sahabbansa da cewa:
“Tashi ka dama mana gumba, mu
buda baki.” Sai shi kuma ya ce: “Ya
Manzon Allah! Ai rana ba ta gama
faduwa ba.” Sai Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce masa: “Tashi
dai ka dama mana! ” Nan take ya tashi
ya dama gumbar, ya kawo wa Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya sha.
Qare shan ke da wuya sai ya daga
hannunsa ya yi nuni ya ce: “Ai da
zarar rana ta faku a nan, dare kuma ya
kunno kai daga can to, Azumi ya
kammala.”
Haka kuma Abdullahi dan Harisu ya
riwaito daga wani Sahabi na Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya
ce : “Na shiga wurin Annabi Sallallahu
Alaihi Wasallama wata rana, sai na
taras yana sahur. Sai ya ce mani:
“Haqiqa sahur wata albarka ce Allah
ya arzutta ku da ita, kar ku bari ta
wuce ku.” Bayan wannan kuma Zaidu
dan Sabitu Raliyallahu Anhu ya ce:
“Mun yi sahur wata rana tare da
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai
ya miqe don yin Sallah. Ni kuwa sai
na tambaye shi da cewa: “Wace irin
tazara ya kamata mutum ya sanya
tsakanin qare sahur da kiran Sallah?
Sai ya karba mani da cewa:
“Gwargwadon yadda za a iya karanta
aya hamsin” Manzon Allah ya yi
gaskiya. Ko shakka babu, duk wanda
ya jinkirta sahur kamar haka, ba zai ji
wuyar Azumi ba ko kadan, ba kuma za
a yi Sallar Asuba ba da shi ba. Bayan
wannan kuma, Abu Harairata ya riwaito
cewa, Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: “Madalla da sahur
din da mumini ya yi da dabino.” A kan
wannan magana kuma ta yin sahur da
dabino, Anas Raliyallahu Anhu ya ce,
wata rana Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama zai yi sahur, sai ya ce: “Ya
kai Anas, ka ga lokacin sahur ya yi,
samo mani dan wani abu in sa baka.”
Anas ya ce: “Sai na kawo masa
dabino da ruwa a cikin kwacciya.
Hakan kuwa ta faru ne, bayan har
Bilalu ya yi kiran salla.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories