IBNU TAIMIYYAH BAI HALATTA MAULIDI BA

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Author: Dr.Ibrahim Jalo Jalingo


Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah bai halatta idin maulidi ba, a’a a gurinsa rikon ranar haihuwar Manzon Allah a matsayin idi yana daga cikin bidi’o’in da ‘yan bidi’a suka kirkira; wannan shi ne ma ya sa ya rubuta cikin littafinsa mai suna: Iqtidhaa’us Siraa’til Mustaqiim 2/123-124 kamar haka:

((وكذلك ما يحدثه بعض الناس اما مضاهاة للنصارى في ميلاد عيسى عليه السلام واما محبة للنبي صلى الله عليه وسلم وتعظيما والله قد يثيبهم على هذه المحبة والاجتهاد لا على البدع من اتخاذ مولد النبي صلى الله عليه وسلم عيدا مع اختلاف الناس في مولده فان هذا لم يفعله السلف مع قيام المقتضي له وعدم المانع منه لو كان خيرا ولو كان هذا خيرا محضا او راجحا لكان السلف رضي الله عنهم احق به منا فانهم كانوا اشد محبة لرسول الله صلى الله عليه وسلم وتعظيما له منا وهم على الخير احرص وانما كمال محبته وتعظيمه في متابعته وطاعته واتباع أمره وإحياء سنته باطنا وظاهرا ونشر ما بعث. به والجهاد على ذلك بالقلب واليد واللسان فان هذه طريقة السابقين الأولين من المهاجرين والأنصار والذين اتبعوهم بإحسان)).

Ma’ana: ((Haka nan abin da sashin mutane ke kirkira ko dai saboda koyi da Kiristoci cikin bukin Kirsimeti’ ko kuwa saboda son Annabi mai tsira da amincin Allah da girmama shi, zai yiwu Allah ya ba su lada a kan nuna kokari da soyayya’ amma ba zai ba su lada ba a kan bidi’o’in rikon maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi ba duk da yake ma masu tarihi sun yi sabani a kan wace rana ce da wani wata ne aka haife shi! Shi dai bukin maulidi babu wani daga cikin magabata da ya yi shi duk kuwa da cewa dukkan dalilan da ake bayarwa na yin bukin a yanzu akwai su a wancan lokacin ma, kuma babu wani abu da zai hana su yin bukin inda yin shi alheri ne. Lalle ne da yin bukin maulidi tsantsar alheri ne to da Salaf Magabata su suka fi cancantar yin sa a kanmu, saboda sun fi mu son Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da girmama shi, kuma sun fi kowa son aikata alheri. Lalle cikar soyayya da girmamawa ga Annabi tana cikin bin shi ne da yi masa da’ah da bin umurnin shi, da raya sunnar shi ciki da waje, da yada abin da aka aiko da shi, da yin jihadi da zuciya, da hannu, da harshe a kan hakan wannan ita ce hanyar Magabata na farko daga cikin Muhajirai da Ansarawa da wadanda suka bi su da kyautayi)).

Don Allah ku lura da maganarsa da ya ce: ((والله قد يثيبهم على هذه المحبة والاجتهاد لا على البدع من اتخاذ مولد النبي صلى الله عليه وسلم عيدا )) Ma’ana: ((Zai yiwu Allah Ya ba su lada a kan nuna kokari da soyayya, amma ba zai ba su lada ba a kan bidi’o’in rikon maulidin Annabi mai tsira da amincin Allah a matsayin idi ba)), in kuka lura da kyau za ku fahimci cewa babu mai cewa Ibnu Taimiyyah ya halatta yin maulidi cikin wannan magana tasa sai mutumin da ya zabi bin son zuciyarsa a kan tsayuwa kan daidai ko da kuwa hakan ya saba wa abin da yake son ji, ko yake son gani; domin a nan abubuwa ne guda biyu:
1. المحبة والاجتهاد watau son Annabi da Ijtihadi.
2. البدع من اتخاذ مولد النبي ص عيدا watau bidi’o’i na rikon maulidin Annabi a matsayin idi.
– Ku lura da inda Ibnu Taimiyyah ya ce: Allah na iya ba da lada a kan son Annabi da kuma ijtihadi, idan kuka lura za ku fahimci cewa tabbas babu talazumi tsakanin son Annabi da Ijtihadi da tsakanin Bidi’ar yin bukin maulidi; domin ana iya samun son Annabi da Ijtihadi ba tare da yin bukin maulidi ba; saboda dukkan Sahabbai da Tabi’ai sun so Annabi sun kaunace shi, kuma sun yi Ijtihadi amma kuma babu daya daga cikinsu da ya yi bukin maulidi. Akasin wannan shi ma sahihi ne, ma’ana ana iya samun yin bukin maulidi ba tare da son Annabi da Ijtihadi ba; domin daga cikin masu bukin maulidi akwai masu bayyana sabo da alfasha a lokacin bukin, kamar cakuda tsakanin maza da mata da ma abin da ya zarce hakan muni.
– Sai kuma sai Annabi ya sake cewa: Allah ba ya ba da lada a kan bidi’o’in rikon maulidi a matsayin idi.
Don Allah Jama’a in banda bacewar basira ta kaka ne wani zai fahimci mai wannan magana da cewa wai ya halatta bukin maulidi, wai ya halatta rikon ranar maulidi a matsayin idi? Allah Ka shiryar da al’ummarmu. Ameen.

Leave a Reply

Latest updates
Categories