Ku kula da wanda kuke daukan Addinin ku a wurinsu

Danna nan domin shiga group na karatu Online

An rawaito daga ibn Sirin yana cewa

إن هذا العلْمَ دينٌ فلينظُرْ أحدُكُم مِمَّن يأخُذُ دينَهُ

Hakika wannan Ilimin addini ne, ɗayanku ya lura sosai daga waye zai rinƙa ɗaukan addininsa.

Haƙiƙa shi addinin Musulunci ya ginu ne kan ilimi, shiyasa ba’a yinsa da jahilci, dole sai mutum ya nemi ilimin yanda ake yinsa. Amma sai dai wurin neman wannan ilimin ya kamata mutum ya lura sosai wurin waye zai ɗauki ilimin nashi? Wurin waye zai koyi addini? Domin a wannan zamani namu fitintinu sun yaɗu da yawa, Maluma na ƙarya masu da’awar Sunnah sun yaɗu a bayan ƙasa, jahilci ya yawaita da sunan ilimi. Kamar yadda Annabi ya bada labari

daga cikin alamun tashin Qiyaama, za’a ɗauke ilimi sannan kuma jahilci ya yaɗu ya tabbatu.

Sahihul bukhari : 80

hanyoyin da Allah ke ɗauke ilimi shine Mutuwar Malamai na Allah, ta yadda ba’a samun masu maye gurbin su. Sai kuma wasu jahilai suzo su maye gurbin su wanda basu fahimci addini ba, kuma ba Addinin bane a gabansu. Sabida haka ya dace mu kula da wa’inda muke ɗaukan ilimi a wurinsu, ko muke sauraron su. mu tabbatar cewa sun cancanci a saurare su sabida suna da ilimin ba wai kawai dun suna da zaƙin baki ba. Kuma mu tabbata masu tsoron Allah ne ba wai a baki kawai ba. Mu ƙaurace wa sauraron ko wani irin mai da’awar malanta sai wanda duniyar ilimi ta tabbatar da cewa shi malami ne. Bawai kuma ana gane shi da laƙabi da ake bashi bane irin laƙabi na wannan zamani na Dr, Prof da sauransu. Wannan laƙabi ne kawai baya tabbatar da cewa mutum ya makkanu a ilmi.

Allah yasa mudace. Ya kuma daɗa shiryar damu tafarki madaidaici.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Ku kula da wanda kuke daukan Addinin ku a wurinsu”
  1. I like the valuable information you provide in your articles.

Leave a Reply

Latest updates
Categories