Mas'alolin aure Fitowa ta 14(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

Muna cikin bayani akan nau’ikan aure da ake yi a lokacin jahiliyya, wadanda shari’ar musulunci ta zo ta haramta su. TAMBAYA
Mene ne auren dadiro, irin wanda ake yi a zamanin Jahiliyya, kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Auren dadiro aure ne da mutanen Jahiliyya suke yi, wanda mutum zai rika soyayya da mace, ya ajiye ta yana zina da ita a boye, amma da zarar ya bayyana, to, ya zama haramun a wurinsu. Wannan auren shari’ar musulunci ta haramta shi, kuma yana daga cikin mafi sharrin nau’ikan zina, domin za a rika ganin mace ko namiji kamar salihi, bayan kuwa a boye tatatcen mazinaci, ko mazinaciya ce. Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya ce:
…فَانْكِحُوهُنَّ بِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ مُسَافِحَاتٍ وَلَا مُتَّخِذَاتِ أَخْدَان…
Ma’ana:
… Ku aure su da iznin iyayensu, kuma ku ba su sadakinsu bisa kyautatawa, alhali suna katangaggu ba masu zina ba, kuma kada ku rike su a matsayin dadiro….
A nan muke yin nasiha ga `yan’uwa musulmi wadanda suka mayar da matar dadiro tamkar matar aure, a kama mata daki a hamshakin otel tare da kashe mata kudi fiye ma da yadda ake yiwa matar aure. Lallai su sani cewa wannan mummunar dabi’a ce, su nisance ta domin karshen al’amarinsu ba zai yi kyau ba a nan duniya da kuma ranar gobe kiyama.
TAMBAYA:
Mene ne auren musanyen mata? kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Auren musanyen mata aure ne shima da mutanen jahiliyya suke yi; mutum zai ce da wani mutum ka karbi matata, kai kuma ka ba ni taka matar, wato yana nufin ya ba shi matarsa ya rika saduwa da ita, haka shi ma ya ba shi tasa matar. Wannan auren haramtacce ne, musulunci ya haramta shi, domin miji ba shi da ikon halatta matarsa ga wani. Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya ce:
فَانْكِحُوهُنَّبِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ مُسَافِحَاتٍ …
Ma’ana:
… Ku aure su da iznin iyayensu, kuma ku ba su sadakinsu bisa kyautatawa, alhali suna katangaggu ba masu zina ba….
A nan ayar ta nuna ita matar aure katangaggiya ce kuma Allah ya hana wani ya aure ta ko ya sadu da ita idan ba mijinta ba, saboda haka aikata haka haramun ne.
Abin mamaki, asalin musanyan mata mutanen jahiliyya ne suke yinsa ko kuma kasashen arna wadanda ba su san Allah da Manzonsa ba, amma sai ga shi yanzu wai a samu `ya`yan musulmi suna yinsa da nufin wayewar kai, ko da’awar `yancin dan Adam, wannan kuwa tabewa ce duniya da lahira, don haka masu aikata wannan mummunar dabi’a ya kamata su yi hattara kuma su tuba zuwa ga Ubangiji subhanahu wa ta’ala. Allah ya nisanta mu daga wannan mummunar dabi’a.
TAMBAYA:
Mene ne auren neman iri kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Auren neman iri aure ne shima na jahiliyya wanda mutum zai tura matarsa ta je wurin wani mai mulki ko wani jarumi ko mai yawan kyauta ya sadu da ita domin ta haifa masa da irinsa. Wannan auren, kamar yadda ya tabbata a hadisin Nana A’isha رضي الله عنها ta ce:
…كَانَ الرَّجُلُ يَقُولُ لِامْرَأَتِهِ إِذَا طَهُرَتْ مِنْ طَمْثِهَا أَرْسِلِي إِلَى فُلَانٍ فَاسْتَبْضِعِي مِنْهُ وَيَعْتَزِلُهَا­زَوْجُهَا وَلَا يَمَسُّهَا أَبَدًا حَتَّى يَتَبَيَّنَ حَمْلُهَا مِنْ ذَلِكَ الرَّجُلِ الَّذِي تَسْتَبْضِعُ مِنْهُ فَإِذَا تَبَيَّنَ حَمْلُهَا أَصَابَهَا زَوْجُهَا إِذَا أَحَبَّ وَإِنَّمَا يَفْعَلُ ذَلِكَ رَغْبَةً فِي نَجَابَةِ الْوَلَدِ فَكَانَ هَذَا النِّكَاحُ نِكَاحَ الِاسْتِبْضَاع…
Ma’ana:
… Mutum ya kasance (a zamanin jahiliyya) yana tura matarsa idan ta tsarkaka (daga al’adar ta) sai ya ce da ita: ki je wurin wane ya sadu da ke, shi kuma mijin sai ya nisance ta, ba zai taba ta ba har sai cikinta ya bayyana, idan cikin ya bayyana, sai ya sadu da ita idan yana so, suna yin haka ne don kwadayin samun da(jarumi ko fasihi ko kyakkyawa d.s), to, wannan shi ake kira da auren neman iri…
Wannan auren shi ma zina ce tsagwaronta, kuma musulunci ya hana yin sa, saboda haka duk wanda ya yi shi za a yi masa hukunci irin na zina.
A nan muke cewa; hadisin Nana A’isha رضي الله عنها yana nuna cewa, duk wanda ya tura matarsa wurin wani, yana yin haka ne domin ya samu da mai siffa irin ta wanda ya sadu da ita, ko dai don ya zama sadauki ko mai kyawun halitta ko mai kyauta sai musulunci ya zo ya hana. Amma abin mamaki har yanzu akwai jahilai da suke yin irin wannan aika-aikar, suna tura matansu zuwa ga wani wanda suke kudurce cewa yana da albarka don ya sadu da ita da nufin samun tabarruki, hakika yin haka sabawa Allah da Manzonsa ne tare kuma da jahiltar musulunci sannan tabewa ne da hasara, haka kuma zina ce tsagwaronta, kuma duk wanda ya halatta yin haka, to, hakika ya halatta zina, wanda kuma duk ya halatta zina kafiri ne cikakke, Allah ya kiyashe mu tabewa, amin.
TAMBAYA:
Mene ne auren taron dangi kuma mene ne hukuncinsa?
AMSA:
Wannan shima aure ne na jahiliyya, wanda mutane uku zuwa goma suke auren mace daya a lokaci guda, kamar yadda ya tabbata a hadisin Nana A’isha رضي الله عنها ta ce:
وَنِكَاحٌ آخَرُ يَجْتَمِعُ الرَّهْطُ مَا دُونَ الْعَشَرَةِ فَيَدْخُلُونَ عَلَى الْمَرْأَةِ كُلُّهُمْ يُصِيبُهَا فَإِذَا حَمَلَتْ وَوَضَعَتْ وَمَرَّ عَلَيْهَا لَيَالٍ بَعْدَ أَنْ تَضَعَ حَمْلَهَا أَرْسَلَتْ إِلَيْهِمْ فَلَمْ يَسْتَطِعْ رَجُلٌ مِنْهُمْ أَنْ يَمْتَنِعَ حَتَّى يَجْتَمِعُوا عِنْدَهَا تَقُولُ لَهُمْ قَدْ عَرَفْتُمْ الَّذِي كَانَ مِنْ أَمْرِكُمْ وَقَدْ وَلَدْتُ فَهُوَ ابْنُكَ يَا فُلَانُ تُسَمِّي مَنْ أَحَبَّتْ بِاسْمِهِ فَيَلْحَقُ بِهِ وَلَدُهَا لَا يَسْتَطِيعُ أَنْ يَمْتَنِعَ بِهِ الرَّجُل
Ma’ana:
…Akwai auren da mutanen jahiliyyya suke yi wanda mutum uku zuwa goma suke haduwa su auri mace daya suna saduwa da ita, idan kuma ta haihu sai ta kira su ta ce da su: kun san abin da kuke aikatawa da ni, to, a yanzu na haihu, sai ta jingina dan ga wanda take so daga cikinsu kuma babu wanda zai yi mata musu a kan hukuncin da ta yi…
Babban malami Ibn Hajar ya fada a cikin littafinsa cewa:
Bisa ga dukkan alamu ba ta jingina `ya mace gare su, saboda abin da aka sani na kiyayyarsu ga `ya`ya matan da aka samu ta hanyar aure ingantacce, ballantana kuma ta irin wannan auren.
Wannan auren shima haramun ne a musulunci, kuma ya sabawa dokokin aure baki daya, domin aiki ne na jahiliyya wadanda ba su san Allah da Manzonsa ba kuma zina ce tsagwaronta, haka kuma babu wanda zai aikata wannan mummunan aiki face jahili ko kafiri.
Allah ya kara mana shiriya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates