Mas'alolin Aure Fitowa ta 2(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

TAMBAYA TA 2:
Shin wadanne dalilai ne ke zaburarwa akan yin aure?
AMSA:
Na farko akwai umarni daga Ubangiji subhanahu wata’ala inda yake cewa:
…فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ……النساء:3
Ma’ana: …Ku auri abin da ya dadada gare ku na daga mata biyu-biyu ko uku-uku ko hudu-hudu…
Da kuma fadinsa subhanahu wa ta’ala cewa:
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلًا مِنْ قَبْلِكَ وَجَعَلْنَا لَهُمْ أَزْوَاجًا وَذُرِّيَّةً…ال­رعد:38
Ma’ana:
Hakika Mun aiko Manzanni kafin ka, Muka kuma sanya musu matan aure da zuriya…
Sannan Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya kara fada cewa:
وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَمِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ …النور: 32
Ma’ana:
Ku aurar da zawarawa daga cikinku kuma ku aurawa managarta daga cikin bayinku da kuyanginku…
Kuma hadisai masu yawa sun tabbata daga Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama wadanda suke kwadaitar damu yin aure. Daga cikin su akwai hadisin Abdullahi Ibn Mas`ud radhiyallahu anhu wanda yake cewa:
كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ شَبَابًا لاَ نَجِدُ شَيْئًا، فَقَالَ لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلّمَ: يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ.
Ma’ana:
Mun kasance tare da Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama muna matasa ba mu da komai (na halin yin aure), sai Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya ce mana: “Ya ku samari! Wanda ya sami ikon yin aure daga cikinku, to ya yi aure. Domin yinsa shine ya fi (taimaka wa mutum wajen) kau da ido (daga haram) da kiyaye farjinsa (daga aikata alfasha). Wanda ba shi da ikon yin auren, to, ya lazimci yin azumi, domin azumi zai zame masa makari (mai datse sha’awa).
Kuma hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Amr radhiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama ya ce:
الدُّنْيَا مَتَاعٌ، وَخَيْرُ مَتَاعِ الدُّنْيَا الْمَرْأَةُ الصَّالِحَةُ.
Ma’ana:
Duniya wani jin dadi ce, kuma mafificin jin dadi do duniya shi ne: mace ta gari.
Haka kuma wani hadisin ya tabbata daga Anas Ibn Malik t wanda a cikinsa Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama yake cewa:
…أَمَا وَاللهِ إِنِّي لَأَخْشَاكُمْ لِلَّهِ، وَأَتْقَاكُمْ لَهُ، لَكِنْ أَصُومُ وَأَفْطِرُ وَأُصَلِّي وَأَرْقُدُ وَأَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتِي فَلَيْس مِنِّي.
Ma`ana:
…Na rantse da Allah, na fi ku jin tsoron Allah, kuma na fi ku kiyaye dokokinSa. Sai dai duk da haka, nakan yi azumi kuma nakan sha, nakan yi sallar dare kuma nakan yi bacci, sannan kuma ina auren mata. Duk wanda ya kyamaci sunnata, ba ya tare da ni.
A nan ka ga wannan hadisi, yana gargadi ne ga wanda yake cewa, zai ta yin azumi ba zai sha ba, da wanda ya ce zai yi ta yin sallar dare ba zai yi barci ba, da kuma wanda ya ce zai yi ta ibada ba zai yi aure ba, saboda da`awar gudun duniya. Wanda ya aikata haka ya sabawa sunnar Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama Kuma sabawa sunnar Manzon Allah sallallahu alaihii wa sallama bata ne. Allah ya kiyashe mu sabawa sunnar Manzonsa sallallahu alaihii wa sallama, Ya sa mu dace da bin ta sau da kafa, amin

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates