Mas'alolin aure Fitowa ta 12(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

·

·

Bayani game da dalilan da Shi’a Imamiyya suke kafa hujja da su don halatta auren mutu’a:
1-
(A)- Da farko dai ayar da suka dogara da ita ko kadan ba dalili ba ce a kan halaccin auren mutu’a; domin kuwa tana magana ne a kan ingantaccen aure na dindindin, da kuma abin da ya wajaba a baiwa mace na sadakinta. Abinda yake nuna wannan maganar shine; farkon ayar Ubangiji subhanahu wa ta’ala yana magana ne akan matan da bai halatta a aura ba, sannan sai ya yi magana akan yin aure wanda yake sananne a shari’a. Ya ce:
وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ كِتَابَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَأُحِلَّ لَكُمْ مَا وَرَاءَ ذَلِكُمْ أَنْ تَبْتَغُوا بِأَمْوَالِكُمْمُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْبِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً… النساء2
Ma’ana:
Haka kuma an haramta muku (auren) katangaggun mata (wato matan da suke karkashin aure), face abinda kuka mallaka na kuyangi, (wannan) hukuncin Allah ne a gare ku tabbatacce. Kuma an halatta muku koma bayan wadannan(nau’ikan matan da aka ambata), ku aure su da dukiyoyinku, kuna masu kare kanku, ba masu zina ba. Abin da kuka ji dadi da shi daga gare su (na saduwar aure), to, ku ba su ladansu na sadaki…
Ambaton kalmar” ujurahunna” “ladan su” ba yana nufin ladan mutu’a ba ne , domin Allah yakan ambaci “sadakin aure” da kalmar”ujuur” (ladan aure) kamar yadda ya ke a wurare da dama a cikin Al-Kur’ani Mai Girma, misali :
يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنَّا أَحْلَلْنَا لَكَ أَزْوَاجَكَ اللَّاتِي آتَيْتَ أُجُورَهُنَّ… الأحزاب: 50
Ma’ana:
Ya kai Annabi (mai girma)! Hakika Mu, mun halatta maka matanka wadanda ka baiwa “ujuur din su” (sadakin aurensu)…
Kalmar ujurahunna a nan babu ko shakka sadakin aure take nufi, ba wai ladan mutu’a ba.
Da kuma fadinsa:
فَانْكِحُوهُنَّبِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ…­النساء: 25
Ma’ana:
Ku aure su bisa izinin waliyyansu, kuma ku ba su”ujuur din su” (sadakinsu) bisa kyautatawa…
A nan ma kalmar “ujurahunna” sadaki ake nufi ba ladan mutu’a ba.
(B)- Ita kuwa hujjar da suka kafa na kira’ar da ake cewa kira’ar Ubayyu Ibn Ka’ab da Abdullahi Ibn Abbas رضي الله عنهما kira’a ce shazza, wadda malaman kira’a ba sa kirga ta a cikin tabbatattun kira’o’i. Ita kuwa Kira’a Shazza ba za ta ci karo da tabbatacciyar kira’a mutawatira ba, inda Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya fada a Suratul Muminun:
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ (5) إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (6) فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ (7)المؤمنون:7– 5
Ma’ana:
(Hakika Muminai) Su ne masu kiyaye farjinsu. Saifa ga matayensu, ko abin da suka mallaka na kuyangi, hakika wadannan ba abin zargi ba ne. Wanda duk ya nemi (wani abu) koma bayan wannan, wadannan su ne masu shisshigi da ketare dokokin Allah.
Abin fahimta a nan shine Allah ya bayyana cewa mace ba ta halatta ga mutum, sai ta wadannan hanyoyi guda biyu, ko dai aure na dindindin ko kuma mallakar kuyanga, amma bai yi maganar auren mutu’a ba. Sannan a karshen ayoyin, Allah ya yi bayanin narko ga wanda ya nemi jin dadi da wata mace sabanin ta hanyar da aka ambata.
(C)-Kuma idan ma muka dauka cewa waccan kira’ar tabbatacciya ce, to, duk da haka ba za ta zama hujjar yin auren mutu’a ba, saboda ka’idar da malaman Usulu suke cewa; “Idan dalilan halattawa da na haramtawa suka hadu akan mas’ala daya, to, ana gabatar da dalilin haramtawa.
2-
(A)- Hujjar su ta biyu; game da fatawar Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhuma na halatta auren mutu’a, wannan ya faru ne a farkon lamari, amma daga baya an sanar da shi haramta auren mutu’a da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yayi har zuwa ranar alkiyama.
Imamu Muslim ya rawaito hadisi cewa:
عَنْ عَلِىٍّ أَنَّهُ سَمِعَ ابْنَ عَبَّاسٍ يُلَيِّنُ فِى مُتْعَةِ النِّسَاءِ فَقَالَ مَهْلاً يَا ابْنَ عَبَّاسٍ فَإِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم نَهَى عَنْهَا يَوْمَ خَيْبَرَ وَعَنْ لُحُومِ الْحُمُرِ الإِنْسِيَّةِ.
Ma’ana:
Hakika Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu ya ji Ibn Abbas radhiyallahu anhuma yana saukakawa akan auren mutu’a, sai ya ce; ka saurara ya Ibn Abbas, lallai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya hana yin auren mutu’a da cin naman jakin gida a ranar Khaibar.
Don haka ba za a kafa hujja da fatarwar Ibn Abbas radhiyallahu anhu ba, domin shi kansa sai daga baya sakon Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama na haramcin auren mutu’a ya isa gare shi.
(B)- Ita Kuwa maganar Jabir Ibn Abdullah radhiyallahu anhuma cewa:
كُنَّا نَسْتَمْتِعُ بِالْقُبْضَةِ مِنَ التَّمْرِ وَالدَّقِيقِ الأَيَّامَ عَلَى عَهْدِ رَسُولِ اللَّهْ صلى الله عليه وسلم. وَأَبِى بَكْرٍ حَتَّى نَهَى عَنْهُ عُمَرُ…
Ma’ana:
Mun kasance muna mutu’a da cikon tafi na dabino da gari (garin alkama) a zamanin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da Sayyadina Abubakar radhiyallahu anhu, har saida Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya hana…
To, a nan za mu ce da su Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya ji hanin auren mutu’a ne daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama, shi ya sa ya hana yinsa kamar yadda Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu ya ji haramcin a wajen Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama kuma ya hana Ibn Abbas radhiyallahu anhuma. Wannan dalilin shi ya sa su Jabir ba su ja da Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ba, kamar yadda Ibn Abbas radhiyallahu anhu bai ja da Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu ba.
(B)-Kuma koda ma za’a kaddara cewa Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhuma da Jabir Ibn Abdullahi radhiyallahu anhuma ba su janye fatawarsu ba har suka mutu, to, ba za a yi aiki da fatawarsu ba, tunda hana yin auren mutu’a ya tabbata daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.
Amma maganar da suka yi cewa: Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya hana yin auren mutu’a ne saboda wata manufa ta siyasa, to, wannan ba abin sallamawa ba ne, domin kuwa Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya yi haka ne don sanarwa da aiwatar da abinda ya ji daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama na hana mutu’a. Kamar yadda aka rawaito daga Salim Ibn Abdallah daga babansa radhiyallahu anhu ya ce:
صَعِدَ عُمَرُ الْمِنْبَرَ فَحَمِدَ اللَّهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ ثُمَّ قَالَ : مَا بَالُ رِجَالٍ يَنْكِحُونَ هَذِهِ الْمُتْعَةِ وَقَدْ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ -صلى الله عليه وسلم- عَنْهَا لاَ أُوْتَى بِأَحَدٍ نَكَحَهَا إِلاَّ رَجَمْتُهُ.
Ma’ana:
Sayyadina Umar radhiyallahu anhu ya hau mimbari ya godewa Allah ya yi yabo a gare shi, sannan ya ce: mene ne ya sa wasu mazaje suke yin auren mutu’a, bayan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya hana? To duk wanda aka kawo mini shi ya yi auren mutu’a sai na jefe shi(a matsayin haddi, muddin ya taba aure).
Abinda ke karfafa maganar Sayyadina Umar radhiyallahu anhu shine hadisin da ya zo daga Urwatu Ibn Zubair ya ce:
أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ الزُّبَيْرِ قَامَ بِمَكَّةَ فَقَالَ إِنَّ نَاسًا – أَعْمَى اللَّهُ قُلُوبَهُمْ كَمَا أَعْمَى أَبْصَارَهُمْ – يُفْتُونَ بِالْمُتْعَةِ – يُعَرِّضُ بِرَجُلٍ – فَنَادَاهُ فَقَالَ إِنَّكَ لَجِلْفٌ جَافٍ فَلَعَمْرِى لَقَدْ كَانَتِ الْمُتْعَةُ تُفْعَلُ عَلَى عَهْدِ إِمَامِ الْمُتَّقِينَ – يُرِيدُ رَسُولَ اللَّه صلى الله عليه وسلم فَقَالَ لَهُ ابْنُ الزُّبَيْرِ فَجَرِّبْ بِنَفْسِكَ فَوَاللَّهِ لَئِنْ فَعَلْتَهَا لأَرْجُمَنَّكَ بِأَحْجَارِكَ. قَالَ ابْنُ شِهَابٍ فَأَخْبَرَنِى خَالِدُ بْنُ الْمُهَاجِرِ بْنِ سَيْفِ اللَّهِ أَنَّهُ بَيْنَا هُوَ جَالِسٌ عِنْدَ رَجُلٍ جَاءَهُ رَجُلٌ فَاسْتَفْتَاهُ فِى الْمُتْعَةِ فَأَمَرَهُ بِهَا فَقَالَ لَهُ ابْنُ أَبِى عَمْرَةَ الأَنْصَارِىُّ مَهْلاً. قَالَ مَا هِىَ وَاللَّهِ لَقَدْ فُعِلَتْ فِى عَهْدِ إِمَامِ الْمُتَّقِينَ. قَالَ ابْنُ أَبِى عَمْرَةَ إِنَّهَا كَانَتْ رُخْصَةً فِى أَوَّلِ الإِسْلاَمِ لِمَنِ اضْطُرَّ إِلَيْهَا كَالْمَيْتَةِ وَالدَّمِ وَلَحْمِ الْخِنْزِيرِ ثُمَّ أَحْكَمَ اللَّهُ الدِّينَ وَنَهَى عَنْهَا
Ma’ana:
Abdullahi Ibn Zubair radhiyallahu anhu ya mike a Makka yana mai huduba sai ya ce: “hakika wasu mutane Allah ya makantar da zukatansu kamar yadda ya makarantar da idanunsu, suna ba da fatawa da yin auren mutu’a”. Yana yin shagube ne ga wani mutum. Sai (Abdullahi Ibn Abbas radhiyallahu anhu) ya kirawo shi ya ce: lallai kai mai kausasa harshe ne, wallahi mutu’a ta kasance ana yin ta a zamanin Shugaban masu takawa (wato. Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama). Sai Ibn Zubair radhiyallahu anhu ya ce: to kai ka je ka yi mutu’ar mana, to, wallahi idan kuwa ka yi sai na sanya an jefeka da duwatsu(a matsayin haddi). Sai Ibn Shihab ya ce: “Khalid Ibn Muhajir ya ba ni labari cewa: yayin da yake zaune a wajen wani mutum, sai wani mutum ya zo masa ya tambaye shi halaccin auren mutu’a, sai ya ba shi fatawa da yin sa, sai Ibn Abi Amratal Ansariy radhiyallahu anhu yace da shi; ka bi a hankali! Sai ya ce: mece ce ita? Na rantse da Allah an yi ta a zamanin Shugaban masu takawa, sai Ibn Abi Amr radhiyallahu anhu ya ce: ai ita(mutu’a) rangwame ce a farkon Musulunci ga wanda ya matsu kamar yadda aka halatta mushe da jini da naman alade ga wanda ya matsu. Sannan bayan Musulunci ya cika sai aka haramta ta”.
3- Ita kuwa hujjarsu ta hankali cewa: auren mutu’a amfani ne kubutacce daga muni, ba abin da hankali mai kyau zai sallama masa ba ne, domin kuwa ita ce mafi tsantsar cutarwa ga macen da aka yi mutu’a da ita da kuma dan da ta haifa ta hanyar mutu’a; saboda duk matar da take bayar da kanta ga mazaje barkatai su sadu da ita da sunan mutu’a, ko shakka babu za ta wayi gari da ‘ya ‘ya an tafi an barta da su barkatai, Idan ba haka ba, ta fuskanci barazanar zubar da cikin, kuma maza za su rika gudar auren ta aure na hakika, don haka za ta sami kanta cikin kaskanci a idanun jama’a, sannan kuma, kowa yana iya neman saduwa da ita kamar karuwa. Haka kuma dan da ta haifa zai wayi gari ba shi da uba, ana yi masa kallon dan zina, don mai auren mutu’a ba ya so a jingina masa dan da aka haifa a dalilin mutu’ar. Kuma auren mutu’a, ana yin sane kawai don sha’awa, ba don samun zuriya ba. Sannan kuma babu rahama ballantana tausayin da Allah ya sanya a tsakanin ma’aurata wadanda suke saukaka rabuwa bayan an yi aure. Haka kuma matar da aka yi mutu’a da ita ba ta takaba ballantana iddar da Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya yi umarni da yin su.
Haka kuma duk hujjar da aka kafa da hankali ta sabawa nassi, to, ba za a yi la’akari da ita ba.
4- Dangane da maganar ijma’in Ahlulbaiti a kan auren mutu’a kuwa, bai tabbata ba,
A)- domin sanannen abu ne cewa Zaidu Ibn Aliyu yana tare da Jumhurun malamai a bisa haramcin auren mutu’a, ga shi kuma yana daga cikin manyan Ahlulbaiti.
B)-Sannan ga Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu wanda shi ne kololuwa a cikin shugabannin Ahlulbaiti shima ya haramta auren mutu’a, kamar yadda hadisi ya gabata.
Bari ma shi ne wanda ya rawaito hadisin da ke hana auren mutu’a a yakin Khaibar.
C)- Sannan an rawaito daga Abdullahi Ibn Sinan ya ce:
Na tambayi Abu Abdullahi (Ja’afarus Sadik) alaihis salam dangane da hukuncin mutu’a, sai ya ce: kar ka kuskura ka kazanta kanka da ita.
D)- Haka kuma an rawaito daga Ammar ya ce : Abu Abdullahi alaihis salam ya ce da ni da Sulaiman bn Khalid: hakika an haramta auren mutu’a”.
E)- kuma Aliyu bn Yakzin ya tambayi Abu Hassan alaihis salam a kan mutu’a, sai ya ba shi amsa cewa : Mene ne ya hada ka da mutu’a? Allah ya wadatar da kai ga barinta”.
Wannan ne ya sanya babban malamin nan na Malikiyya wato Hafiz Ibn Abdulbar ya ce:
Malamai sun hadu akan cewa : “auren mutu’a haramun ne” daga cikin su akwai Imam Malik da almajiransa, da manyan malaman Madina da Sufyanus Sauri da Abu Hanifa daga malaman Kufa da Imamus Shafi’i da Imamul Lais bn Sa’ad daga malaman Misra da Magrib da Auza’i daga cikin Manyan malaman Sham, da Imam Ahmad bn Hanbal da Ishak da Abu Saur da abu Ubaidah da Dawuduz Zahiri da Imamud Dabari, dukkansu sun tafi a kan haramcin auren mutu’a.
Dalilansu kuwa su ne:
i- fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ (29) إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (30) فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ (31) المعا رج: 31 – 29
Ma’ana:
(Hakika muminai) sune wadanda suke kiyaye farjinsu. Saifa ga matayensu, ko kuma abin da suka mallaka na kuyangi, hakika su ba abin zargi ba ne. Wanda ya nemi (wani abu) koma bayan wancan, wadannan sune suka ketare dokokin Allah…..
Dalili a cikin wannan aya shi ne; bai halatta mutum ya sadu da wata mace ba, sai matarsa ta aure ko kuyangar da ya mallaka kamar yadda ya gabata.
Ita kuwa wadda ake zaman mutu’a da ita, ba matar auren da shari’a ta yarda da ita ba ce kuma ba kuyanga ba ce, kuma yin hakan bayan haramta shi, ketare dokokin Allah ne. Dalilan da suke karfafa cewa matar mutu’a ba matar aure ba ce, kuma ba kuyangar da aka mallaka ba ce su ne:
a)- Idan matarsa ce da sun gaji junansu(idan daya a cikin su ya rasu kafin karewar muddar su). Saboda fadin Ubangiji subhanahu wa ta’ala cewa:
وَلَكُمْ نِصْفُ مَا تَرَكَ أَزْوَاجُكُمْ إِنْ لَمْ يَكُنْ لَهُنَّ وَلَدٌ… النساء: 12
Ma’ana:
Kuma kuna da rabin abin da matanku suka bari, idan sun kasance ba su da `ya`ya…
b)- Kuma idanda matarsa ce sai a tabbatar masa da dan da ta haifa ta hanyar mutu’ar, saboda fadin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama cewa:
الولد للفراش وللعاهر الحجر
Ma’ana:
Da ana danganta shi ne zuwa ga ubansa (idan har matar aure ce ko sadaka), amma wanda ya yi zina da matar aure ko sadaka har ta yi ciki, to, shari’a ta hana shi wannan dan*.
Amma masu da’awar yin auren mutu’a, ba’ma’ sa son danganta dan mutu’a zuwa ga ubansa, saboda matar da aka yi mutu’ar da ita ba ta zama matar firash (matar aure) ba.
c)- Haka kuma idanda matarsa ce da za ta yi masa idda, idan sun rabu ko ya mutu, domin matan aure na shari’a sune Allah ya hukuntawa wadannan al’amuran, amma babu idda a cikin auren mutu’a.
Duk wadannan hukunce-hukuncebabu nassi infantacce da ya kebance matar mutu’a; wanda hakan ya nuna ita ba matar aure ba ce. Ita wata rukusa ce da musulunci yayi a wani lokaci kafin a haramta ta. Kamar yadda giya ba a haramta ta rana daya ba, amma haramcinta a yanzu har tashin kiyama ne.
iii)- Dalilansu kuma daga sunna su ne kamar haka;
1- Hadisin da ya tabbata daga Sayyadina Aliyu radhiyallahu anhu na hana auren mutu’a a Khaibar, kamar yadda ya gabata cewa:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم نَهَى عَنْ مُتْعَةِ النِّسَاءِ يَوْمَ خَيْبَرَ وَعَنْ أَكْلِ لُحُومِ الْحُمُرِ الإِنْسِيَّةِ.
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya hana yin auren mutu’a da cin naman jakin gida a ranar yakin Khaibar.
2- Hadisin da ya tabbata daga Rabi’i Ibn Sabrata radhiyallahu anhu ya ce:
أَذِنَ لَنَا رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم بِالْمُتْعَةِ فَانْطَلَقْتُ أَنَا وَرَجُلٌ إِلَى امْرَأَةٍ مِنْ بَنِى عَامِرٍ كَأَنَّهَا بَكْرَةٌ عَيْطَاءُ فَعَرَضْنَا عَلَيْهَا أَنْفُسَنَا فَقَالَتْ مَا تُعْطِى فَقُلْتُ رِدَائِى. وَقَالَ صَاحِبِى رِدَائِى. وَكَانَ رِدَاءُ صَاحِبِى أَجْوَدَ مِنْ رِدَائِى وَ كُنْتُ أَشَبَّ مِنْهُ فَإِذَا نَظَرَتْ إِلَى رِدَاءِ صَاحِبِى أَعْجَبَهَا وَإِذَا نَظَرَتْ إِلَىَّ أَعْجَبْتُهَا ثُمَّ قَالَتْ أَنْتَ وَرِدَاؤُكَ يَكْفِينِى. فَمَكَثْتُ مَعَهَا ثَلاَثًا ثُمَّ إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم قَال مَنْ كَانَ عِنْدَهُ شَىْءٌ مِنْ هَذِهِ النِّسَاءِ الَّتِى يَتَمَتَّعُ فَلْيُخَلِّ سَبِيلَهَا.
Ma’ana
Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya yi mana izinin yin auren mutu’a ranar fat’hu Makka, sai na tafi ni da wani mutum zuwa wata mace daga kabilar Banu Amir kamar budurwar (Kabilar Aiza’a) sai muka bijirar da kanmu gare ta domin mu yi mutu’a da ita, sai ta ce; mai za ku ba ni? Sai na ce bargona, sai abokina ma ya ce: bargonsa, bargon abokin nawa ya fi kyau, ni kuma na fi shi samartaka, idan ta dubi bargon abokina sai ya burgeta, idan kuma ta dube ni sai samartakata ta burgeta, sai ta ce: kai da bargonka kun ishe ni, sai muka zauna tare da ita kwana uku, sannan sai Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya ce: duk wanda yake tare da matar mutu’a, to, ya rabu da ita.
A wata ruwayar kuma Rabi’u Ibn Sabratal Juhani ya ce:
أَنَّ أَبَاهُ حَدَّثَهُ أَنَّهُ كَانَ مَعَ رَسُولِ اللَّه صلى الله عليه وسلم فَقَالَ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّى قَدْ كُنْتُ أَذِنْتُ لَكُمْ فِى الاِسْتِمْتَاعِمِنَ النِّسَاءِ وَإِنَّ اللَّهَ قَدْ حَرَّمَ ذَلِكَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ فَمَنْ كَانَ عِنْدَهُ مِنْهُنَّ شَىْءٌ فَلْيُخَلِّ سَبِيلَها وَلاَ تَأْخُذُوا مِمَّا آتَيْتُمُوهُنَّشَيْئًا.
Ma’ana:
Lallai babansa (Sabratal Juhanī radhiyallahu anhu) ya ba shi labarin cewa: Hakika sun kasance tare da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sai ya ce: Ya ku mutane! Hakika da na yi muku izinin yin mutu’a, amma yanzu Allah ya haramta ta har zuwa ranar alkiyama, saboda haka duk wanda yake tare da matar mutu’a, to, ya sallame ta, kuma kada ku karbi komai daga abin da kuka ba su.
iv)- Dalilinsu na hankali sun ce: Aure ana yin sane don wasu manufofi, ba wai don sha’awa kadai ba, auren mutu’a kuwa babu wadannan manufofin a cikinsa, sai dai kawai biyawa kai bukata ta sha’awa.
v)- Dalilinsu na ijma’i; suka ce: Hakika al’ummar musulmi sun tafi a kan haramcin auren mutu’a tunda Allah da Manzonsa sallallahu alaihi wa sallama sun hana yinsa tun a ranar fat’hu Makka har zuwa ranar tashin Akiyama, don haka ya zama dole a hanu, ba kuma za a saurari maganar kowa ba. Allah ya fahimtar da masu yi su dena.
Kuna iya neman wannan littafi da na wallafa mai suna “Tsarabar ma’aurata” don Karin fa’idoji da kuma mara’ji’i. Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala a’lihi wa sahbihi ajma’iin.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: