Sallar walaha Sallar masu koma wa zuwa ga Allah

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ

ﺫﺭ رضي الله عنه  ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻧﻪ ﻗﺎﻝ :

” ﻳﺼﺒﺢ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺳﻼﻣﻰ ﻣﻦ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺻﺪﻗﺔ، ﻓﻜﻞ

ﺗﺴﺒﻴﺤﺔ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﺤﻤﻴﺪﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻬﻠﻴﻠﺔ

ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻛﻞ ﺗﻜﺒﻴﺮﺓ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﺃﻣﺮ ﺑﺎﻟﻤﻌﺮﻭﻑ

ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻧﻬﻲ ﻋﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﺻﺪﻗﺔ، ﻭﻳﺠﺰﺉ ﻣﻦ ﺫﻟﻚ

.ﺭﻛﻌﺘﺎﻥ ﻳﺮﻛﻌﻬﻤﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﺤﻰ

رواه مسلم:720


Manzon Allah(Sallallahu alaihi wasallam) yace ‘Kowani Gaɓa yana wayan gari da sadaka akansa.(Ma’ana wanda za’a ƙaddamar masa )

Toh sai yaci gaba da cewa ‘Kowata tasbihi(Subhanallah) da mutum zaiyi sadaqa ce, ko wata tahmidi(Alhamdulillah) da mutum zaiyi sadaka ce. Ko wata tahlili(La’ilaha illallah) da mutum zaiyi sadaqa ce. Kowace takbiri(Allahu Akbar) da mutum zaiyi sadaka ce. Umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna ma sadaka ce. Amma duka wa’innan ayyuka da aka lissafa, ‘Sallah raka’a biyu ta walaha ta isar wa mutum’ (wato in mutum yayi wannnan raka’a biyu ta adduha ta wadatar masa. ya sauke nauyin wannnan sadaƙar dake kan gaɓoɓinsa)


Kaman yadda akace, mutum yana da gaɓoɓi tsakanin babba da ƙarami guda 360 a jikinsa.
Sannan ita salatu-dduha sunnah ce wanda akeso musulmi ya lazimceta. Domin falalarta kamar yadda tazo a hadisai da dama wanda wannan hadisin yana cikinta. A wani wuri annabi yace:

Sallahce ta masu maida lamari ga Allah(Ma’ana masu yawan tuba)

Muslim ya rawaito hadisi ta 748

Yawan raka’ointa:


Sallar raka’a biyu ne yayi sama.
Ma’ana: In kayi raka’a biyu ta wadatar. In ka ƙara kuma ka samu ƙarin lada.

Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda ya rawaito cewa annabi yayi masa wasici yace:

أَوْصاني خليلي صلَّى اللهُ عليه وسلَّم بثلاثٍ: صيامِ ثلاثةِ أيَّامٍ من كلِّ شهرٍ، وركعتي الضُّحى، وأنْ أُوتِرَ قبل أنْ أنامَ

Bukhari ya rawaito hadisi na: 1981

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yayi min wasiyya da abu uku:

1. Yin azumin kwana uku a kowani wata

2. Raka’oi biyu na walaha

3. yin wutiri kafin nayi bacci

Aciki ya ambaci cewa raka’oi biyu na walaha. Sannan kuma an rawaito annabi ya ƙara akan raka’oi biyu. Shiyasa sallar na fara wa ne daga raka’oi biyu zuwa sama. Hudu, ko takwas ko kuma yayi sama. Wasu maluma sun ƙayyade shi da raka’a takwas, amma magana mafi inganci shine zaka iya yin ko raka’a nawa kaga zaka iya yi.

Lokacin Sallar walaha:

Lokacinta na farawa bayan bullowan rana kaman da minti 15 kuma tana fita kafin lokacin azahar da mintoci. Amma anfiso ayita a karshen lokaci ga wanda keda dama. Kaman ana saura awa ɗaya ko biyu ayi sallar azahar. Kaman yanda annabi yayi nuni da cewa ‘Lokacin da rana tayi zafi’ ai lokacinta. Amma in mutum yayi kafin wannan lokaci yayi daidai. Allah sa mudace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories