ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Fitowa Ta 41(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Da sunan Allah za mu shiga:
FASALI NA UKU
Tarihin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Daga Annabta Zuwa Hijira
Gari ya waye
Kafin cikar shekarun manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam arba’in halin da duniya take ciki ya kara rikicewa. Jahilci ya yi kanta a cikin mutane domin sun dimauta daga bin mahaliccinsu. Amma shi kam ya kasance mafi tsarkin mutane, kuma mafi nisantar su daga aikin assha. Bai taba halartar wani buki na addinin gumaka ba. Bai taba sha’awar giya ba balle ya kurba ta. Haka kuma bai taba shiga caca ba duk da kasancewar mutane a lokacin ba su ganin illar ta. A daidai wannan lokacin ne ya rinka yin mafarki, idan aka tashi da safe sai abinda ya gani a cikin mafarki ya faru kamar an kifa kwarya a kan ‘yar uwarta. Daga bisani sai aka sanya ma sa sha’awar kebanta da nisantar jama’a saboda tunaninsa da nasu ya banbanta. Ra’ayinsu ya yi hannun riga. Al’adunsu na jahiliyya kuma sam ba su burge shi. Saboda haka sai ya zabi wani wuri nesa da mutane, can a kan hanyar garin Ta’if, a kan wani dutse mai suna “Jabal An-Nur”. Ya samu wani kogo ana ce da shi “Hira’” ya rava cikin sa yana bautar ubangiji mahalicci bisa iya abinda ya sani a wancan lokaci daga “Hanifiyya”; addinin annabi Ibrahim Alaihis Salam.
Wani abin da ya rinka ba shi mamaki a wannan lokaci shi ne, jin gaisuwar girma ta musamman wacce bai saba da irin ta ba daga wani dutse da yake shudewa kusa da shi. Sahihu Muslim, littafin Fadha’il, babin falalar nasabar manzon Allah da gaisuwar dutse gare shi. Da kuma As Sirah An-Nabawiyyah, na Ibn Hisham (1/234-235).
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kan yi wannan khalwa ne a cikin kowane watan Ramadhan shekaru uku a jere kafin samun annabtar sa. Idan ya samu wasu ‘yan kwanaki guzurinsa ya kare sai ya dawo gida ya sake shirin komawa. A shekarar sa ta uku ne, sa’adda yake kusan cika shekaru arba’in a duniya yana cikin wannan kogo sai bakon arziki, wato (Jibril (AS)) ya same shi da sakon Allah duk da yake a lokacin bai san abinda sakon yake nufi ba.
Mu bari Nana Aisha -uwar muminai- ta ci gaba da ba mu wannan labari..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates