ALKAKI DA RUWAN ZUMA22(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 22
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam A Gidan Baffansa Abu Talib
A lokacin da ajali ya gabato ma
Abdulmuttalibi abu na farko da ya fara
mayar da hankali gare shi shi ne
wasicci ga wanda zai kula ma sa da
jikansa. Wanda ya dora ma wannan
muhimmin aiki kuwa shi ne dansa Abu
Talib. To, sai dai a wancan lokaci Abu
Talib yana cikin karancin halin rayuwa.
Don haka sai Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya dukufa wajen
neman abin hannunsa don ya taimaka
ma baffan nasa. Ya zabi sana’ar kiwon
tumaki wadanda yakan yi jinga da
ma’abotansu a kan kiwon su. Wannan
ba abin mamaki ba ne domin ‘yan
uwansa annabawan Allah dukkansu
sunyi kiwo kamar yadda shi da kansa
Sallallahu Alaihi Wasallam ya fada.
(Sahihul Bukhari 2262). Kuma Allah
Tabaraka Wa Ta’ala ya labarta ma na
cewa, annabinsa Musa (AS) ya yi
jingar kiwo ma surukinsa. Suratul
Qasas 25-29. Wasu daga cikin su kuma
sun yi karin wasu sana’oi daban daban.
Alal misali, annabi Nuhu (AS) ya yi
aikin kafinta. Annabi Idris (AS) ya yi
sakar hannu. Annabi Dawud (AS) ya
yi sana’ar qira. Haka ne shi ma annabin
mu Muhammad Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi kiwon tumaki a lokacin
kuruciyarsa yana karbar jinga daga
mutanen Makka. (Sahihul Bukhari,
Kitabul Ijara, Bab Ra’yil Ganam Ala
Qararit, hadisi na 2262. Malamai sun
zayyana irin dabi’un kirki da makiyaya
ke samu, musamman kiwon tumaki.
Wadannan dabi’u sun hada da:
1. Hakuri
2. Natsuwa
3. Kankan da kai
4. Jarunta
5. Tausayi
6. Kokarin neman abinci dss
Babu shakka kuwa duk wanda ya saba
da kiwon tumaki – dabbobin da suka fi
kowadanne rashin natsuwa da bin oda –
ba zai gaza ba wajen kiwon ‘yan adam
duk yadda rashin hankalinsu ya
kasance.
Wani darasi da ya kamata mu koya a
nan shi ne, neman abinci shi ne
rayuwar annabawa, ba zama ci-ma-
kwance ba. Don haka musulunci yana
karfafa mu mu tashi tsaye domin
samun na kanmu. Yin maba da maula
da roko da banbadanci duka dabi’u ne
na kasa da ba su dace da musulmi
nagartacce ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates