Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 23
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam A Lokacin Samartaka
Saurayi, a ilimin sanin halayyar dan
Adam, mutum ne mai wuyar sha’ani.
Ga shi dai da gaggawa cikin al’amari,
ga ji-ji-da-kai ga kuma son jin dadi.
Ba kasafai kake samun saurayi ba shi
da wasu fizge-fizge ba wadanda
dattawa ke kallo a matsayin kauce ma
hanya. Shi kam manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ba haka
samartakarsa ta kasance ba. Ya yi
rayuwa tsaftatacciya abin burgewa
wadda ba abin da dattijai zasu ce ma sa
sai mashaallahu! Bari mu dan kawo
wasu abubuwa da suke nuna mana
halayyarsa a irin wannan lokaci.
1. Fatauci:
A daidai lokacin da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya cika
shekaru goma sha biyu ya fita sau daya
a tare da baffansa Abu Talib zuwa
fatauci a kasar Sham. A cikin ayarin da
suka tafi kuwa akwai dattawa daga
cikin manyan Quraishawa.
An ba da labarin cewa, sun hadu da
wani malami daga cikin malaman
Nasara mai suna Jarjis, ana kuma kiran
sa Bahira wanda ya lura da dukkan
alamomin annabta daga fuskar jikan
Abdulmuttalibi, kuma a kan haka ya
girmama su, sannan ya hane su da
tafiya da shi cikin yankin Rumawa. Ya
ce, idan Rumawa suka kyalla idon su a
kan manzon Allah za su gane shi kuma
za su kulla ma sa sharri ko su hada shi
da wata cuta. (Al-Jami’u na Tirmidhi,
hadisi na 3620 da Sahih As-Sirah An-
Nabawiyyah na Ibrahim Al Ali, shafi
na 58-59. Sai dai akwai jayayya mai
karfi a tsakanin masana dangane da
ingancin faruwar wannan lamari. Sanin
gaibu sai Allah).
2. Harbul Fijar
Kamar yadda muka fadi a can baya
kafin bayyanar musulunci an yi yakoka
masu yawa a tsakanin kabilun
larabawa. Daga cikin fitattun yakokan
su kuwa akwai jerin yakoka da ake
kira “Harbul Fijar” yakin fajirci saboda
sun saba ma ka’ida don an yi su a cikin
gari mai alfarma.
Wannan yaki ya kai tsololuwa a
lokacin da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ke da shekaru
goma sha hudu (14). Yakin kuma ya
gudana ne a tsakanin kabilarsa ta
Quraish tare da hadin guiwar kabilar
Kinanata da kuma kabilar Hawazin
wacce ta kawo ma su takakka har a
cikin birnin Makka. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya shedi
wannan karafkiya a tare da
baffanninsa, kuma bai tsaya a matsayin
dan kallo ba wajen kare alfarmar gari
mai albarka duk da yake a lokacin yana
matashi ba za a sa shi a cikin sojoji ba.
Duk da haka ya ba da tasa gudunmawa
domin kuwa shi ya rinka kwashe kibau
da abokan gaba ke jefowa yana tsara
su waje daya ya mayar da su ga ‘yan
uwansa domin su kuma su yi amfani
da su wajen mayar da martani. Babu
shakka wannan yana nuna irin
jaruntaka da sadaukantakar da ya
kasance a kan ta a daidai wannan
lokaci. (As- Sirah Al- Halabiyyah, na
Ali Al- Halabi, (1/127-129).
Leave a Reply