ALKAKI DA RUWAN ZUMA25( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 25
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam A Lokacin Samartaka
4. Aure Da Gina Iyali
A daidai lokacin da manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya kai
shekaru ashirin da biyar ya yi fice a
wajen sadaukantaka da halin girma.
Ba wani gida daga cikin gidajen
Quraish face suna farin cikin in da zai
nemi aure a gidansu. Ba kuma wata
mace daga cikin su karama ce ko
babba da ba zata yi murna ba idan
aka ce Muhammad ne Sallallahu Alaihi
Wasallam yake neman auren ta. A
daidai wannan lokacin ne Sallallahu
Alaihi Wasallam ya nemi aure. To,
amma abin sha’awa shi ne bai nemi
auren karamar yarinya ba. Wacce ya
nema ita ce khadija ‘yar gidan
Khuwailid, bazawara ‘yar babban gida
da ta yi aure har sau biyu kuma tana
da ‘ya’ya. As-Siratun Nabawiyyah, na
Sallabi, shafi na 59-61.
A game da dalilin aurensu, da yawan
marubuta sun kawo labarin cewa,
kasuwanci ne ya fara hada su in da
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya je birnin Sham tare da
bawanta Maisara suka yi fatauci da
dukiyarta. Aka ce bayan da ta ga
albarkokin wannan bawan Allah ne, da
kanta sai ta nemi kulla zumuntar aure
da shi kuma ta aiki kawarta Nafisah
bint Munabbih wadda ta shirya ma sa
maganar kuma ya amince da ita.
Asalin wannan ruwaya ta fito ne daga
littafin shaihun malamin nan Ibnu
Ishaq amma fa ba ta da isnadi. Don
haka malamai ba su karfafa ta ba. Shi
kam zancen auren tabbatacce ne har a
mafi ingancin littafan ruwaya na
Bukhari da Muslim.
Babu wani sabani cewa, shekarun
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam a lokacin auren 25 ne.
Amma game da shekarun amaryar tasa
ruwayoyi sun yi sabani. A lokacin da
fitaccen malamin nan Waqidi yake
ganin ta kai shekaru 40, shi kuma
malam Ibnu Ishaq na ganin
shekarunta 28 ne. Wannan kauli nasa
kuwa babu shakka ya fi karfi. Domin
ko bayan kasancewar malamai na da
shakku wajen karbar kaulin Waqidi,
maganar Ibnu Ishaq ta fi kusa da
hankali. Domin kuwa mawuyacin abu
ne – a al’adance – macen da ta kai
shekaru 40 ta haifi ‘ya’ya 6 bayan
haka. A bisa wannan riwayar kenan
Nana Khadija ta girme shi ne da
shekaru 3. Kuma duk ‘ya’yan da Allah
ya ba shi ita ce ta haife su in ban da
Ibrahim wanda kuyangarsa Mariya ‘yan
asalin kasar Masar ta haifa. A cikin
ikon Allah kuwa ‘ya’yan nasa gaba
daya sun riga shi komawa ga Allah in
ban da ‘yar aurtan ‘ya’ya matansa; ita
ce sayyida Fatima. Ita kam ta rayu dan
lokaci kadan da bai shige wata shida
ba a bayansa.
Duba: Rasulullahi Fi Makka, shafi na
79.
Nana Khadija macce ce mai hakuri da
kaifin hankali da sanin ya kamata.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam da kansa ya kan nemi
shawararta a wasu al’amurra nasa.
Kuma babu shakka cewa, ya ji dadin
zama da ita fiye da yadda za a misalta.
Bayan so da kauna da ke tsakanin su
Nana Khadija ta taimaki maigidanta
matuka a lokacin da bai da wata
madafa in ba tata ba. Shi ya sa ma
bai taba tunanin kara aure ba duk
tsawon rayuwarta. Sun yi shekaru 21
tare da ita sannan Allah ya karbi ranta.
Kuma yakan fadi alherinta ko bayan
mutuwar ta har a gaban iyalansa. Abin
da Nana A’isha ta ce ya kan motsa
kishi a zuciyarta amma ba yadda za ta
yi domin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam mutum ne da ba ya
manta alheri ko kankane ne aka yi ma
sa ballantana kuma alherin babbar
masoyiyarsa uwar ‘ya’yansa. Sahihu
Muslim, Kitab Fadha’il As-Sahaba,
hadisi na 2437.
Babu shakka wannan uwa ta
mummunai ta karantar da mu abubuwa
da dama. Kuma a dalilin aurenta
al’ummar musulmi sun karanci
darussa da hukunce hukunce masu
amfani. Da farko dai mun gano cewa,
halas ne ga namiji ya auri matar da ta
girme shi, ita ma halas ne ta auri
wanda bai kai shekarunta ba. Sannan
halas ne mace ta nuna kanta ga
mutumin kirki don neman ya aure ta.
Kuma ya halasta namiji ya tare da
matarsa a gidanta idan shi bai mallaki
gida ba. Mun kuma fahimci cewa,
auren macce mawadaciya ga namiji
talaka ba laifi ba ne kuma ba aibi ba
matukar akwai so da kauna da
mutuntawa. Idan ma har ta taimaka
bisa radin kanta ta dauke ma sa wasu
nauye-nauyen gida da kudinta kuma a
haka ta kyautata ba ta yi laifi ba.
Macce kuma – bisa ga darasin da
Nana Khadija ta koya ma al’umma –
ita ce babban jigon da namiji
managarci. Shi ya sa masu hikima ke
cewa, duk in da ka ga namiji ya
gawurta akwai nagartacciyar macce a
bayansa. Ar-Rahmah Al-Muhdah, na
Sheikh Dr. Ali Muhammad As-Sheikh,
shafi na 98.
Nana Khadija dai ba wani mahaluki da
manzon girma ya amfana da shi a
farkon rayuwarsa ta addini kamar ta.
Shi ya sa da aka tambayi shehin
musulunci Ibnu Taimiyyah game da
matsayinta da na kanwarta uwar
mummunai A’isha sai ya sa hikima, ya
ce, a farkon musulunci Khadija ita ce
mafificiyar macce wacce ta taimaki
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ta hanyar karfafa shi da
taimakon da’awarsa. A karshen
musulunci kuma Nana A’isha ita ce
mafificiya wacce ta kiyaye ma
musulmi kaffatanin rayuwar manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da
irin basirar da Allah ya ba ta. Har ya
zama ba wani hukunci da ya danganci
rayuwarsa face an samo wani ilmi mai
albarka dangane da shi a wurin ta.
Babban darasi ga malamai magadan
annabawa a cikin wannan lamari shi
ne su rinka taka-tsantsan wajen
neman aure. A maimakon kyau da
kuruciya su nemi asuli da tarbiyya da
nagarta.
A cikin mutuwar ‘ya’yan manzon Allah
tun a rayuwarsa akwai darasi babba.
Manzon Allah ya dandani zafin
mutuwarsu kamar yadda ya dandani
zafin mutuwar iyayensa tun da wuri.
Haka ita ma uwar tasu manzon Allah
Sallallahu Alaihi wasallam ya dandani
zafin mutuwar ta wacce ta zo daidai
da mutuwar baffansa mai kyautata
kula da shi da ba shi kariya daga
makiya. Kada ka taba tsammanin idan
kana masoyin Allah ba zaka gamu da
matsalolin rayuwa ba. Ai duniya ba
komai ba ce a wurin Allah. Kuma
jarabawoyin rayuwa sukan kara ma
mumini kaifin hankali da sabawa da
hakuri da tausaya ma jama’a kamar
yadda jin dadin duniya idan ya yi yawa
yake sa dakilewar basira da karancin
hakuri da raina mutane. Ga kuma
dinbin lada da Allah ya yi tanadi ga
wanda ya yi hakuri da dacin rayuwa ya
mayar da al’amari ga Allah.
Wani muhimmin darasi kuma a nan
shi ne, lura da cewa, addinin
musulunci ba kayan gado ba ne.
Domin kuwa da haka ne abu ne mai
sauki ga madaukakin sarki ya raya ma
manzo ‘ya’yansa maza domin su gaje
shi. Allah dai ya yi ma sa ni’imar
haifuwa, bai zamo bakarariya ba. Ya
jiyar da shi dadin haifuwa na wani
lokaci sannan ya karbi abinsa. A cikin
wannan akwai sanyayawa ga wanda
aka ba shi aka amshe, ko kuma wanda
ba a ba shi ba ma sam. Sai su yi koyi
da ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam
a cikin hakurinsa da juriya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates