ALKAKI DA RUWAN ZUMA26( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa Ta 26
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam A Lokacin Samartaka
5. Ginin Ka’aba
Annabi Ibrahim Alaihis Salam shi ne
kakan annabawa kuma wanda ya bi
gumaka duk ya rugurguza su. Suratul
Anbiya’: 48. Haka kuma shi ne wanda
Allah ya daukaka shi da ginin dakin
Allah na farko a bisa doron kasa.
Allah Ta’ala ya umurce shi da yin
ginin wanda dansa Isma’il – kakan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya taimaka ma sa a kai.
Suratul Baqarah: 127-129.
Tsawon ginin Ka’aba a wancan lokaci
kamu tara ne, fadinta kuma kamu
talatin, a daya gefen kuma kamu
ashirin da biyu, sannan babu rufi a
saman ta. Yau da gobe ta sa wannan
ginin ya samu matsala musamman
bayan wata ambaliyar ruwa da aka yi
wacce ta kusa hadiye dakin, amma
saboda kwarjinin da dakin yake da shi
aka rasa wanda zai iya buge
bangayensa don a sabunta su. Daga
bisani Quraishawa suka yanke
shawarar sake wannan aiki a lokacin
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yana da shekaru talatin da
biyar (35) suka kuma sa sharadi cewa
duk wanda zai ba da gudunmawa ya
tabbatar ya zo da halas. Kada wanda
ya kawo kudin sata ko na zalunci ko
kudin karuwa. Wannan ne ya sa suka
rasa wadatar kayan aiki, abin da ya
janyo dole suka rage fadin Ka’aba a
kasa da kamu shida da rabi bayan sun
kara ma ta tsawo ninki biyu ta koma
kamu goma sha takwas daga kamu
tara da take a farko. Kuma a da tana
da kofofi biyu a kasa masu fuskantar
juna, sai suka rufe kofa daya, ita kuma
dayar suka daga ta ta yadda ba za a
iya shiga dakin ba sai da tsani don
kauce ma ambaliyar ruwa da kuma
wata manufa ta siyasa ita ce, kada
wanda ya shiga a cikin dakin sai da
izninsu. Suka kuma yi ma dakin Allah
rufi bayan a da a sake yake ruwan
sama na kwarara kai tsaye a cikin sa.
Quraishawa dai sun raba aikin kashi
kashi. Kowace kabila aka ware ma ta
inda ake son ta gina. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi ruwa
da tsaki a cikin wannan aiki na alheri
tare da baffanninsa da sauran
danginsa. Ya rinka dauko duwatsu a
bisa kansa tare da baffansa – kuma
tsaransa – Abbas dan Abdulmuttalib
suna kawo wa don taimaka ma
magina.
Wannan ya kara tabbatar da abin da
muka fadi a baya cewa, ayyukan alheri
ko da wa ana hada kai ayi su. Kuma
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam bai rayu daban da
mutanensa ba ko a lokacin
jahiliyyarsu. Kawai dai ya kaurace ma
su ne ga abubuwan da suke yi na
ma’asi da shirka.
A cikin wannan aikin na ginin Ka’aba
ne Allah madaukakin sarki ya bayyana
ma Quraishawa darajar manzonsa,
alama a kan cewa, lokaci ya yi kusa
da wannan taliki zai zo ma su da
hanyar warware matsala da duk wani
rikici a tsakanin su. Ba da dadewa ba
zai zo ma su da hanya mikakkiya
wadda za ta sa su zauna lafiya, kuma
su ci ni’imar duniya da ta lahira idan
sun yi ma sa da’a. Abin da ya faru a
wannan lokaci shi ne, a lokacin da
gini ya iso daidai Hajarul Aswad, bakin
dutsen da Allah ya sauko ma annabi
Ibrahim (AS) shi daga aljanna (Dutsen
fari ne, zunuban ‘yan Adam suka
dushe haskensa. Al-Jami’ na Imam
at-Tirmidhi, hadisi na 877, kuma
Tirmidhi da Albani sun inganta shi)
sai Quraishawa suka yi sabani a kan
wanda zai dora shi a wurinsa. Kowace
kabila tana ganin za a yi ma ta gori
idan ba ita ce ta samu falalar sanya
shi ba. Rikici kuwa ya harde, abu
kadan ya rage ya koma yaki. Daman
da irin haka ne yaki yake somawa a
cikin su. Ana haka ne, sai Allah ya jefo
ma wani dattijo a cikin su tunani
cewa, mu sanya alkali da zai yi
hukunci a cikin wannan sha’ani. Kuma
idan ya yi hukunci duk mu amince da
abinda ya zartar. To, wane ne za a
sanya wanda ba zai yi son zuciya ya
gabatar da kabilarsa ba? Kawai sai
suka amince a bar wannan hukuncin
ga duk wanda Allah ya jefo shi ya fara
shigowa a wannan masallaci. Rufe
bakinsu ke da wuya sai ga
Muhammad (tsira da amincin Allah su
kara tabbata a gare shi) ya kunno kai
bai san abin da ake ciki ba. Sai ya ji
gaba daya an dauki shewa da tafi ana
cewa, mun amince, ga amintacce! Da
suka yi ma sa bayanin matsalarsu sai
Allah ya jefo ma sa hikima, ya sauke
mayafinsa ya shimfida shi, ya sa
hannayensa masu tsarki ya dauko
dutsen ya dora a mayafin nasa.
Sannan sai ya ce ma su, kowace
kabila ta ba ni wakili guda daya. Sai
ya umurci wakilan nan da su kama
sassan mayafin nan su cira shi daidai
wurin da za a dora dutsen sannan ya
sake sa hannunsa ya dauko Hajarul
Aswad ya dora shi a wurinsa.
Allahu akbar! Ashe tuntuni ga wanda
ya san makamar zaman lafiya da
adalci a cikin su amma ba su sani ba.
Da wannan sai ya samu darajoji guda
biyu; ga matsayin warware rikici da
kwantar da tarzoma ga kuma darajar
dora dutsen a wurinsa wadda rigima a
kan ta ce ta so ta haifar da yaki. Da
wannan ya samu karin kwarjini da
muhibba a cikin jama’a shekaru biyar
kafin annabtarsa.
Yan uwa, a nan ne muka kawo
karshen abin da Allah ya ba mu ikon
kawo ma ku dangane da rayuwar
fiyayyen halitta daga haifuwa zuwa
girma. Kafin mu soma da maganar
manzanci zamu yi waiwaye don amsa
wasu tambayoyi masu muhimmanci da
suka shafi matsayinsa da darajarsa.
Za mu soma da kara kyamarar tarihi
don ta dauko mana hoton wannan
mahaluki da ganin sa ya fiye mana
kome dadi a duniya.
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates