Musulunci Ya Samu Garkuwa
Bayan tafiyar muhajirai na farko su goma sha hudu babu abin da mushrikai suka kara a kan musulmi sai ta’addanci da ketare iyaka. A cikin haka ne watarana Abu Jahli ya tafka irin ta’asar tasa; ya kalli kwayar idon manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya zage shi, kuma ya yi ma sa izgili, ya yi kokarin muzanta shi. Fiyayyen halitta wanda ya fi kowa hakuri ya shude abin sa bai ce ma sa uffan ba. Ashe duk abin nan da ke faruwa a bisa idon wata kuyanga ‘yar gidan Abdullahi bn Jud’an (wanda manzon Allah ya taba sa hannu a kan wata yarjejeniya a kan ‘yancin masu rauni a gidansa). Sai wannan kuyanga ta kwashe labarin duk abin da ya faru ta fada ma Hamza, wanda yake baffan manzon Allah ne kuma abokin renon sa, tun da yake macce guda ce ta shayar da su nono. Hamza ya ce ma ta, tsakaninki da Allah a gabanki aka yi haka? Ta ce, kwarai. Nan take jinin Hashimanci ya motsa a cikin jikinsa, ‘kasa ta kasa daukar kafafunsa. Bai zarce ko ina ba sai majlisin kafirai in da Abu Jahli yake baje kolinsa. Da isar Hamza, ga shi saurayi mai karfi, kuma mafi kwarjinin samarin Makka. Bai tsaya wani dogon bahasi ba sai ya cira bakarsa ya watsa ta a kan Abu Jahli sai da ya yi ma sa mummunan rauni. Sannan ya ce, ya za ka zage shi ina kan addininsa?!
Allahu Akbar. A lokacin da Hamza ya furta wannan kalami bai kudure a zuci abin da ya fadi ba. Amma kuma ko da ya dawo hayyacinsa bayan fushi ya sake shi, sai ya sake nazarin abin da ya fada. To, mene ne illa idan na bi addinin d’ana amintacce wanda na tabbata Allah ya aiko shi, ba karya yake yi ba?
Wannan dan karen duka mai zafi da Abu Jahli ya sha watakila shi ne karo na farko da ya fara samun irin sa. Abin da ya sa da rikici ya barke tsakanin danginsu biyu, ya ce ku dakata. Wallahi ni ne na jawo jidali, don na ci mutuncin dan yayansa. Mukhtasar Siratin Nabiy, na Sheikh Muhammad bn Abdilwahhab, shafi na 90.
Labarin dukan da Abu Jahli ya sha a hannun Hamza sai ya rinka yaduwa a cikin jama’a, yana tafiya kafada da kafada da labarin musuluntar sa da ya ba da sanarwa. Wannan ya kashe jikin Quraishawa matuka. Kwana uku bayan haka, sai kuma suka ji Umar dan Khattabi shi ma ya musulunta.
Game da musuluntar Umar, wani al’amari ne na Allah da ya zo a matsayin ijaba ga du’ain manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam. Domin kuwa Khabbab bn Al-Arat ya ji manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana addu’a yana cewa, “Ya Allah! Ka karfafi addininka da wanda ka fi so a cikin biyu; Umar dan Khattabi ko Abu Jahli dan Hisham”. Umar saboda karfin jiki da jaruntarsa, Abu Jahli kuma saboda karfin iko da sarautarsa.
Har zuwa ranar da ya musulunta, Umar bai da wani sassafci ko dan kadan ga musulmi. Amma albarkacin wannan addu’a take Allah ya sanyaya zuciyarsa bayan da ya tarar da kanwarsa tare da mijinta, Sa’id bn Zaid suna karatun Alkur’ani a karkashin kulawar malamin da aka hada su da shi; Khabbab bn Al-Arat.
Da musuluntar sa, abu na farko da Umar ya yi shi ne, ya je wurin kawun nasa “Abu Jahli” ya kwankwasa kofarsa. A cikin lalama da fara’a ya ce ma sa “Maraba, lale. ‘Dana me ya kawo ka a wannan lokaci”? Umar ya ce, na zo ne in sanar da kai na bi Allah, na bi Muhammad manzon Allah! Da jin haka, a fusace, Abu Jahli ya tura ma sa kofa ya hada ma sa da zagi mummuna.
Bayan haka kuma sai ya tambaya, wane ne ya fi kowa yada labari a wannan gari? Aka ce ma sa Jamil Al-Jumahi. Ibnu Umar yana ba da labari, ya ce, sai na bi shi don na ga abin da zai faru. Wallahi bai gama fada ma Jamil sakon ba sai da ya zabura ya ruga zuwa kofar masallaci. Ya kuwa kwala ihu yana cewa, jama’a ku saurara! Umar fa ya karkace!! Shi kuma Umar yana bin sa yana cewa, karya yake yi. Na dai bi hanyar gaskiya. Ba da jimawa ba kuwa aka yi ma Umar taron dangi, suna duka yana dukan su. Amma da yake sarkin yawa ya fi sarkin karfi sai da suka kai shi kasa. A nan ne ya ce, wallahi da mun kai mutane 300 a musulunci, da Makka ta yi maku kamshin dan goma.
Daga wannan lamari musulmi suka fara samun kan su, aka daina muzguna ma su. Domin kowa yana tsoron haduwar sa da wadannan jarumawa guda biyu idan yana shi kadai. A hankali ma sai suka fara fitowa masallaci suna yin sallar su ba tare da fargaba ba. Wannan shi ne labarin da ‘yan gudun hijira na farko suka ji suka dauka gari ya yi sanyi suka dawo.
Ku biyo mu a darasi na gaba don jin yadda aka kaya har musulmi suka sake yin hijira karo na biyu.
Allah ya hada mu da alheri.
Leave a Reply