Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya Dawo Gida
Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya zo shiga Makka sai ya yi wata siyasa wacce take cike da hikima bisa ga halin da ya bari da wanda ya tabbatar zai samu a garin. Sai da ya yi nazari mai zurfi sai ya zabi Mut’im bn Adiy; daya daga cikin wadanda suka kafa wancan kwamiti na yaga takardar zalunci da aka lika ga Ka’aba wadda ta wajabta masu daurin ta-la-la na tsawon shekaru, sai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya aika ma sa cewa, yana rokon shiga Makka a karkashin kariyarsa. Mut’im bai yi wata-wata ba ya ba da shela a cikin garin Makka cewa ya amintar da Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, kuma yana kalubantar duk wanda yake tunanin taba shi ko ya yi ma sa wulakanci. Sannan ya gayyato ‘ya’yansa suka fito da takubba suka shigar da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam har cikin masallaci ya yi dawafi ya yi sallah, sannan suka raka shi gidansa ba wani wulakanci da ya same shi.
Mut’im dai shugaban gidan Naufal dan Abdu Manaf ne. Kuma ya mutu a kan kafirci amma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam bai manta ma sa wannan alheri da taimako da ya yi ma sa ba. Har a lokacin da ake takaddama a kan fursunonin mushrikai da aka kama a Badar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa ya yi, da ace Mut’im yana duniya idan ya neme su kyauta zan sakar ma sa su. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 4024.
Leave a Reply