Ci Gaban Yaduwar Musulunci
3. Musuluntar Dhimad Al-Azdi
Dhimad dan kasar Yemen ne, daga
fitacciyar kabilar nan ta Azd-Shanu’a
masu dogon tarihi. Mutum ne da
Allah ya yi ma sa baiwa ta yin rukiyya
ga masu fama da kamun iskoka. A
lokacin da ya ji wawayen Makka suna
tadin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam suna ce ma sa mahaukaci
ya dauka maganar arziki ce. Don
haka sai ya dauki alkawalin zuwa ya
yi ma sa tawada ko Allah zai sa a
dace a tunaninsa.
Haka kuwa ya dora ma kansa zuwa
wurin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya gabatar da kansa yana
cewa: “Ya Muhammad! Ni mutum ne
da nake tawada ga wadanda aka
jarabce su da kamun iskoka. Kuma
da yawa wadanda Allah ya ba su
lafiya a sanadiyyata. Ko kana da
bukata?” Sai manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya kimtsa domin ya
yi ma sa jawabi. Sai ya soma da
gabatarwar da yake yi wacce ta
kunshi godiya da yaba ma Allah a
kan cewa, duk wanda Allah ya shiryar
shi ne shiryayye, wanda kuma ya
batar babu mai juya shi zuwa ga
tafarkin shiriya. Sannan sai shaidar
gaskiya. Kamar dai yadda kuka ji
masu huduba suna fara hudubobinsu
“innal hamda lillah…”. Sannan sai ya
ce, amma ba’ad.
A nan ne Dhimad ya ce ma sa
dakata. Maimaita wannan kalamin
naka. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam bai musanta ma sa ba sai
ya sake maimaitawa. Suka yi haka
har sau uku. Dhimad ya ce, to ai ba
ka bukatar ka yi wani jawabi. Wannan
ma ya ishe ni. Wallahi ba irin
bokayen da ban gani ba da masu
siddabaru da mawaka. Ban taba jin
magana mai kama jiki ba irin wannan
taka. Kuma na yi amanna kai ba ko
daya ba ne a cikinsu. Ba ni hannunka
kawai in yi maka caffa a kan shiga
musulunci. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ce, to zaka karba
ma mutanenka? Ya ce, eh, har da
mutanena.
Akwai wata rana da ayarin mayakan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam suka shuda ta kan
mutanen Dhimad suka yada zango
wajensu. Da aka tashi wucewa sai
shugaban ayarin ya ce, akwai wanda
ya taba kayan wadannan mutane a
cikin ku? Sai wani mutum daya ya ce,
eh. Na dauki shantalinsu na kama
ruwa. Ya ce, to ka mayar ma su da
kayansu. Wadannan mutanen Dhimad
ne. Sahih Muslim, hadisi na 868
daga ruwayar Ibnu Abbas
Radhiyallahu Anhu.
Haka dai zamu ga duk wata
furofagandar da Quraishawa suka yi
don su bata sunan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ko su
dushe haskensa sai ta kara ingiza
masu hankali zuwa ga bincike da
gane gaskiya. Duba kuma irin
kyawon halin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam yadda wannan ya zo
ya ce zai yi ma sa rukiyya amma bai
nuna fushi ba sam ko damuwa. Ya
dai yi niyyar ya yi ma sa bayanin ko
shi waye. Amma cikin hikimar Allah
shimfidar bayanin nasa kawai sai ta
ishi wannan bawan Allah mai
wankakkiyar zuciya. Daga nan kuma
masu wa’azi da huduba ya kamata su
fahimci muhimmancin irin wannan
shimfida mai albarka da take bude
zukata masu tsarki, ta wanke masu
kazanta da daudar son zuciya da
sabon Allah. Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam bai yi nauyin baki ba
da wannan bawan Allah ya musulunta
sai ya ce ya isar da sakon musulunci
zuwa ga jama’arsa, kasancewarsa
mutum mai daraja da matsayi wanda
in ya fada ana saurarawa. Su kuma
sahabbai suna darajanta duk wanda
suka san yana da matsayi a wurin
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Don haka suka ce a kyale
mutanen Dhimad, kome nasu kar a
taba.
Mu kwana lafiya cikin amincin Allah
Leave a Reply