ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 64( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Manzon Allah Da Danginsa Sun
fuskanci Daurin Ta-la-la
Bayan da duk kokarin Quraishawa na
dakile addinin Allah ya ci tura.
Musulunci sai ci gaba da yaduwa
yake yi a birni da kauye. Ga kuma
musulmi sun hakurce duk irin
wahalhalun da ake ba su. Sannan
kuma ta fuskar hujja an kasa i ma su,
an kuma kasa sa su sassafta. Kawai
sai suka sake hawa kan teburin
shawara suka yi matsaya a kan cewa,
babu wata mafita sai dai a kashe
manzon Allah! Da labari ya kai ga
Abu Talib sai ya tara duk zuriyyar
Abdulmuttalib ya sanar da su abin da
ake ciki, kuma ya nemi su daura
damarar kariyar sa har in da karfinsu
ya kare. Musulmi da wanda ba
musulmi ba daga cikin danginsa suka
dauri aniyar yin haka. Musulmi sun yi
saboda Allah, kafirai kuma saboda
kishin dangantakarsu. Wannan sai ya
haifar da yankewar alaka tsakanin su
da sauran mutanen Makka.
Quraishawa suka rubuta taba’a suka
lika ta a jikin Ka’aba cewa, daga yau
ba aure da auratarwa, ba saye da
sayarwa, babu rahama babu tausayi
tsakanin su da Banu Abdilmuttalib
har sai sun mika Muhammad an
yanke ma sa hukuncin kisa! Tsarki ya
tabbatar ma Allah!
Wasa-wasa fitina ta fankama. Dangin
annabi da sahabbansa suka shiga
wani mawuyacin hali. Ba a magana
da su, ba a ciniki ko auratayya da su,
ba a bari wani tallafi ko taimako ya je
hannunsu. Idan aka kawo haja daga
kasashen waje kuma ba a bari su
shiga kasuwarta ballantana a saida
ma su. Duk a cikin haka kuma kullum
dare sai an sauya ma manzon Allah
wurin kwanciya fiye da sau daya don
jin tsoron a kawo ma sa farmaki.
Shekara uku cif wannan zalunci yana
gudana a kan su. Abincin da za su ci
ma sai da ya gagare su.
Ana haka, sai Allah cikin ikonsa ya
zo da mafita. Wani bawan Allah ana
ce da shi Hisham bn Amr daga gidan
Banu Hashim ya shirya juyin mulki
kan wannan zalunci. Nan take ya
nemi mutane masu hankali irin sa
daga kabilu daban daban. Ya gana da
su a asirce kuma suka amince su
biyar kan cewa za su yi tawaye ma
wannan zalama. Suka jagorantar da
Zuhairu bn Abi Umayya daga kabilar
su Abu Jahli “Banu Makhzum” wanda
kuma yake dan gwaggon manzon
Allah ne “Atika”. Sai da Zuhairu ya
dubi lokacin haduwar su gaba daya,
sai ya zo ya yi dawafi sannan ya yi
shela: “Ya ku jama’a! Wane irin
zalunci ne wannan? Muna ci, muna
sha, muna sa suturar da muke so
amma ‘yan uwanmu ‘yan gidan
Hashim suna halaka, yunwa tana son
ta ga baya gare su?!” Hankula kuwa
gaba daya sai suka karkata gare shi.
Sai ya ci gaba: “Wallahi ba zan zauna
a wurin nan ba sai an yaga wannan
takarda ta zalunci da keta alfarmar
zumunta”. Sai Abu Jahli ya yi fararat
ya ce, “karya kake yi wallahi. Ba a
yaga ta”. Zam’atu bn Al-Aswad ya
mike daga can wani bangaren
masallaci – daman haka aka shirya –
ya ce ma Abu Jahali, ai kai ne
makaryaci wallahi. Ko can farko da
aka rubuta ta mu ba mu amince ba.
Yana gama fadin haka sai Abul
Bukhturi ya tashi – shi ma yana cikin
kwamitin – ya ce, wallahi Zam’atu ka
yi gaskiya. Ba da ra’ayinmu aka
rubuta ta ba. Shi ma Mut’im bn adiy
ya tashi tsaye, sai Hisham shi ne ya
zo na karshe. Duk suka muzanta Abu
Jahli, suka karfafa a yaga wannan
muguwar takarda. Shi kuma Abu
Jahli bai samu ko mutum daya da ya
goyu bayan sa ba. Sai kawai cewa ya
yi: “wannan da gani ka san abu ne da
aka shirya. To, ba za mu yarda ba”.
Mut’im ya nufaci Ka’aba kawai ya
ballo wannan azzalumar takarda. Ko
da aka dauko ta duk gara ta cinye
kalaman zalunci da yanke zumunta
da ke cikin ta, amma ta bar wuraren
da sunan Allah ya ke. Allahu Akbar!
Ko wannan kadai ya ishe su wa’azi in
da akwai rabo. Amma ina! Mai rabon
shan duka…
A cikin wannan darasi akwai ababen
lura da dama. Sau da yawa Allah
yakan taimaki musulunci ta hannun
wanda ba musulmi ba idan ya ga
dama kamar yadda wadannan
mushrikai su biyar suka shirya
wannan tawaye har musulmi suka
samu sa’ida. Musulmi kuma suna iya
cin gajiyar aikin alheri ko ya fito daga
wurin kafiri. Shi kuma zalunci duk
lafiyayyen hankali yana kyamar sa.
Abin da duk ya fi wannan ban
sha’awa shi ne irin tarbiyyar
sahabban annabi da bin umurni da
suke yi da tsayawa kan doka. Kana
tsammanin a cikin su ba wanda zai
iya bin dare ya kashe shugaban
wawayen nan “Abu Jahali” duk a
huta? Ko dan karamin matashin cikin
su “Ali dan Abu Talib” da bai wuce
shekaru 15 ba a wancan lokaci yana
iya wannan. Ballantana akwai
jarumawa manya irin su Hamza da
Umar da sauran su. Me ya hana su yi
haka? Saboda ba a ba su umurni ba.
Irin wannan shawara da wani daga
cikin su ya yi gabansa ya yanke ta
zai yiwu ya samu nasarar gamawa –
cikin dare – da Abu Jahli ko ma duk
wani arne irin sa. To, amma kuma
me zai biyo bayan haka? Shi ya sa
aka ce mai hako ba ya ta da hannu.
Don haka, hakurin shi kadai ne
mafita. Kuma albarkacinsa duniya ta
tausaya ma su, ta tsani shugabannin
Makka saboda nuna halin rashin
imani da suka yi. Mutane da dama da
suke zuwa aikin Hajji suna yada
labarin a sauran garuruwa sai ana
cewa, lallai wannan addinin gaskiya
ne. In ba haka ba wa zai dauki
wahala kan sa har ya shiga wannan
hali! A daidai wannan lokacin ne
kabilun Gifara da Dausu da Azd-
Shanu’a – ta Yemen – da mutanen
Najran da Habasha suka yi ta shiga
musulunci. To, ina amfanin a ta da
fitina a wannan lokaci tun da babu
cikakken shirin tunkarar ta! Wanda
Allah ke wa fada ba ya fada.
Da yawan zaluncin da ake yi mutane
ba su amince da shi ba a cikin
zukatansu ba. Idan aka samu dalili
sai su yi fito-na-fito da shi. Don
haka ba a yanke hukunci a kan
mutane ga abin da ba su suka yi shi
ba.
Su kuma Banu Hashim da Banul
Muttalib albarkacin wannan hakuri
nasu Allah ya ba su kaso daga cikin
humusin ganimar yaki. Sabanin Banu
Abdishams da Banu Naufal. Duk
dangi daya ne amma ba su taimaki
annabi ba. Hadewa suka yi da kafirai.
Sai aka fitar da su daga cikin wannan
rabo. Duba Tafsir Al-Qur’an Al-Azim,
na Ibn Kathir a wurin ayar ganima ta
Suratul Anfal: 41 (2/312). A ranar
Khaibar wadannan gidajen biyu kadai
annabi ya raba ma wannan kaso na
ganima. Da aka tambaye shi sai ya
ce: “ba su taba rabuwa da mu ba a
zamanin Jahiliyyah ko na
musulunci”. Sunan Abi Dawud, hadisi
na 2980.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya kasance yana tuna
“Muhassab” wurin da mushrikai suka
hadu don cim ma wannan muguwar
matsaya. Kamar yadda ya ce a ranar
da zai isa lokacin Hajji, aka tambaye
shi, a wane gida za mu sauka gobe?
Sai ya ce, Akilu ya bar mana sauran
gidaje ne a Makka? Za mu dai sauka
a Muhassab, can in da Quraishawa
suka hadu a kan kafirci su da Banu
Kinanata. Sahih Al-Bukhari, hadisi na
3058.
Tura ta kai bango. Wane mataki ne
kuma musulmi za su dauka? Mu
hadu a darasi na gaba cikin yardar
Allah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 64( Dr. Mansur Sokoto)”
  1. Assalamu alaikm

Leave a Reply

Categories
Latest updates