GA WANI DAN LABARI MAI ……..
************************
Wani saurayi ne musulmi yake
soyayya da wata budurwa krista,
soyayyarsu tayi karfi sosai kowa daga
chikinsu yana tunanin bazai iya
rayuwa ba ba tareda dayanba.
Sai dai kash! Iyayen yarinyar sun
tsaya kai da kafa chewa bazasu aura
mata musulmi ba, haka shima
saurayin iyayensa suka ki yadda ya
auri krista.
Amma duk da haka basu hakura da
juna ba kuma kowanne daga chikinsu
yaki auran wani daban.
Sai saurayin wani lokachi ya kwanta
jinya har aka kwantar da shi a asibiti
amma wannan budurwar tashi krista
saboda soyayya tana ta yi masa
dawainiya da kai kawo.
Watarana saurayin jinya tayi tsanani
har yana kokarin chikawa lokachin
kuma budurwar bata nan sai wani
abokinsa.
Sai abokinnasa da yaga mutuwa zaiyi
saurayin sai yake kokarin bashi
kalmar shahada la’alla ko za’a dache
ya fada saboda yayi kyakkyawan
karshe na chikawa da kalmar
shahada.
Amma inaaa! Saurayin yaki karba
daga karshe ma chewa yayi shi fita
zaiyi daga musulunchi ya koma
kristaniti saboda ya samu daman
haduwa da budurwarsa a lahira. Wai
idan ya mutu yana musulmi
budurwarsa kuma krista, bazasu
hadu ba a lahira. Yana fadan wannan
maganar sai ya chika.
Chaaan kafin a fita dashi daga asibiti
sai budurwar ta dawo tana tambayan
abokin saurayinnata chewa ina yake
saurayin. Sai abokin yache mata ai
ya rasu. Amma bai fada mata abunda
ya faru ba kafin rasuwannashi.
Budurwar tayi ta kuka a asibiti dakyar
aka bata haquri ta daina.
Ita kuma daga karshe tache to
wallahi zata musulunta. Sai aka
Akache mata ai ba yanzu ya kamata
ki musulunta ba. Tun da ya kamata ki
musulunta saboda saurayinki ya
samu damar aurenki, amma yanzu da
ya mutu ai ko kin musulunta sai dai
dan kanki.
Sai tache ai ita bazata iya auran wani
ba tunda saurayinta ya mutu, saboda
haka zata musulunta tunda
saurayinta musulmine inyaso su
hadu a lahira, sai budurwa ta shiga
addinin musulunchi.
Kuma haka ta zauna tsawon
rayuwarta bata auri kowaba har itama
Allah yayi mata chikawa.
*************
FADAKARWA!
Samari da ‘yan mata masu soyayyar
wuche gona da iri sai a maida
hankali a dinga yi saboda Allah.
* Sau diyawa zakaji saurayi musulmi
ya koma krista kuma daga zaran ka
binchiki dalili sai kaga saboda wata
krista che da yake so.
* Wasu kuma a chikin musulunchin
ake basu sharadin sai in sun shiga
Shi’a za’a aura musu ko zasu daman
auran yarinyarda suke so.
***
Allah yasa mu dache.
Allah ya bamu ikon aikata komai
domin Shi.
Leave a Reply