Labarin Sheikh Ali Dan Muhammad
Al-Kadhibi – Wani malami dan kasar
Bahrain da Allah ya ganar da shi
gaskiya ya dawo daga rakiyar Shi’a.
GABATARWA
“Godiya ta tabbata ga Allah, godiya
mai yawa, mai tsarki, mai albarka
wadda ta cike sammai da qasa da duk
abin da Allah ya so bayan su. Tsira
da amincin Allah su tabbata ga
zababben bawansa, cikamakin
manzanninsa; annabi Muhammad da
iyalansa da sahabbansa da duk
wadanda suka bi su da kyautatawa
har rana ta qarshe. Bayan haka:
Na yi wannan dan rubutu ne don in
zayyana ma mai karatu wasu ‘yan
nazarce-nazarce da wasu ‘yan
tambayoyi da na yi ma kaina har suka
ja ni zuwa ga gaskiya wacce ban taba
tunanin – a can baya – zan iya
janyuwa zuwa gare ta ba.
Rikici ne ba na wasa ba, kuma aiki ne
ja; mutum ya bar abinda ya saba da
shi kuma ya gaje shi daga iyaye da
kakanni idan ya gane cewa gaskiya ita
ce sabaninsa. Ba ni kadai abin ya
shafa ba, da yawa wadanda suka
qarar da rayuwarsu a wajen kare wata
manufa ko tabbatar da wata aqida,
kwatsam! Sai Allah ya ganar da su
cewa ba a kan daidai suke ba. A nan
ne mutum zai yi ta fama da rikici a
tsakanin sa da zuciyarsa amma idan
ya daure sai Allah ya yi ma sa gamon
katar. A nan ne mutum zai gane cewa,
riqo da rubabbiyar aqida don kawai
son zama tare da ‘yan uwa da dangi
bai kamata ba. Idan mutum ya yi haka
to, ya yi cinikin duna wanda ba shi da
riba sai hasara. A maimakon haka
kamata ya yi mutum ya yi riqo da
gaskiya a lokacin da ta bayyana gare
shi.”
Baban Khalifi
Muhammad Al-Qadhibi
TUNA BAYA;
Tun da farko na tashi a gidanmu na
tarar da iyayena masu tsananin kula
da riqo da addinin Shi’a. Ban yi
wayon sanin mahaifina ba sai dai
kawuna wanda ya riqe ni tsakani da
Allah bayan mutuwar mahaifin nawa.
Kawuna yana cikin shehunai masu
rawani, kuma ya yi karatu a Hauza ta
yankin Jadd Hafs a qasar Bahrain,
bayan nan kuma ya samu qarin ilimi a
babban birnin Qum na qasar Iran.
Ba zan manta yadda kawuna yake kula
da mu yana ba mu tarbiyya ba, yana
hana mu cudanya da bata gari don
kada su gurnata mu. A ranar da ya ji
ina cewa zan karanci ilimin kida a
jami’a idan na gama makarantar
sakandare bata ransa ya yi, sannan ya
kira ni cikin lumana ya lurar da ni, ya
ce, ka ga ni, sa’ad da nake yaro irinka
ban samu mai dora ni a kan hanya ba.
Ya rinqa rarrashi na har ya canja min
ra’ayi. Wataqila da yanzu ni wani
shahararren makadi ne.
Mahaifiyata ita kuma ba ta da aiki sai
jiran lokutan bukukuwa wadanda ake
yi akai-akai don raya addinin Shi’a.
Tana bugun gaba da shiga a cikin su
tana ganin – ta haka – za ta samu
falalar hidimar sayyidi Husaini. Sau da
yawa takan je bukukuwan ko ba ta da
lafiya. In aka yi ma ta magana sai ta
ce, ai shiga wannan sha’ani shi ne
maganin ciwonta. Mahaifinta kuwa
sana’arsa ita ce yin ganguma da ake
kida da su a bukukuwan Ashura da
sauran bukukuwa da makokai da ake
yi a koda yaushe. Wani abin da mai
karatu zai so ya sani shi ne cewa,
dukkan mu muna bin tafarkin shehun
malami ayatullahi Al-Khu’i ne.
A lokacin quruciya babu abin da yake
ba ni sha’awa kamar in halarci
makokin Haji Abbas a unguwar
Hammam ta garin Manama. Idan
lokacin ya yi za ka gan ni tun da safe
na ridi tuta na shiga gaban jama’a.
Bayan da na girma kuma ina cikin
masu bugun bayansu da sarqoqi idan
ana wannan buki. A makaranta ma
babu abin da muke buqata kamar a
ce yau ranar makoki ce ko wani buki
daga cikin bukukuwan addini tun da
yake ta nan ne muke samu mu dan
shaqata. Ita kuma hukumar makaranta
tana qarfafa mu sosai a kan halarta. A
nan ne dalibai maza da mata suke
haduwa a yi ta rusa soyayya.
A gidanmu na tarar da ana yawan
alwashi. Misali, gwaggona da muke
tare da ita ta kasance tana yawan bari
(zubewar ciki). Don haka sai ta yi
alwashi ga Imam Ali cewa, idan Allah
ya ba ta Da kuma ya raya shi za ta
rinqa zuwa da shi wurin makokin
Ashura na kowace shekara yana
sanye da likkafani, kuma zai hau doki
ana shafa ma sa jinin ‘yan makoki da
yake fita daga jikinsu a sanadiyyar
dukan da suke yi ma kawunansu. Ana
haka kuwa sai Allah ya bai wa
gwoggona da namiji aka sa ma sa
suna Aqilu. Sun yi shekaru suna cika
wannan alwashi da shi har sai bayan
da ya girma ne ya qi amincewa da ci
gaba da yin haka. Ya ce ma su ya
bincika kuma ya gano yin alwashi ga
wanin Allah bai halalta, kuma idan an
yi ba dole ne a aiwatar ba. Ni ma dai
na samu wata matsala mai kama da ta
Aqilu. Domin kuwa lokacin da nake
yaro qarami na yi fama da ciwon
wuya wanda ya sa aka yi mani tiyata
ta farko ba ta yi ba, aka sake yin ta
biyu. Abin ya tayar ma mahaifiyata
hankali matuqa sai da ta je neman
shawara wurin shehi ya ce ma ta, ta
je ta yi alwashi a wata hubbare da ke
Manama cikin yankin As-Saqiyya. Ita
kuma kamar yadda duk ‘yan Shi’a
suka qudurta ta dauka cewa
qaburbura suna iya yin wani abu idan
an buqace su ta irin wannan hanya.
Wannan maganar sai da aka bijiro da
ita bayan na canja sheqa zuwa
tafarkin Sunna, suka ce wai na ci
amanar Ahlulbaiti tun da su ne suka
warkar da ni kuma ba domin su ba da
yanzu wai, ina cikin marigaya! Suka yi
ta yi ma ni barazana cewa idan ban
koma ma addinin Shi’a ba to duk abin
da ya same ni in kuka da kaina. Cikin
ikon Allah a yanzu wannan hubbaren
an rusa ta don an gano cewa babu
qabarin kowa a cikin ta, shirme ne
kawai irin na jahilai. Cigaba a darasi na biyu
Leave a Reply