SALO DA HANYOYIN DA MANZON ALLAH (S.A.W) YAKE BI WAJEN DA'AWA(Sheikh Dr. Muhammad Rabi'u Umar R/ lemo)

Wanda Ya Rubuta Kuma Ya Gabatar
Sheikh Dr. Muhammad Rabi’u Umar R/lemo
Gabatarwa
Yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta, Manzon Allah, da alayensa da sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsu zuwa ga ranar sakamako.
Bayan haka : Babu ko shakka kira zuwa ga addinin Allah yana xaya daga cikin manya-manyan wajiban addini, domin ta hanyarsa ne a gane qarya da gaskiya, shiriya da vata, daidai da ba daidai ba, don haka ma Allah Maxaukakin Sarki ya aiko da Manzanni da Annabawa don su koyar da mutane, su kira su zuwa ga addinin gaskiya. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa :
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? [??????: ??].
Ma’ana : “Haqiqa Mun aiko da Manzanninmu da hujjoji, kuma mun saukar musu da littattafai da mizani don mutane su tsaya a kan gaskiya” (Alhadid : 25). Don haka kiran mutane zuwa ga addini da karantar da su, da yi musu wa’azi aiki ne na Annabawan Allah da Manzanni.
Mahimmancin Da’awa A Musulunci
Aikin da’awa ba qaramin mahimmanci ne da shi ba a addinin musulunci, aiki ne mai gwaggwavan lada a wurin Allah Maxaukakin Sarki. Allah (S.W.T) yana cewa :
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ????: ??
Ma’ana : “Waye yafi kyakkyawan zance fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah, ya yi aiki nagari ya kuma ce ni ina cikin musulmi” (Fussilat : 33). A cikin wannan aya zamu ga Allah Mai girma da buwaya yana yabon masu da’awa da aiki nagari, da cewa babu wanda ya fi su kyan zance da magana.
Sheikh Abdul-Aziz bin Baz ? Allah ya yi masa rahama ? yana cewa :
“Ma’anar ayar ita ce, babu wanda ya fi shi (wato mai kira zuwa ga Allah) kyakkyawar magana, saboda ya yi kira zuwa ga Allah, ya yi nuni zuwa gare Shi, kuma ya yi aiki da abin da ya yi kira zuwa gare shi. Ma’ana ya yi kira zuwa ga gaskiya kuma ya yi aiki da ita, ya yi inkarin varna kuma ya tsoratar daga gare ta, kuma duk da haka bai ji kunya ba, ya bayyana abin da yake kai ya ce, “Ni ina cikin masulmi”().
A wani wurin Allah Maxaukakin Sarki yana cewa Annabinsa (S.A.W) :
? ? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ? [????: ???] Ma’ana : “Ka ce wannan shi ne tafarkina, ina kira zuwa ga Allah a kan hujja (basira) ni da duk wanda ya bi ni. Tsarki ya tabbata ga Allah, ba na cikin masu tarayya da Allah”. (Yusuf : 108).
A cikin wannan ayar zamu ga Allah Maxaukakin sarki yana bamu labarin cewa haryar Manzon Allah (S.A.W) da muminan da suka bi shi, ita ce kira zuwa ga Allah, kira zuwa ga kaxaita Allah (S.W.T) a cikin bauta, a bisa hujja da basira.
Haka kuma hadisi ya tabbata a cikin “Sahihu Muslm” daga Abu Hurairata Allah ya yarda da shi, ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
«???? ????? ????? ?????? ????? ???? ???? ???????? ?????? ??????? ???? ????????? ??? ???????? ?????? ???? ??????????? ???????. ?????? ????? ????? ????????? ????? ???????? ???? ???????? ?????? ?????? ???? ????????? ??? ???????? ?????? ???? ?????????? ???????» ???? ????.
Ma’ana : ((Duk wanda ya yi kira zuwa ga shiriya, to yana da lada kwatankwacin ladan waxanda suka bi shi, kuma hakan bai tauye musu komai daga cikin ladansu ba. Hakanan duk wanda ya yi kira zuwa ga vata, to yana zunubi kwatankwacin zunuban waxanda suka bi shi, kuma hakan bai tauye musu komai daga zunubansu ba”. Muslim ne ya rawaito shi.
Idan muka dubi wannan hadisi zamu ga cewa mai da’awa zuwa ga addini yana da ximbin lada, wanda Allah Maxaukakin Sarki ne kaxai ya san iya adadinsa, domin kuwa babu wanda ya san iya waxanda suke amfanuwa da da’awar mai da’awa sai Allah. A wani hadisin da Imam Muslim ya rawaito daga Abdullahi xan Mas’ud ? Allah ya qara masa yarda ? ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce :
((?? ?? ??? ??? ??? ??? ??? ?????)) ???? ????.
Ma’ana : ((Wanda ya yi nuni zuwa (aikin) alheri, to yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata (alherin). Muslim ne ya rawaito shi.
Lamarin da’awa bai tsaya nan ba, saboda ya tabbata a hadisi, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Aliyyu xan Abi Xalib ? Allah ya qara masa yarda – :
((??????????? ????? ???????? ??????? ???? ??????? ?????? ???? ???? ???? ??????? ???? ?????? ?????????)).
Ma’ana : “Wallahi, Allah ya shiryi mutum xaya da kai, ya fi a ce kana da jajayen dabbobi”. Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Saboda Mahimmancin wannan aiki na da’awa Manzon Allah (S.A.W) yake aika sahabbansa zuwa ga wasu garuruwa don kiran mutane da ilmantar da su, kamar yadda ya aiki Mu’azu xan Jabal da Aliyyu xan Abi Xalib zuwa Yemen, ya aika Mus’ab xan Umair zuwa ga Madinah kafin ya yi hijira, ya aika mutum saba’in daga sahabbansa zuwa ga wasu mutane don su karantar da su Alqur’ani da Sunnah, da dai sauransu, duk wannan yana nuna mana mahimmancin da’awa, kuma babu yadda za a yi al’umma ta rayu kyakkyawar rayuwa sai da masu da’awa zuwa ga gaskiya, zuwa ga ingantaccen addini, in kuwa aka rasa to wannan al’ummar ta lalace, don haka buqatar al’umma zuwa ga masu da’awa ta gaskiya, waxanda za su xora al’umma a kan addini ingantacce, tafi buqatar al’ummar zuwa ga abinci da abin sha, saboda qarshen wanda ya rasa abinci shi ne mutuwa, amma zai iya mutuwa ya shiga Aljannah, savanin wanda yake kan vata da shirka da kafirci qarshensa idan bai samu mai tsamo shi ba, shi ne halaka da tavewa duniya da lahira. Allah ya kiyaye mu.
Kashe-Kashen Waxanda Ake Wa Da’awa
Waxanda ake yi wa da’awa sun kasu gida-gida, kuma yana da matuqar mahimmanci ga mai da’awa ya sansu, don ya san ina ne yake fuskantar da da’awarsa, kuma wane salo ya kamata ya bi a wajen da’awar, saboda haka malamai sun kasa waxanda ake wa da’awa zuwa gida biyu, a kuma qarqashin kowanne kaso akwai wasu kashe-kashen, ga su kamar haka :
Kashi Na Farko : Musulmai, waxanda suka yi imani da Allah, suka amsa saqon da Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi. Waxannan su ne waxanda malamai suke ce musu “Ummatul Ijaba” sun kuma kasu zuwa gida uku :
• Waxanda suka yi gaba a cikin ayyukan alheri (Sabiquuna Bil Khairati). Su ne waxanda suke yin nafilfili a kan ayyukan wajibai da Allah ya xora musu.
• Waxanda suke tsaka-tsakiya (Muqtasiduuna). Su ne waxanda suka tsaya a kan wajibai.
• Waxanda suka zalunci kansu (Zalimiy Anfusihim) Su ne musulmai masu savo.
Waxannan su ne kashe-kashen na farko, Allah ya faxe su a cikin suratul Faxir aya ta 32. Wannan kaso ana yi musu da’awa ne zuwa ga tabbata a kan addinin da barin abin da ya sava masa.
Kashi Na Biyu : Kafirai Waxanda ba musulmai ba. Su kuma sun kasu da yawa, amma zamu iya haxe su a cikin waxannan kashe-kashen masu zuwa :
1. Masu inkarin samuwar Allah da ayyukansa (Malahidah).
2. Masu haxa Allah da wani wajen bauta (Al-Mushrikuuna).
3. Waxanda suka yi ridda suka bar addinin musulunci.
4. Ma’abota Littafi, kamar Yahudu da Nasara (Ahlul Kitab).
5. Munafikai, waxanda suka bayyana addini a baki, suka voye kafirci a zuci.
Waxannan sune kashe-kashen waxanda ba musulmi ba, kuma dukkaninsu suna buqatar da’awa. Don haka wajibi ne akan mai da’awa ya san salo da hanyar da zai fuskanci kowanne kaso daga cikin waxannan, domin salon da ya dace da mai inkarin samuwar Allah ba lallai ba ne ya dace da wanda yake ahlul kitabi kirista ko bayahude, kamar yadda salon da ya dace da musulmi mai savo ba lallai ba ne ya dace da kafiri ba, saboda haka yana da kyau mai da’awa ya san da su wa yake mu’amala, kuma ta yaya zai kira su.
Matakan Da’awa Duba Da Yanayin Waxanda Ake Wa Da’awar
Kasancewar waxanda ake wa da’awa sun kasu gida-gida to ya zama wajibi a samu matakai daban-daban wajen yin da’awar, don da’awar ta yi daidai da kowanne vangare.
Malamai sun dunqule matakan da’awa ? duba da waxanda ake wa da’awar ? zuwa gida uku, su ne : Hikima, kyakkyawan wa’azi, da kyakkyawar jayayya (Mujadala). Allah Maxaukakin Sarki ya faxi waxannan matakai a cikin faxinsa :
?? ? ? ? ? ? ?? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? [?????: ???].
Ma’ana : “Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da wa’azi kyakkyawa. Ka yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Haqiqa Ubangijinka shi ne masanin wanda ya vace daga tafarkinsa, kuma shi ne ya san shiryayyu”. (Annahal : 125).
Ibnul Qayyim ? Allah ya yi masa rahama ? yana cewa wajen fassara wannan ayar : “Sai Allah (S.W.T) ya ambaci matakan da’awa, ya sanya su kashi uku, gwargwadon halin waxanda ake wa da’awar, saboda kodai (wanda ake wa da’awar) ya kasance mai neman gaskiya ne, mai kwaxayinta, da son ta, da gabatar da ita akan abin da ba ita ba, to wannan za a yi masa da’awa da hikima ne, ba ya buqatar wa’azi ko jayayya. Ko kuma wanda ake wa da’awar ya kasance ya bijire ya shagala da abin da ba gaskiya ba, amma idan aka nuna masa gaskiyar zai gane ta, ya bi ta, ya fifita a kan waninta, to wannan yana buqatar hikima da wa’azi na tsoratarwa da kwaxaitarwa. Ko kuma ya kasance mai taurin kai da bijirewa, to wannan za a yi masa da’awa da jayayya mai kyau” (Duba Assawa’iqil Mursala : 4/1276 ? 1277).
A taqaice dai, idan muka dubi wannan aya zamu ga cewa duk wani matakin wa’azi da za a yi, ba zai fita daga xayan ukun nan ba.
Hanyoyin Kiran Kafirai Zuwa Musulunci
Duba da cewa mafi yawancin waxanda suke nan, masu wa’azin maguzawa ne, zamu xauki hanyoyin da ake bi wajen kiran waxanda ba musulmi ba (Kafirai) mu yi bayani a kansu.
Babbar hanyar farko wajen kiran kafirai zuwa ga musulunci ita ce hanyar da Alqur’ani ya bi, wadda take qunshe da hujjoji da dalilai gamsassu, waxanda sun isa su jawo duk wanda Allah ya yi masa gamon-katar zuwa ga rungumar addinin musulunci.
Idan muka dubi Alqur’ani zamu iya dunqule hanyoyin kiran kafirai zuwa ga addinin musulunci cikin hanyoyi masu zuwa :
1 ? Hanya Ta Farko : Bayanin kyan addinin musulunci, ta hanyar faxin kyawawan abubuwan da ya qunsa, na gaskiya, amana, haquri, girmama na gaba, tausaya wa na qasa, baiwa duk mai haqqi haqqinsa, da sauransu. A nan wajibi ne mai da’awa ya zama yana nuna waxannan halaye a aikace, fiye da faxi da baki.
2 ? Hanya Ta Biyu : Qoqarin warware musu abubuwan da aka faxa musu game da addini, wanda ba daidai ba, da hujjoji na nassi da hankali.
3 ? Hanya Ta Uku : Tunatar da su qarshen al’ummun da suka gabata, da irin yadda Allah ya halakar da su yayin da suka qi gaskiya.
Anan yana da kyau mai da’awa ya yi qoqarin haxa abubuwan da suke faruwa na musibu a yau da savawa Allah da ake yi, kamar abin da ya faru na Sunami, da gobarar daji da wasu qasashen Turai suke fama da ita, ko tsananin sanyi wanda ya mamaye su kwanakin baya, da makamantansu, duk waxannan abubuwa Allah yana aiko su ne don tsoratarwa da wa’azantawa, masu hankali da imani ne kaxai suke gane wa.
4 ? Hanya Ta Huxu : Amfani da kwaxaitarwa da tsoratarwa. Kwaxaitarwa ta hanyar ambaton abin da Allah ya tanada ga masu xa’a, tsoratarwa kuma da abin da Allah ya tanada ga yan wuta.
5 ? Hanya Ta Biyar : Nuna musu abubuwa marasa kyau da suke cikin addininsu, da tufka da warwarar da take ciki, ta hanyar bibiyar littattafan da suka yi imani da su, da fito da waxannan abubuwa.
6 ? Hanya Ta Shida : Tuna musu ni’imomin da Allah ya yi musu, da nuna musu dauwamar waxannan ni’imomi suna haxe da bin Allah da barin sava masa.
7 ? Hanya Ta Bakwai : Haxa kamamcecciniya (muqarana) tsakanin musulunci da sauran addinan, don fito da fifikon addinin musulunci a kan sauaran addinan.
8 ? Hanya Ta Takwas : Tattaunawa da su da ilimi da kyakkyawan bayani da hujjoji na nassi da hankali.
Waxannan sune mahimman hanyoyin da mai da’awar kafirai zuwa musulunci, zai yi amfani da su. Anan mai da’awa zai duba ne ya xauki hanyar da ta fi dacewa da irin mutanen da zai kira zuwa ga addini.
Abin da ya rage mana anan shi ne mu san salon da mai da’awa zai bi wajen amfani da waxannan hanyoyi.
Salon Da Manzon Allah (S.A.W) Yake Bi Wajen Da’awa
Anan zamu xauki salon da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen da’awa, ba tare da duban musulmi ne za a yi wa da’awar ko ba musulmi ba, saboda Manzon Allah (S.A.W) shi ne fiyayyen masu da’awa, kuma dukkan wani mai da’awa yana buqatar sanin salon Manzon Allah a cikin da’awa, a kowanne vangare. Daga cikin salon da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen da’awa akwai :
1 – Salon tausasawa da bi sannu-sannu : Wannan salo yana daga cikin manya-manyan salon da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen da’awa, kuma Allah Maxaukakin Sarki ya umarce shi da shi inda yake cewa :
?? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ?? ? ? ? ? ? [?? ?????: ??? ] ((Saboda rahama daga wajen Allah ka tausaya musu. Da ka kasance mai kaushin hali da tsaurin zuciya da sun watse daga wajenka. Ka yi musu afuwa ka nema musu gafara, ka yi shawara da su a cikin al’amari, idan ka yi azama ka dogara ga Allah, haqiqa Allah yana son masu tawakkali)) (Ali-Imran : 159).
Misalin wannan salo shi ne abin da ya faru a lokacin da balaraben qauye ya yi fitsari a masallaci, sahabbai suka yi masa tsawa, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da su, “ku qyale shi, kada ku yanke shi”.Da ya gama, sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni aka zuba guga xaya na ruwa a kan bawalin. Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi “Waxannan masallatai an gina su ne don sallah da ambaton Allah, basu dace da irin wannan qazanta ba”. Bukhari ne ya rawaito shi.
Hakanan yana daga cikin wannan salo, abin da ya faru lokacin da wani matashi ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W) ya nemi ya bashi izini ya yi zina!, sai sahabbai suka yi masa tsawa, sai Manzon Allah (S.A.W) ya hana su, sannan ya cewa wannan matashi, kana so a yi da babarka? Ya ce, “a’a” ya ce masa : kana so a yi da yar uwarka, yarka, gwaggwonka, duk yana cewa ‘a’a. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa “To haka ma mutane basa so a yi da iyayensu, ko yan uwansu ko ‘ya’yansu, ko gwaggwanninsu” daga nan Manzon Allah (S.A.W) ya xora hannunsa a kansa ya ce, “Allah ka tsarkake zuciyarsa, ka gafarta masa zunabansa, ka tsare masa farjinsa”. Imam Ahmad ne ya rawaito shi.
A cikin waxannan hadisai guda biyu, zamu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) yayi amfani da salon tausasawa, da bi a hankali wajen kiran wanda ya aikata wani savo ko yake yunqurin aikata.
2 ? Salon Sakin Fuska da fara’a : Yin amfani da wannan salo yana sa wanda ake wa da’awa ya saki jiki da mai da’awar, kamar yadda ya faru ga Mu’awiya bin Abil Hakam Assulamiy ? Allah ya qara masa yarda ? lokacin da ana sallah wani ya yi atishawa, sai ya ce masa “Yar ha mukal lahu” sai sahabbai suka yi ta kallonsa ? saboda ya yi wani abu, wanda bai kamata ya yi shi a cikin sallah ba ? da ya ga haka, sai ya ce, “me yasa me ku kuke ta kallona?” sai suka riqa dukan cinyoyinsu, suna nuna masa ya yi shiru, sai ya yi shiru. A lokacin da aka gama sallah, wannan sahabi ya ce, “Wallahi Manzon Allah (S.A.W) bai kyare ni ba, bai yi min tsawa ba, bai tsangwame ni ba, kawai dai ya ce min, “wannan sallah bai kamata a yi magana a cikinta ba”. Muslim ne ya rawaito shi.
A cikin wannan hadisi zamu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) ya sakar wa wannan sahabi fuska, bayan ya yi abin da yake ganin zai masa tsawa, zai kyare shi, amma sai Manzon Allah (S.A.W) bai masa haka ba, sai ya sakar masa fuska, sannan kuma ya karantar da shi cikin kwanciyar hankali. Sakamakon hakan ya sa wannan sahabi ya yi tambayoyi muhimman ga Annabi (S.A.W) dangane da masu zanen a qasa don sanin gaibu, da kuma abin da ya faru tsakaninsa da baiwarsa, har ya mare ta. Manzon Allah (S.A.W) ya ba shi amsa.
3 ? Salon Farawa da Muhimmi Sannan muhimmi : Fahimtar wanan salo yana da matuqar mahimmanci, saboda akwai abin da yake wajibi, sai a gabatar da shi a kan abin da yake ba wajibi ba. Manzon Allah (S.A.W) ya xora Mu’azu xan Jabal a kan wannan salo lokacin da ya aike shi Yemen, ya ce masa :
((?????????? ??????? ??? ??????????? ???????? ????????? ????? ??????? ???????? ??????? ?????????????? ????? ??????? ???? ?????? ?????????? ?????? ????????? ??? ?????????? ?????????????? ??????? ???????? ?????????????? ????? ??????? ?????? ?????????…)). ???? ????.
Ma’ana : ((Ya zama abu na farko da zaka kira su zuwa gare shi, shi ne bautawa Allah. Idan suka san Allah, ka faxa musu Allah ya wajabta musu salloli biyar a cikin yini da dare, idan suka yi haka, ka faxa musu Allah ya wajabta musu zakka?..)). Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
A wannan hadisi zamu ga farkon abin da Manzon Allah ya umarci Mu’azu ? Allah ya qara masa yarda ? da shi, shi ne kira zuwa ga Tauhidi , wato tsarkake Allah da bauta, da barin bauta wa waninsa, sannan sai Sallah, sai Zakkah. Don haka idan mai da’awa ya zo wajen waxanda ba musulmi ba, farkon abin da yake wajibi a kansa shi ne ya ga sun karvi kalmar shahada, sun yarda da bautawa Allah shi kaxai, ba tare da haxa shi da wani ba, daga nan sai sauran hukunce-hukunce su biyo baya.
A bisa wannan bayani ba daidai ba ne, mai wa’azi ya fara wa maguzawa maganar haramcin giya, ko wasu al’adunsu da suka taso a kai, don wannan yana iya sa su qin musuluncin.
4 ? Salon Kyauta Da Taimako : Ba da kyauta ga wanda ake wa da’awa salo ne mai mahimmanci wajen da’awa, wannan ya sa musulunci ya yi izini da cewa za a iya ba Mu’allafatu Qulubuhum zakka, waxanda wasu malamai suka ce su ne, waxanda ake fatan musuluntarsu, kuma a qarqashinsu akwai mabiya da yawa, wasu kuma suka ce, su ne masu raunin imani. Almuhim dai a cikin wannan umarni akwai nuna mahimmancin kyauta da bayarwa wajen da’awa. Kuma ya tabbata Manzon Allah (S.A.W) ya yi amfani da wannan salo a lokacin da aka dawo daga yaqin Hunain, ya bawa wasu daga cikin sahabbansa ganima, waxanda basu daxe da shiga musulunci ba, ya hana Al-ansar (Mutanen Madina).
An karvo daga Safwan ? Allah ya qara masa yarda ? ya ce, Manzon Allah (S.A.W) bai gushe ba, yana bani daga ganimar yaqin Hunain, alhali shi ne wanda na fi qi a cikin halitta, – ya yi ta bani ? har sai da ya zama babu wani abin da Allah ya halitta da na fi so, fiye da shi”. Muslim ne ya rawaito shi.
A wata riwayar da Imam Muslim ? Allah ya yi masa rahama ? Safwan ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya bashi dabbobi xari, sannan ya qara masa xari, ya sake qara masa xari”. Haka nan Manzon Allah (S.A.W) ya ba Ikramatu xan Abi Jahli, da Safwan xan Umayyah da Nudair xan Harisu, kowannensu dabba xari xari.
Wannan misali ne a kan amfani da wannan salo wajen da’awa, kuma duk wanda ya jarraba wannan salo zai tabbatar da mahimmancinsa da amfaninsa.
5 ? Salon Girmamawa : Girmama abokin magana ko wanda ake wa da’awa salo ne mai matuqar mahimmanci a babin da’awa, wannan salo ya fito fili a cikin wasiqun da Manzon Allah (S.A.W) ya aika wa sarakunan Rumawa da Farisawa, inda ya buxe wasiqar kowanne daga cikinsu da cewa, “Zuwa ga mai girma”. Don haka idan wanda za a yi wa da’awa shugaba ne a cikin mutanensa, to yana da kyau mai da’awa ya kiyaye wannan girman na shi, ya ba shi haqqinsa daidai gwargwado.
Haka nan idan muka duba qissar Thumama xan Uthal zamu ga wannan salo a fili. Thumama xan Uthal, shugaba ne a cikin mutanensa, amma sai sahabbai suka kamo shi a lokacin da Manzon Allah (S.A.W) ya aika su a cikin wata runduna zuwa Najd. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya sa aka xaure shi a jikin xaya daga cikin dirkokin masallaci. Da safe sai Manzon Allah (S.A.W) ya zo inda yake, ya ce masa, me zaka ce ya Sumama?. Sai ya ce wa Manzon Allah (S.A.W) : “In ka kashe ni, ka kashe ma’abocin jini(), in ka yi ni’ima (wato ka yi afuwa) to ka yi wa wanda yake mai godiya ni’ima, in kuwa dukiya kake so, to tambayi a baka”. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya tafi ya barshi, har sai washegari ya sake dawowa ya tambaye shi, ya sake bada irin waccan amsar, haka suka yi da Manzon Allah (S.A.W) har sau uku, a rana ta uku, Manzon Allah ya ce “a sake shi”. Da aka sake shi, sai ya tafi bayan masallaci ya yi wanka ya zo ya musulunta. (Duba Sahih Bukhari da Muslim don ganin wannan qissar).
Anan zamu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) ya yi mu’amala da wannan bawan Allah, ya lura da matsayinsa a cikin mutanensa, ya sake shi, wanda hakan ya zama sababin musuluntarsa.
Ibnu Hajar ? Allah ya yi masa rahama ? ya ce, “A cikin wannan hadisi akwai tausasawa ga wanda ake san ran musultarsa daga cikin ribatattun yaqi, idan har akwai maslaha ga musulunci a cikin hakan, musammam ma ga wanda adadi masu yawa za su bi shi a kan musuluncinsa”. (Fathul Bari 8/88).
6 ? Salon Aika Saqo : Wannan salo ana bin sa ne, don isar da saqo ga wanda baya kusa, ko kuma yake da girma da matsayin da mai da’awa ba zai iya isa gare shi ba. Manzon Allah ya yi amfani da wannan salo lokacin da ya aika wa sarakunan qasashe wasiqu, yana kiransu zuwa ga addinin musulunci. A qarqashin wannan salo akwai buqatar mai da’awa ya rubuta taqaitaccen bayani dangane da abin da yake da’awa zuwa gare shi, ya kuma yaxa shi cikin mutane.
7 ? Salon Tambayar da Amsarta A Fili Take : Alqur’ani da Sunnah cike suke da irin wannan salo, a tambayi wanda ake wa da’awa wani abu, wanda amsar shi zata jawo hankalinshi zuwa ga abin da ake so ya fahimta. Idan muka duba waxannan ayoyi zamu ga wannan salo a fili. Allah ya ce :
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ?? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?? ? ? ?? ? ? ? ? ?? (?????: ?? ? ??)
8 ? Salon Buga Misalai : Buga Misali da abubuwan da suke fili don wanda ake wa da’awa ya gane abin da ake kiran shi zuwa gare shi, salo ne da Manzon Allah (S.A.W) ya yi amfani da shi wajen da’awa, misalinsa :
An karvo daga Abu Hurairata ? Allah ya yarda da shi ? ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce :
«??????? ???????? ?????? ??????????? ?????? ???????? ????????? ??? ????????? ?????? ?????????? ???????? ??????????? ??????? ??? ???????? ???????? ?????? ???????? ????????????? ?????????????? ??????????????? ?????? ????? ?????????? ??????? ???????????? ????? ????? ???????????? ???? ???????? ??????? ???? ???????? ??????? ???? ???????? ?????????????? ???????????? ??????» ???? ????.
Ma’ana : ((Misalina, kamar misalin mutun ne, ya hura wuta, yayin da ta haska abin da yake gefenta, sai faxa-wuta da waxannan dabbobin da suke shiga wuta suka riqa faxa wa ciki, shi kuma mutumin yana kare su, su kuma suna fin qarfinsa suna faxa wa cikinta)) Manzon Allah ya ce, “Wannan shi ne misalina da misalinku, ni ina riqe ku daga faxa wa wuta, ku kuma kuna rinjayata kuna faxa wa cikinta”. Muslim ne ya rawaito shi.
A cikin wannan hadisi zamu ga Manzon Allah (S.A.W) ya yi amfani da buga misali ga Al’ummarsa, don su gane haxarin bijirewa umarninsa. Don haka yana da kyau mai da’awa ya riqa amfani da salon buga misalai don masu sauraran shi su gane abin da yake nufi.
Waxannan su ne wasu daga cikin salo-salon da Manzon Allah (S.A.W) yake bi wajen da’awa. Don haka akwai buqatar mai da’awa ya duba salon da ya dace da mutanensa ya yi amfani da shi. Allah Maxaukakin Sarki ya datar da mu.
Rufewa:
Wannan shi ne xan abin da Allah Maxaukakin Sarki ya bani ikon tattarawa, don haka inda na dace to daga Allah ne, ina qara roqonsa falalarsa da baiwarsa, in kuwa na yi kuskure to daga gare ni ne, da shaixan, kuma ina roqon Allah Maxaukakin Sarki ya yafe min, ya bani ikon gyarawa.

One response to “SALO DA HANYOYIN DA MANZON ALLAH (S.A.W) YAKE BI WAJEN DA'AWA(Sheikh Dr. Muhammad Rabi'u Umar R/ lemo)”
  1. ZAKARIYA YUSUF LIMAN Avatar
    ZAKARIYA YUSUF LIMAN

    Assalam alaikum ayuhal muslimun.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: