ALKAKI DA RUWAN ZUMA( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 35
Daga Cikin Fifikonsa
4. Darajar Sahabbansa (kashi na
daya)
Ba wani zamani da ya kai alherin na
manzon Allah. Ba wasu mutane da
suka kai alherin mutanensa, wadanda
suka ba da gaskiya gare shi, suka
taimake shi. Su ne abokan rayuwarsa,
abokan huldarsa, makwautansa,
surukansa, almajiransa, sojojinsa. Da
su ne ya yaki duniya har ya isar da
sakon Allah. Babu yadda za ka iya
raba rayuwar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam da ta sahabbansa.
Domin kuwa ba zai kasance liman ba
in ba don suna bayansa ba. Ba zai
zama kwamanda ba in ba don
sojojinsu suna kewaye da shi suna
yaki karkashin tutarsa ba. Ba zai
zama malami ba in ba don sun
gurfana suna daukar karatu a wurinsa
ba.
Idan akwai wani mahaluki wanda
zama da shi yake janyo kusanci zuwa
ga Allah. Idan akwai wani mahaluki
wanda hada hannu da shi yake sa a
samu matsayi a wurin Allah. Idan
akwai wani bawan Allah wanda
taimakonsa yake sa a samu yardar
Allah. To, babu shakka duk musulmi
sun sani wannan mutum shi ne dan
Amina fiyayyen halitta.
Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya sanar da
sahabbai cewa, kasancewarsu a
zamanin manzo ba al’amari ne na
wasa ba. Allah ya ce:
“Kuma ku sani a cikin ku akwai
manzon Allah. In da zai biye ma
ra’ayinku a cikin al’amurra da yawa
da zaku wahala. Amma Allah shi ne
ya soyar da imani a gare ku, kuma ya
kawatar da shi a cikin zukatanku,
kuma ya kyamatar da kafirci da
fasikanci da sabo zuwa gare ku.
Wadancan su ne shiryayyu. Falala ce
daga Allah (wadda ya yi ta a gare ku)
da ni’ima. Kuma Allah mai cikakken
sani ne, mai cikakkiyar gwaninta”
Suratul Hujurat: 7-8.
To, ka ji fa. Allah yana ba da shedu a
kan su kamar haka:
1. Zama da suka yi da manzon Allah
babbar daraja ce da babu irin ta.
2. Sahabbai masu zanzarin neman
bautar Allah ne har sai annabi ya
taka ma su birki don gudun wahala
ta cim ma su.
3. Allah ya sanya ma su son imani
kuma ya kawata shi a zukatansu,
babu abin da suke sha’awa kamar
sa. Don haka ne ma suke sadaukar
da kome nasu a kan sa.
4. Sahabbai ba sa son kafirci da
fasikanci da sabo. Suna gudun su iya
kokarinsu.
5. Wannan kuma aikin Allah ne da ya
zabe su don sahibtar manzonsa sai
ya sa suka zamo haka. Kuma wata
falala ce da ni’ima daga wurin sa.
6. Allah cikin cikakken saninsa da
gwanintarsa ne ya yi haka. Don haka,
da ya san za su canja ko ba su
cancanta ba tun farko ba zai zabe su
ba. Ya kuwa za ayi mutanen da tun
ba a halicce su ba Allah ya ba da
bushara da su a cikin At-Taura da
Linjila, sannan za su canja addini ko
su lalace bayan shiriyarsu?! Duba
Suratu Muhammad: 29 ka ga
busharar da muka fada ma ka.
Duk wanda zai zo bayan sahabbai sai
dai ya riski wata falala amma su kam
sun kwashe kashin farko. Tun da ba
zaka iya taimakon annabi da
kariyarsa da yin hijira zuwa gare shi
da mika ma sa sadakarka hannu da
hannu ba. Ballantana ace ka nemi
shawararsa ko ka yi fatawa a wurin
sa ko kuma ya nemi shawara gare ka,
ko ka auri ‘yarsa ko ka aura ma sa
taka. Kai, ko ma ya shedi daurin
aurenka ko ya yi addu’a a gare ka ko
ya halarci jana’izarka. Wannan duk
yana cikin rabon da sahabbai sun
riga sun yi gaba da shi. Ya za ayi ka
cim ma mutanen da fatawoyinsu da
amsoshin da Allah ya ba su suna
cikin Kur’ani? Duba misali a Suratul
Baqarah kawai: 189, 215, 217, 219,
220 da 222. Kuma wadanda suka yi
yaki sahu daya da mala’iku, a
karkashin jagorancin fiyayyen halitta?
Duba Suratu Ali Imran: 124-126 da
Suratul Anfal: 12. Kuma wadanda
Allah ya ce ma annabinsa ya yi
shawara da su? Suratu Ali Imran:
159.
Shi ya sa Allah Tabaraka Wa Ta’ala
ya kasa musulmi kashi uku; muhajirai
da ansarai da wadanda suka bi su da
kyakkyawar addu’a. Suratul Hashr:
8-10.
Ashe kenan ba shi cikin musulmi
wanda ke bin dugadugansu don ya
fito da laifinsu ko kuskurensu.
Darajarsu ta kai su keta doka – bisa
halayyar ‘yan adam ta kasawa –
amma a cikin lumana da rarrashi
ubangijinmu ya ba da shelar ya yafe
ma su. Kamar abin da ya faru a Uhud
da baraden musulunci suka kasa jure
wahalar da ta keyawa su bayan
nasara ta juya zuwa gefen abokan
gaba. Suka kuwa rinka zurawa da
gudu a cikin firgici da tashin hankali.
Wannan zunubin kuwa – gudu a
fagen jihadi – babbar kaba’ira ce da
Allah ya yi kyaci mai tsanani a kan
ta. Kuma ya ce, duk wanda ya yi haka
zai gamu da fushin Allah, ya dandani
kunar wutar jahannama. Suratul
Anfal: 16-17. To, amma su da yake
‘yan gata ne, dubi abinda Allah ya ce
mu su:
“Hakika wadannan da suka juya
(suka gudu) daga cikin ku a ranar da
rundunoni biyu suka hadu (Ranar
Uhud) shaidan ne ya ribace su da
sashen abinda suka yi na zunubi,
kuma HAKIKA, WALLAHI Allah ya yafe
ma su. Hakika Allah mai yawan
gafara ne, mai yawan hakuri” Suratu
Ali Imran: 155.
A daya ayar kuma ya ce:
“Sannan sai Allah ya juyar da ku
daga gare su domin ya jarabce ku.
Kuma HAKIKA, WALLAHI Allah ya yafe
ma ku. Hakika, Allah mai baiwa ne a
kan mummunai”. Suratu Ali Imran:
152.
Duk da wannan laifin nasu ga shi dai
Allah yana kiran su mummunai kuma
yana shelanta ya yafe ma su har da
rantsuwa da karfafawa.
Ku biyo mu don ci gaba da jin
matsayinsu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates