ALKAKI DA RUWAN ZUMA32( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 32
Daga Cikin Fifikonsa
2. Albarkacin Sawunsa (kashi na 2)
9. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yakan shafi maras lafiya ya
yi ma sa addu’a sai ya samu waraka
nan take. Misali, a wani lokaci da
Jabir bn Abdillah ya yi rashin lafiyar
da ta tsananta har ta gusar da
hankalinsa manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya ziyarce shi tare
da sayyidi Abubakar (R), sai manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya
sa aka kawo ma sa ruwa ya yi alwala
sannan ya zuba ma sa saura. Take
sai Jabir ya farka. Ya ce, ya manzon
Allah! Me kake umurni na yi a game
da dukiyata? Sai Allah ya saukar da
ayoyin gado da ke cikin Suratun
Nisa’i: 11-14. Duba Sahih Al-
Bukhari, hadisi na 194 da kuma na
4577.
10. Haka kuma a lokacin Fathu
Khaibar, manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya yi tofi a idon
sayyidi Ali (R) take idonsa suka
warke bayan da farko bai ko iya
fitowa yakin ba saboda ciwon da
suke yi ma sa. Sahih Al-Bukhari,
hadisi na 2847.
11. Wanda ya fi wannan ma shi ne
idon Qatadah bin Nu’uman da ta
darare har ana son a cire ta. Amma
da Sallallahu Alaihi Wasallam ya sa
hannunsa ya mayar da ita kuma ya yi
ma sa tofi a kai nan take sai ta warke
har ta fi dayar karfin gani da lafiya.
Dala’il An-Nubuwwa na Imam Baihaqi
(3/251-253).
12. Ya isa abin farin ciki ga duk wani
sahabi ya samu tufan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam don ya yi
amfani da shi wajen neman waraka
daga wurin Allah. Sayyida Asma’u
‘yar Abubakar Siddiqu (RA) ta taba
fito da wata rigar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam da ta
samu daga wajen kanwarta A’isha
suka rinka wanke ta ana shayar da
ruwan ga marasa lafiya. Sahih
Muslim, hadisi na 5310.
13. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ba kawai ya yi kawaici a
kan neman tubarraki da sawunsa da
sahabbai ke yi ba, a’a, ya ma karfafa
su a kan haka. Misali, a lokacin da ya
kammala hajjinsa na bankwana, an yi
ma sa aski sannan sai ya bayar da
gashin kansa aka raba ma mutane.
Sannan ya yanke kumba ita ma ya sa
aka raba ma mutane. Al-Musnad na
Imam Ahmad, hadisi na 16521, kuma
Sheikh Shu’aib Arna’ut ya inganta
shi.
14. A wuraren yaki da makamantansu
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yakan karfafa ma sahabbai
neman albarkacinsa ko don makiya
su samu ru’uba a cikin zukatansu ta
hanyar ganin matsayinsa a wurin
musulmi. A Hudaibiya, lokacin da
mushrikai suka hana musulmi shiga
Makka, jekadan Quraishawa Urwa bn
Mas’ud ya ga abin mamaki da ya zo
taron sasantawa tsakanin su da
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Ba wata majina da
manzon Allah zai yi kaki face
sahabbai sun yi wuf sun sharbe ta
sun goge ta ga jikinsu. Idan ya
umurce su da wani abu za su yi
gaggawa su aikata shi. Idan sun yi
magana a gabansa su kan sassauta
murya, kuma ba su daga kai su kalle
shi saboda girmamawa. Ga abin da
Urwa ya ce ma Quraishawa da ya
koma a wajen su:
« ﺃﻱ ﻗﻮﻡ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻟﻘﺪ ﻭﻓﺪﺕ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ، ﻭﻭﻓﺪﺕ
ﻋﻠﻰ ﻗﻴﺼﺮ ﻭﻛﺴﺮﻯ ﻭﺍﻟﻨﺠﺎﺷﻲ، ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺭﺃﻳﺖ
ﻣﻠﻴﻜﺎ ﻗﻂ ﻳﻌﻈﻤﻪ ﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﻣﺎ ﻳﻌﻈﻢ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﻣﺤﻤﺪ –
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ – ﻣﺤﻤﺪﺍ …».
“Ya ku jama’a! Wallahi na je wajen
sarakuna. Na ziyarci sarkin Ruma da
na Farisa da na Habasha. Wallahi ban
taba ganin sarkin da jama’arsa ke
girmama shi irin girmamawar da
mutanen Muhammadu suke yi ma sa
ba”. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 2732
da 2731.
15. A lokacin da Salmanul Farisi ya
shirya biyan maigidansa gindi 300 na
dabino wadanda zai dasa su don ya
fanshi kansa daga kangin bauta, ba
abin da ya cece shi sai sanya albarka
da manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi ga wannan aiki.
Musnad Ahmad, hadisi na 23788.
Kuma Sheikh Al-Arna’ut ya kyautata
shi.
Wannan fa shi ne manzon Allah
kamar yadda sahabbansa suka
fahimce shi. Haka kuma almajiransu
na farko da na karshe mabiya Sunnah
suka kudure girmansa a cikin
zukatansu. Kuma suka rubuta a cikin
littafansu. Wannan ne kuma suke
karantar da almajiransu. Akwai abin
da madaukakin sarki ya gani ya batar
da wadannan ababe daga al’ummar
musulmi bayan can a da ana samun
su jefi-jefi. A shekarar 656H ne da
Tattar suka kona birnin Baghdad tare
da hadin guiwar ‘yan Shi’a,
shugabansu Holaku ya fito da sanda
da rigar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya kona su, ya
warwatse tokarsu kamar yadda Imam
Suyuti ya fada a cikin “Tarikh Al-
Khulafa’” da Baghdadi cikin “Khizanat
Al-Adab” da Qirmani a cikin “Tarikh
Ad-Duwal” da sauransu. A yau akwai
wasu kwayoyin gashi da ake jingina
su ga manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam a Istanbul ta kasar
Turkiyya amma malaman tarihi ba su
tabbatar da sahihancinsu ba. Muna
gurin a yau da za a samu tabbacin
kwayar gashi guda daya ta manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
wallahi da sai mun neme ta mun jika
ta a ruwa mu sha, mu nemi
albarkarsa. Amma fa ba mu ajiye
kowa a irin wannan matsayin in ba
shi “Sayyidul Wara” ba Sallallahu
Alaihi Wasallam. Domin ba a kiyasta
kowa a kan sa. Ba ka ganin duk
Khulafa’u guda hudu ba su kai kan
su a wannan matsayi ba? Ina! Ko
alama. Babu wanda ya ce sun yi
kafada da kafada da fiyayyen halitta a
cikin tsaransu ko mabiyansu ko
almajiransu. Don haka, ba ka samun
ingantattar ruwaya guda daya da ta
nuna sun nemi albarkacin rigar
dayansu ko shantalinsa ko
takalminsa.
Daga nan ne duk wani zargi ko zagi
da ake ma malaman Sunnah yake
samun asali ta bangaren wadanda
suke kai wasu a matsayin shugaban
halitta, suna ba su matsayin
jagoranci da jingina kansu zuwa gare
su. Suna neman tubarraki daga
sawunsu, suna neman biyan bukatu
daga wurin kaburburansu. Dalili na
biyu kuma shi ne kin bin umurnin
shugaban halitta da wasu ke yi sai su
saba ma Ahlus Sunnah. A wurin
mabiya Sunnah babu wanda ya isa ya
tsallake umurnin manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam bisa ga
kowane irin dalili. Kuma babu wanda
ya isa ya haifar da wani abu na
bautar Allah ko neman kusanci zuwa
ga Allah sai shi kadai ma’aikin Allah.
Don haka, ba su kirkira kome a cikin
addini na buki ko murna ko bakin ciki
ko zikiri ko ibada kowace iri. Sun
tsaya ga annabi Muhammadu ba su
tsallake shi ba. Shi kadai ne
limaminsu, kowa ma sai dai ya zama
ladan mai jiyarwa. Shi ya sa ba su
jinginuwa ga kome sai sunnarsa. Ai
daman kuma shugaban halitta cewa
ya yi: “Duk wanda ya aikata wani aiki
ba bisa umurninmu ba, an mayar ma
sa da aikinsa”. Ma’ana ba zai samu
lada daga ubangiji a kai ba. Duba
Sahih Al-Bukhari, hadisi na 2499 da
Sahih Muslim, hadisi na 3242 da
3243.
Ya Allah! Ka raya mu a kan tafarkin
manzonka, ka karbi rayukanmu a kan
sa, ka tashe mu a karkashin tutarsa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates