ALKAKI DA RUWAN ZUMA33( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 33
3. Matsayin iyalansa (kashi na daya)
Iyalan kowane mutum su ne
adireshinsa. Ma-so-uwa kuwa dole
ne ya so danta. Ko a lahira mutane
na samun karin daraja a cikin aljanna
idan suna cikin iyalan mutumin kirki.
Suratut Tur: 21. To, ina ga iyalan
fiyayyen halitta?
Idan muna maganar matsayi da
darajojin iyalan manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam za mu
kasa su kashi biyu ne:
1. Darajojin da suka shafi duk
membobin wannan babban gida.
2. Sai kuma darajojin da suka
kebanci wasu daidaiku daga cikin su.
Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya kira
iyalan gidan annabawa da sa albarka
a gare su. Kamar yadda ya kira iyalan
annabi Nuhu (Suratul Anbiya’: 76) da
na annabi Ibrahim (Suratu Hud: 73
da Dhariyat: 26) da na annabi Musa
(Suratun Naml: 7 da Suratu Taha: 10
da Suratul Qasas: 29) da na annabi
Isma’il (Suratu Maryam: 55) da na
annabi Lut (Suartul A’raf: 83 da
Suratus Shu’ara’: 170) da na annabi
Ya’qub (Suratu Yusuf: 62) da
sauransu.
Iyalan annabinmu Sallallahu Alaihi
Wasallam ba a bar su a baya ba.
Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya kira su a
cikin Suratul Ahzab: 33 a tsakiyar
magana a kan wasu membobi masu
alfarma a wannan gida su ne matan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam. Allah ya ware ayoyi 7 a
cikin wannan sura don magana a kan
su. A cikin su ne madaukakin sarki
yake cewa:
(( ﻳﺎ ﻧﺴﺎﺀ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻟﺴﺘﻦ ﻛﺄﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺇﻥ ﺍﺗﻘﻴﺘﻦ،
ﻓﻼ ﺗﺨﻀﻌﻦ ﺑﺎﻟﻘﻮﻝ ﻓﻴﻄﻤﻊ ﺍﻟﺬﻱ ﻓﻲ ﻗﻠﺒﻪ ﻣﺮﺽ
ﻭﻗﻠﻦ ﻗﻮﻻ ﻣﻌﺮﻭﻓﺎ * ﻭﻗﺮﻥ ﻓﻲ ﺑﻴﻮﺗﻜﻦ ﻭﻻ ﺗﺒﺮﺟﻦ
ﺗﺒﺮﺝ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ ﺍﻷﻭﻟﻰ، ﻭﺃﻗﻤﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺁﺗﻴﻦ ﺍﻟﺰﻛﺎﺓ
ﻭﺃﻃﻌﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺇﻧﻤﺎ ﻳﺮﻳﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻴﺬﻫﺐ ﻋﻨﻜﻢ
ﺍﻟﺮﺟﺲ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﻴﺖ ﻭﻳﻄﻬﺮﻛﻢ ﺗﻄﻬﻴﺮﺍ * ﻭﺍﺫﻛﺮﻥ ﻣﺎ
ﻳﺘﻠﻰ ﻓﻲ ﺑﻴﻮﺗﻜﻦ ﻣﻦ ﺁﻳﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ، ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻛﺎﻥ ﻟﻄﻴﻔﺎ ﺧﺒﻴﺮﺍ *))
Wadannan ayoyi sun nuna yadda
madaukakin sarki yake son tsarki ga
iyalan annabinsa gaba daya. A nan
gaba za mu yi maganar su wane ne
iyalan nasa?
Akwai darajoji da suka kebanci wasu
daga cikin iyalansa ban da wadancan
darajoji nasu na tarayya. Za mu ba da
misalai daya daya kawai saboda
takaitawa.
1. Sayyidi Abbas baffan manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam dan
uwan mahaifinsa kuma tsaransa (An
haifi Abbas shekaru biyu kafin
manzon Allah). Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya
kasance tare da kusancin shekarunsu
yana darajanta shi a matsayinsa na
kanen mahaifinsa wanda ya
musulunta kuma ya taimaka ma sa. A
kan sa ne ma manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam yake
cewa: “Ashe ba ku san baffan mutum
irin babansa ne ba?” Sahih Muslim,
hadisi na 983. Ma’ana, yadda za ku
darajanta mahaifina da Allah ya
kaddari rayuwar sa zuwa yau, haka
ya kamata ku darajanta ma ni baffana
wanda yake dan uwansa.
2. Sayyidi Ali dan Abu Talib. Kanen
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ta zumunta. Mahaifinsa shi
ne wan mahaifin manzon Allah. Kuma
wanda ya kula da shi cikakkiyar
kulawa a lokacin da ya rasa kakansa
da mahaifiyarsa. Darajojinsa suna da
yawa. Cikin su har da fadin manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
cewa, ba mai son sa sai mumini,
kuma ba mai kin sa sai munafuki.
Sahih Muslim, hadisi na 113.
3. Matan manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam: Ya ishe su daraja
cewa, Allah ya ce su iyayen
mummunai ne. Suratul Ahzab: 6.
Kuma ba musulmin da ke shakka
cewa, su matayensa ne a duniya da
lahira. A kan haka ne ma Allah
Tabaraka Wa Ta’ala ya hana a aure
su bayan sa. Suratul Ahzab: 53.
4. Nana Fatima: ‘Yar autan ‘ya’yan
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam mata. Daga cikin falalarta
akwai cewar manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam: “Fatima tsoka ce
daga jikina. Abin da ya dame ta ya
dame ni”. A wata ruwaya: “Duk
wanda ya fusata ta ya fusata ni”.
Sahih Al-Bukhari, hadisi na 3437 da
3483 da Sahih Muslim hadisi na
4482. Duk da kasancewar sauran
‘ya’yan manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam duk suna shiga a cikin
wannan magana amma furta sunanta
a nan, da kasancewar maganar an yi
ta ne saboda ita yana ba ta karin
matsayi da daraja.
5. Hasan da Husain: Jikokin manzon
Allah kuma ‘ya’yan Fatima. Daga cikin
falalarsu akwai fadar manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam: “Al-Hasan
da Al-Husain su ne farin cikina na
duniya”. Sahih Al-Bukhari, hadisi na
3470 da na 5535.
6. Abdullahi dan Abbas: Kanen
manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ta wajen baffansa Abbas.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya yi ma sa addu’a a kan
Allah ya ilmantar da shi addini, ya
sanar da shi fassarar Qur’ani. Sahih
Al-Bukhari, hadisi na 75. Duba kuma
tafsirin Ibn kathir (1/115). Babu
shakka kuwa wannan addu’a Allah ya
karbe ta. Domin kuwa Ibnu Abbas
yaro ne karami da kalilan ne ilmin da
ya dauka daga manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam, amma ya
bibiyi magabatan sahabbai yana
darajanta su, yana daukar karatu a
wurin su har Allah ya kai shi
matsayin da ya fice na kowa a bayan
rasuwar su. Dubi abin da Imam As-
Sha’abi yake cewa: “An yi jana’izar
mahaifiyar Zaid bn Thabit (RA). Da
aka kare sai aka janyo ma sa
alfadararsa zai hau. Sai Ibn Abbas ya
zo ya rika ma sa linzaminta. Sai
Zaidu ya ce, haba dan baffan manzon
Allah! Ka saki kawai. Sai Ibn Abbas
ya ce, ai haka aka ce mu yi wa
malamanmu. Shi kuma Zaid sai ya
sauko ya sumbaci hannun Ibn Abbas
ya ce, mu kuma haka aka ce mu yi
ma iyalan annabinmu. Duba: At-
Tabaqat Al-Kubra na Ibn Sa’ad
(2/370) da Siyar A’lam An-Nubala’
na Dhahabi (2/437). Kuma shaihun
malami Ibnu Hajar ya karfafa isnadin
wannan labari a cikin Fathul Bari
(11/57). Wannan na nuna karara irin
mutunta juna da ke tsakanin iyalan
annabi da sahabbansa. Sabanin
tatsuniyoyin da ‘yan Shi’ah suka kitsa
kuma wasu littafan tarihi na ruwaya
suka dauko. Masu raunin imani da
karancin sanin wadannan bayin Allah
daga littafi mai albarka; Alkur’ani sai
suke gina akidunsu a kan irin
wadannan ruwayoyi. In da za su
koma ga Alkur’ani abin da ya fadi a
kan su kawai ya ishe su. Mutanen da
Allah ya ce, masu jinkan junan su ne,
ina zaka gaskata mai ce ma suna
gaba?!
Za mu dakata a haka. Amma za mu
dora in Allah ya so.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories