ALKAKI DA RUWAN ZUMA29( Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da
Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Fitowa Ta 29
Wane Annabi ne ya fi?
Allah madaukakin sarki ya bayyana
mana darajar annabawa a matsayin su
na fiyayyu kuma zababbu a cikin
bayinsa. Sa’annan kuma ya bayyana
ma na fifikon manzanni a kan
annabawa wadanda adadinsu yana da
yawan gaske kuma Allah ne kadai ya
san yawan nasu. Majmu’ Fatawa Ibn
Baz 2/66-67. Sai kuma fifikon Ulul
Azmi guda 5 a kan sauran manzanni.
Su ne: Nuhu da Ibrahim da Musa da
Isa da cikamakinsu Muhammad
Sallallahu Alaihi Wasallam amincin
Allah ya tabbata a kan su gaba daya.
(Suratul Baqara: 253 da kuma Suratul
Isra’i: 55 da Suratul Ahzab: 7, 40).
Babu shakka cewa, manzon Allah na
karshe Muhammad Sallallahu Alaihi
Wasallam yana da karin matsayi da
fifiko da yawan daraja da falala a kan
su gaba daya. Wannan kuwa abu ne
da ya fi karfin a bukaci kafa ma sa
dalili. Amma dai za mu ba da ‘yan
misalai gwargwadon yadda wanda bai
sani ba zai sani, wanda kuwa ya sani
zai kara tabbatarwa:
1. Duk lokacin da Allah zai yi maganar
annabawa da sunansa yake farawa.
Wannan shi ne abin da sarkin
musulmi Umar dan Haddabi
Radhiyallahu Anhu ya fadi a lokacin
wafatin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam in da ya gurfana a
wakwancinsa ya ce, kaicona! Na
fanshe ka da uwata da ubana ya
manzon Allah. Kai ne wanda
matsayinsa ya kai cewa, ka zo a
karshe amma a kullum idan Allah zai
fadi yan uwanka annabawa da kai yake
farawa. Yana nuni da wurare kamar in
da buwayayyen sarki yake cewa:
(( ﻭﺇﺫ ﺃﺧﺬﻧﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﻴﺜﺎﻗﻬﻢ، ﻭﻣﻨﻚ ﻭﻣﻦ ﻧﻮﺡ
ﻭﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻣﻮﺳﻰ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ( ( ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : ٧
Ka ga dai a wannan ayar duk “ulul
azmi” ne; mafifitan annabawa aka
kawo. Amma sai da Allah ya fara da
shi tukuna.
2. Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya
bayyana cewa, duk annabawa sai da
Allah ya sanya su suka sa hannu ga
wani alkawali; shi ne gaskata annabi
Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam
da taimakon sa idan ya riske su.
Kuma sannan Allah da kansa ya
rubuta shedarsa a kan wannan
alkawali da ya yi da su. Duba Suratu
Ali Imran: 81 in da Allah ya ce:
(( ﻭﺇﺫ ﺃﺧﺬ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻴﺜﺎﻕ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻟﻤﺎ ﺁﺗﻴﺘﻜﻢ ﻣﻦ ﻛﺘﺎﺏ
ﻭﺣﻜﻤﺔ ﺛﻢ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﺭﺳﻮﻝ ﻣﺼﺪﻕ ﻟﻤﺎ ﻣﻌﻜﻢ ﻟﺘﺆﻣﻨﻦ
ﺑﻪ ﻭﻟﺘﻨﺼﺮﻧﻪ، ﻗﺎﻝ ﺃﺃﻗﺮﺭﺗﻢ ﻭﺃﺧﺬﺗﻢ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻜﻢ
ﺇﺻﺮﻱ؟ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﺃﻗﺮﺭﻧﺎ، ﻗﺎﻝ ﻓﺎﺷﻬﺪﻭﺍ ﻭﺃﻧﺎ ﻣﻌﻜﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﺸﺎﻫﺪﻳﻦ( ( ﺳﻮﺭﺓ ﺁﻝ ﻋﻤﺮﻥ : ٨١
3. A cikin Alkur’ani ba wani annabin
da Allah ya shaya fadin sunansa in ba
shi ba. Duk Allah ya kira su baro baro.
Kamar yadda ya ce:
(( ﻗﻴﻞ ﻳﺎ ﻧﻮﺡ ﺍﻫﺒﻂ ﺑﺴﻼﻡ ﻣﻨﺎ ..))
“Sai aka ce ya kai Nuhu..” Suratu Hud:
48
(( ﻭﻧﺎﺩﻳﻨﺎﻩ ﺃﻥ ﻳﺎ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ))
“Muka kira shi ya Ibrahim!..” Suratus
Saffat: 104
(( ﻭﺇﺫ ﻧﺎﺩﻯ ﺭﺑﻚ ﻣﻮﺳﻰ ))
“Ka tuna lokacin da ubangijinka ya
kira Musa..” Suratus Shu’ara: 10
(( ﻳﺎ ﻋﻴﺴﻰ ﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ ﺍﺫﻛﺮ ﻧﻌﻤﺘﻲ ﻋﻠﻴﻚ ..))
“Ya kai Isa dan Maryam ka tuna
ni’imomina a kan ka..” Suratul Ma’ida:
110
(( ﻳﺎ ﺩﺍﻭﺩ ﺇﻧﺎ ﺟﻌﻠﻨﺎﻙ ﺧﻠﻴﻔﺔ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ))
“Ya Dawud! Hakika mun sanya ka
halifa a bayan kasa..”
” Suratu Sad: 26
Duk da haka a wurare 15 Allah ya yi
kiran sa amma ba in da ya kira shi da
sunan yanka kamar yadda ya kira su.
Sai dai ya ce masa ( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺒﻲ ) ko
kuma ( ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ).
Kai, ko a wuraren da sunansa ya zo a
tare da na kakansa uban annabawa
Ibrahim (AS), Allah ya fadi sunan
kakan, amma sai ya saya nashi suna.
Duba Suratu Ali Imran: 68 da Suratul
Ahzab: 7
(( ﺇﻥ ﺃﻭﻟﻰ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺈﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻟﻠﺬﻳﻦ ﺍﺗﺒﻌﻮﻩ ﻭﻫﺬﺍ
ﺍﻟﻨﺒﻲ .. (( ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ : ٦٨
Ma’ana: “Hakika mutanen da suka fi
cancantar Ibrahim su ne wadanda
suka bi shi da kuma WANNAN ANNABI
da wadanda suka yi imani”. Suratu Ali
Imran: 68.
(( ﻭﺇﺫ ﺃﺧﺬﻧﺎ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻣﻴﺜﺎﻗﻬﻢ، ﻭﻣﻨﻚ ﻭﻣﻦ ﻧﻮﺡ
ﻭﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻣﻮﺳﻰ ﻭﻋﻴﺴﻰ ﺍﺑﻦ ﻣﺮﻳﻢ( ( ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ : ٧
Ma’ana: “Ka tuna lokacin da muka riki
alkawali daga annabawa, da kuma
wurinKA da wurin Nuhu da Ibrahim da
Musa da Isa dan Maryam..” Suratul
Ahzab: 7.
4. Allah ya aiko annabawa zuwa ga
jama’arsu ne kawai. Nuhu zuwa ga
mutanensa, Hudu zuwa ga Adawa
mutanensa, Salihu zuwa ga danginsa
Samudawa, Shu’aibu zuwa ga
mutanen garinsu Madyan, Annabi
Ludu ma haka zuwa ga alkaryun
jama’arsa na Sadum. Duk a cikin
manzanni ba wanda aka aiko shi ga
duniya gaba daya sai Muhammad
Sallallahu Alaihi Wasallam. Allah
Ta’ala ya ce:
(( ﻗﻞ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻧﻲ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻟﻴﻜﻢ ﺟﻤﻴﻌﺎ ..))
Ma’ana: “Ka ce, ya ku mutane! Hakika
ni, manzon Allah ne zuwa gare ku
gaba daya”. Suratul A’raf: 158
Kuma an aiko shi ne don ya zama
rahama ga kowa da kowa, na farko da
na karshe. Talikai duka ba yan adam
kawai ba.
(( ﻭﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﻨﺎﻙ ﺇﻻ ﺭﺣﻤﺔ ﻟﻠﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ))
Ma’ana: “Ba mu aiko ka ba face sai
don rahama ga talikai”. Suratul
Anbiya’: 107
5. Ko a lahira manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam yana da karin matsayi
a kan sauran ‘yan uwansa manzanni
da annabawa. Domin kuwa shi ne
wanda kabari zai fara tsagewa ya fito,
kuma shi ne za a fara bude ma kofar
aljanna. Duk annabawa an ba su
damar yin addu’a guda daya da za a
karba ma su, amma shi sai ya ajiye
tasa sai ranar alkiyama. Don haka shi
kadai ne zai yi babban ceto (don
neman Allah ya yi wa bayi hisabi), shi
ke da tafkin Alkauthar, shi ne mai
“Liwa’ul Hamd” tutar da duk annabawa
zasu shiga a cikin ta. Ga shi kuma
duk ya fi su yawan mabiya a ranar
alkiyama. Sannan zai wanke
al’ummarsa ya yi ma ta sheda gaban
Allah, cewa al’ummar kirki ce, don ita
kuma ta yi ma sauran annabawa
sheda cewa, sun isar da manzanci.
Sai Allah ya karbi shedun al’ummarsa
ya yi hukunci a tsakanin annabawa da
wadanda suka karyata su daga cikin
mutanen su. Suratul Bakara: 143.
Wadannan dalilai da ire-iren su masu
tarin yawa sun tabbatar cewa, manzon
Allah Muhammad Sallallahu Alaihi
Wasallam cikamakin annabawa shi ne
limaminsu kuma shugabansu,
sa’annan mafifici a cikinsu. Kuma ma
dai da bakinsa mafi tsarki da albarka
ya fada cewa “Ni ne shugaban mutane
ranar alkiyama”. Sahih Al-Bukhari,
hadisi na 4435 da Sahih Muslim,
hadisi na 287 daga Abu Huraira (RA).
Ya Allah muna godiya da ka sa mu
cikin al’ummarsa. Ya Allah ka sanya
mu a cikin cetonsa.
Maganar darajojinsa yan uwa yanzu
muka fara. Ya Allah ka taimake mu.

Leave a Reply

Latest updates
Categories