Musulunci Ya Tsallata Zuwa Kasashen Waje
Ganin halin da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yake ciki bayan wafatin wadannan jigogin tafiyarsa guda biyu, sai Allah ya jefo ma sa tunanin fita daga garin Makka don ya nemi magoya baya watakila ko Allah zai kawo ma sa mafita a wani waje tun da su kam sun ki karbar falalar Allah da ya aiko ma su. A cikin watan Shawwal na shekara ta goma da muke magana a kan ta, manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam tare da rakiyar dan gidansa Zaid bn Haritha ya tasar ma gidajen kabilar Thaqif da ke garin Ta’if mai nisan kilomita 90 daga birnin Makka. Kasancewar Ta’if wani gari ne da yake kan tudu, wuri ne mai sanyi da ni’imar yanayi sabanin Makka. Quraishawa da yawa sun mallaki kadarori da gidaje a can, kuma akwai kawance mai karfi da auratayya a tsakanin su da ‘yan kabilar Thaqif mazaunan Ta’if. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi fatar samun matsugunni a wannan gari da kuma goyon baya, ba don kome ba sai don zai zama yankan baya ga mushrikan Makka wadanda suka takura ma sa a garinsu. To, sai dai a nan ma ‘yar gidan jiya ce, domin shugabannin Ta’if ba su ba shi hadin kai ba. Bayan sun yi ma sa maganganu na izgili da cin fuska kuma sai suka tura ma sa yara bata-gari suka yi ma sa rakiya da duwatsu; suka rinka jifar sa har in da ya bace ma su. Rigarsa ta jika sharkaf da jinin jikinsa da na kansa saboda jifa. Haka shi ma Zaid, a wajen kariyar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya gamu da irin abin da ya gamu da shi.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya dauki matakan tsaro da suka dace sosai wajen wannan tafiya. Da farko dai bai tafi a kan abin hawa ba, sai ya tafi a kasa domin ya batar da tunanin jama’a kan cewa barin garin zai yi. Idan kuwa har suka fahimci haka babu shakka zasu kawo ma sa tarnaki a cikin lamarin tafiyar. Na biyu kuma ya tafi tare da Zaid wanda aka san shi a matsayin dansa, ta yadda babu wani shakku a ganin su tare. Sannan ya roki shugabannin Ta’if bayan da suka ki karbar bakuncinsa da su rufa ma sa asiri kada su bayyana maganar zuwan sa can duba da irin tsarguwa da za ta same shi idan labarin zuwan sa ya je ma mutanen Makka tare da cewa bai samu karbuwa ba. Amma duk da haka ba su yi ma sa halin girma ba, sai suka bayyana al’amarinsa har suka sa aka jefe su zuwa bayan gari, shi da dan rakiyarsa. Mausu’at As-Siyar, na Sallabi (1/213).
Manzon Allah ya fito bayan garin Ta’if jina-jina har ga takalminsa, yana neman wurin da zai zauna ya huta. Ya shiga lambun wasu miyagun mushrikan Makka su ne Uutbatu da Shaibatu ‘ya’yan Rabi’ata suna kallon sa har ya samu wata babbar inwa ya zauna yana addu’a:
“Ya ubangijina! Zuwa gare ka kai kadai nake kai karar halin da nake ciki. Ya Allah! Karfina ya tafi, dabarata ta kare, mutane sun raina ni. Ya mafi jinkan masu jinkayi! Kai ne ubangijin masu rauni kuma kai ne ubangijina. Ina ne zaka jingina lamarina? A wurin na nesa da zai muzguna min? Ko wurin makiyin da ka riga ka damka ma sa al’amarina? Idan ba ka cikin fushi da ni, ya Allah, babu damuwa. Amma kuma na fi son kwanciyar hankali. Ina mai neman tsari da hasken fuskarka wanda ke kawar da kowane irin duhu, kuma yake gyara al’amarin yau da gobe, kada fushinka ya sauka a kaina, ko kyamarka ta far mani. Ina mai ba ka hakuri – ya Allah – har sai ka amince. Kuma ba ni da wani karfi ko dabara sai ta wajenka”. Sahih As-Sirah An-Nabawiyyah na Ibrahim Al-Ali, shafi na 136 da kuma Al-Hijrah An-Nabawiyyah Al-Mubarakah, na Dr. Abdurrahman Al-Bir, shafi na 38.
Domin cikon jarrabawar ubangiji sai Allah ya aiko ma sa mala’ika Jibrilu yana a kan hanyar sa ta komawa Makka a tare da rakiyar mala’ikan duwatsu, suna neman izninsa a kan halaka mutanen Ta’if saboda abin da suka yi ma sa. Sai ya ba su hakuri ya ce, ina fatar su shiriya. Ko kuma idan hakan ba ta samu ba a gaba zuriyyarsu ta ba da gaskiya. Ka ji halin girma daga fiyayyen halitta mafi tausayi da rahama ga talikai. Sahih Al-Bukhari, hadisi na 3231.
Duk da irin jarabawoyin da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya hadu da su a cikin wannan tafiya, amma ya samu manyan nasarori guda biyu:
Nasara ta farko: Musuluntar Addas; wani matashi kirista dan kasar waje wanda yake aiki a gonar su Utbatu inda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yada zango yana hutawa. A lokacin da wadannan mushrikai suka ga halin da yake ciki sun tausaya ma sa, sai suka aiki wannan yaron don ya kai ma sa tallafin dabino. Da zai ci ya yi bismillah, sai Addas ya tambaye shi cikin mamaki, a kan wannan kalma. Daga nan ne manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya samu mashiga ta kiran sa zuwa ga musulunci kuma nan take ya karba.
Nasara ta biyu: Musuluntar ayarin aljanu su bakwai wadanda suka saurari karatunsa a cikin kiyamullaili a kan hanyarsa ta komawa Makka. Sun musulunta nan take kuma suka dauki sakonsa zuwa ga ‘yan uwansu aljannu suna yi musu wa’azi da abin da suka ji. Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya ba manzonsa labarinsu a cikin Suratul Jinn da kuma Suratul Ahqaf. Daga bisani bayan aljannu da yawa sun musulunta ta hanyar wadannan masu wa’azi sai suka aiko ma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya je ya karantar da su, kuma ya ba su guzurin abinci daga sauran abin da al’ummar muminai suka ci. Sahih Muslim, hadisi na 150.
Hikimomin Allah da yawa suke. Wannan alheri da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kawo ma mutanen Ta’if ba su karbe shi ba, kirista dan kasar waje ya karba. Kuma duniyar aljannu ita ma ta karba. Idan Quraishawa sun azabta sahabbansa daga cikin mutane, to ya zasu yi da sahabbai aljannu?!
Leave a Reply