ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 67( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Musulmai Sun Sake Komawa
Habasha
A can baya mun ga yadda musulmi
suka dawo daga kasar Habasha suna
cike da fatar samun sassafci bayan
da suka ji labarin cewa, manyan
jarumawa guda biyu sun shiga
musulunci. To, amma ashe abin ba
haka yake ba. Domin kuwa
Quraishawa sun sake jan damara
domin yaki da musulmi, kuma sun
fito da wasu sababbin hanyoyi na
azabta su. Abin da ya sa dole aka
sake umurnin su su koma Habasha.
A wannan karon ma sai adadinsu ya
karu daga 14 zuwa sama da 100.
(Mazaje 82 da mataye 18, tare kuma
da wasu kananan yara daga cikin
‘ya’yansu). Kamar wancan karon dai
ayarin musulmi a cike yake da
makusantan manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam wadanda suka hada
da; Ja’afar bn Abi Talib; dan
baffansa, da Usman bn Affan;
surukinsa da ma ‘yar cikinsa
Rukayya, matar sayyidi Usmanu.
Quraishawa sun damu matuka da
sake yin hijira. Kamar dai suna ganin
dole ne musulmi su zauna su yi ta
jurewa duk wahala da azabar da suke
ba su, amma ba su da hakken su
yawata a cikin kasar Allah mai fadi in
da za su samu ‘yancin kansu. Nan
take suka shirya tafiyar wakilai guda
biyu don su gana da sarkin Habasha
wanda zai ba su damar ingizo keyyar
musulmi a dawo da su gida a
tunaninsu. Wakilan da aka tura su ne:
Amru bn Al-Ass da Abdullahi bn abi
Rabi’ata wadanda ake ganin sun
kware wajen iya huldar jakadanci
kuma sun iya bakinsu wajen isar da
sako. Sannan aka shirya kyaututtuka
na musamman zuwa ga sarki da duk
fadawa da ‘yan majalisarsa a
matsayin cin hanci don a samu hadin
kansu. Sun bayar da kyautar fatu
wadanda aka yi jimar su ga kowane
daya daga cikin ‘yan majalisa da
fadawa kafin su kai ma sarki nasa.
Da suka samu ganawa da sarki suka
gabatar masa da tasa kyauta sai suka
fada masa cewa, sun zo ne suna
wakiltar al’ummar kasarsu kuma sun
kawo karar ‘ya’yansu da suka fandare
masu, suka fice daga addininsu kuma
ba su shiga addinin sarki ba. “Bayan
haka, sun raba kanmu, sun zagi
ababen bautarmu, sun wautar da
iyayenmu. Don haka, bukatarmu ita
ce, sarki ya ba mu izni mu ingiza
keyarsu mu koma da su gida mu
dauki matakin da ya dace a kan su
tun ba su bata ma sarki kasarsa ba”.
In ji wakilan.
Da yake daman an shirya da sauran
‘yan majalisa sai duk suka goyu
bayan su, suka nemi sarki ya yi abin
da suke so ba tare da ya saurari
wadannan mutane ba. Amma Najashi
mutum ne mai hankali, kuma adili.
Sai ya ce, wallahi ba za a taba yin
haka ba. Mutane su baro kasarsu ta
gado, su kaurace ma iyayensu, su
zabi kasata da zama cikin jama’ata
sannan in kore su ba tare da kowane
irin yankan hujja ba! Sannan ya yi
umurni aka kira su don ya ji ta
bakinsu.
Cikin wakilan Quraishawa ya dauki
ruwa sosai da wannan mataki da
sarki ya dauka. Domin sun san cewa,
idan ya saurare su ya ji irin halin da
aka sa su babu gaira babu dalili lalle
ne zai tausaya ma su.
Kafin su zo wurin sarki, sahabbai sun
yi matsaya a kan shugabantar da
Ja’afar bn Abi Talib don ya zama mai
magana da yawunsu. Kuma sun yi
alkawarin ba za su fada ma sarki
karya ba a cikin duk abin da ya
tambaye su. Da zuwan su sarki ya
tambaye su, wane irin addini ne kuke
yi wanda ba shi ake yi a kasarku ba,
ba kuma shi muke yi a nan ba,
sannan kuma kowa bai san shi ba?
Ja’afar ya kada baki ya ce, Allah ya
dade ran sarki. Mu dai a can da a
kasarmu cikin duhu muke. Muna
bautar gumakan da muka sassaka da
hannayenmu, muna cin mushe, muna
aikata alfasha, muna yanke zumunta,
muna cutata ma makwauta, kuma duk
wanda yake da karfi sai ya ci zalun
wanda bai kai shi ba. Muna haka, sai
Allah ya aiko mana manzo a cikinmu.
Duk mun san shi, mun san
matsayinsa da asulinsa. Mun kuma
tabbatar da gaskiyarsa, nagartarsa,
amanarsa da kamun kansa. Wannan
manzo sai ya kira mu zuwa ga
kadaita Allah da bauta, ya ce mu
daina bin gumakan da iyayenmu suka
kasance suna bauta. Ya ce kuma mu
rike gaskiya da amana, mu sada
zumunta, mu kyautata ma makwauta,
mu daina cin kazanta kamar jini da
mushe, mu daina ayyukan alfasha da
shedar zur da cin hakkin maraya da
yin kazafi ga mutanen kirki. Sannan
ya umurce mu mu bauta ma Allah shi
kadai ba tare da mun sanya ma sa
abokin tarayya ba. Ya umurce mu mu
yi sallah, mu ba da zakka, mu yi
azumi. Allah ya taimaki sarki, a kan
haka ne muka bi shi, muka halalta
abin da Allah ya halalta, muka
haramta abin da ya haramta. Kawai
sai sarakunan garinmu suka tsane
mu, suka kafa mana kahon zuka. Ba
kuma irin fitina da azabar da ba su yi
mana ba a kan wai sai mun koma
cikin duhu bayan Allah ya yi walkiya
mun gane hanyar gaskiya. Ganin
haka ya sa muka kamo hanya zuwa
garinka muna neman mafaka don
mun ji labarin kana adalci, ba ka
cuta.
Sarki ya kaxa kai sannan ya ce, to,
kun zo da wani abu cikin abin da
yake karanta ma ku? Ja’afar ya ce,
kwarai kuwa. Sannan sai ya karanta
ma sa farkon Suratu Maryam, in da
Allah ya yi bayanin mahaifiyar annabi
Isah Alaihis Salam da nagartar
iyayenta da tarihin haifuwarta da
ibadarta, har zuwa haifuwar annabi
Isah Alaihis Salam da yadda ya fitar
da ita kunya bayan Yahudawa sun
zarge ta. Ko da Ja’afar ya gama
karatu sarki da malamansa duk sun
jike gemmansu da hawaye saboda
dadin karatu da tasirinsa, kai har
littattafansu duk sun jike sharkaf da
hawayensu. Sarki ya ce, wallahi
wannan littafi naku mafitarsa daya ce
da wanda annabi Musa Alaihis Salam
ya zo da shi. Kuma ba zan taba bari
a cutata maku ba. Ku je duk in da
kuke so ku zauna a cikin kasata na yi
maku izni. Ku kuma ku tafi da
kyautarku, ba na bukata, domin ni
ban bai wa Allah cin hanci sadda ya
ba ni mulkin nan ba. Musnad Ahmad,
hadisi na 1740.
Karya fure take ba ta ‘ya’ya. Wani
hani kuma ga Allah baiwa ne. Najashi
dai daga wannan zaman ne ya kulla
alaka da musulmi kuma ya rinka
sauraron karatun Alkur’ani, har ma ya
samu alaka ta kai tsaye da manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam;
yana aike ma sa sakonni, shi ma
kuma manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yana yi ma sa aike. A
dalilin wannan alakar tasu ne ma ya
sa manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya umurce shi ya daura ma
sa aure da Ramlatu matar da
Ubaidullah bn Jahsh ya bari bayan
cikawarsa a can. Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya tausaya
ma iyalin wannan bawan Allah
kasancewarsa mutumin kirki, ita
kuma ‘yar babban gida ce a garin
Makka, domin diyar Abu Sufyana ce,
amma ta bar jin dadin duniya ta bi
mijinta zuwa Habasha don su tsira
da addininsu. A cikin auren ta kuma
har wayau akwai wata manufa ta
siyasa. Muna gane wannan in muka
san cewa, Abu Sufyana, wanda tuni
ya daura damarar yaki da addinin
musulunci jikinsa ya yi sanyi matuka
da jin cewa, manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam ya daura aure da
diyarsa. Najashi ya yi ma ta sadaki a
madadin manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallam irin sadakin ‘yan
alfarma; dirhami 4000.
Duk da yake yanayin jama’arsa bai
ba shi damar bayyana musuluncinsa
kowa ya sani ba, amma Najashi ya
musuluntar da iyalansa da
amintattunsa, kuma ya bai wa
musulmi dama sun yada addini a
cikin kasarsa.
Muhimmin darasi a cikin wannan
tarihi shi ne cewa, da yawa Allah
yakan yi amfani da rundunar karya
don ya taimaki gaskiya. Dubi yadda
Allah ya juyar da makircin
Quraishawa don bice hasken addini
ya koma babban makami na
taimakonsa da bunkasa shi. Sun yi
amfani da duk hanyoyin da suke
iyawa har da ba da cin hanci. Amma
kuma sai Allah ya taimaki gaskiya. Ta
bangaren musulmi kuma muna iya
lura da zaben Ja’afar da aka yi a
matsayin wakilin musulmi da irin
hikimar da ke tattare da jawabinsa da
ma surar da ya zaba don karanta ma
Najashi.
A lokacin da ajali ya cim ma Najashi,
sayyidi Jibrilu Alaihis salam ya sanar
da manzon Allah, shi kuma ya sanar
da musulmi a Madina, sannan ya
shiga gaba, suka yi sahu-sahu suka
yi ma sa sallar jana’iza ta wanda ba
ya kusa “Salatul Ga’ib”. Sahih Al-
Bukhari, hadisi na 1333 da 3877.
Duba kuma: Usd Al-Gaba (1/99) da
Al-Isaba (1/109).
Wani darasi da bai kamata mu shude
a kan sa ba shi ne fatawar da shehin
musulunci Ibnu Taimiyya
Rahimahullahu ya gina a kan wannan
qissa. Fatawar ta duba cewa, su
wadannan da suka yi hijira zuwa
Habasha suna can ne aka kara yawan
raka’oin sallar azahar da la’asar da
Isha’i suka koma hudu-hudu, a yayin
da ita kuma sallar magriba aka kara
ta ta koma raka’a uku bayan a da
dukkansu raka’oi bi-biyu ne. Ya ce,
kuma ba mu ga in da aka samu
cewa, manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya umurce su da su rama
sallolin da suka yi kafin su san da
wannan kari ba. Ya ce, daga nan
muke fahimtar cewa, jahiltar wasu
lamurran addini idan ba da gangan
ba ne, ba ta wajabta ukuba ga mutum
ko bacin ibadarsa. Majmu’u Fatawa
Ibn Taimiyyah, (22/43).

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ALKAKI DA RUWAN ZUMA Ingantaccen Tarihi, Matsayi Da Darajojin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi Wasallam Majalisi Na 67( Dr. Mansur Sokoto)”
  1. aminu abubakar Avatar
    aminu abubakar

    Annabi (S.A.W) yaji Wani Mutum Yana Cewa (Allahumma Inni As’Aluka Bi Anni Ashhadu Annaka Antallahu La’Ilahailla Anta Al Ahadu, Assamadu, Allazi Lam Yalid Walam Yulad Walam Yakun Lahu Kufu’an Ahad) sai Annabi Yace: Hakika Ya Roki Allah Da Sunansa Mai Girma Wanda In An Rokeshi Yake Bayarwa,in An Kirashi Yake Amsawa.

Leave a Reply

Categories
Latest updates