Haqiqa Qiyaama Ta kusa! Karanta wannan hadisin!
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻣﻮﺳﻰ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ؛ ﻗﺎﻝ: ﻛﺎﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺤﺪﺛﻨﺎ” :ﺃﻥ ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ
ﺍﻟﻬﺮﺝ.” ﻗﻴﻞ: ﻭﻣﺎ ﺍﻟﻬﺮﺝ ؟ ﻗﺎﻝ” :ﺍﻟﻜﺬﺏ ﻭﺍﻟﻘﺘﻞ.” ﻗﺎﻟﻮﺍ:
ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻤﺎ ﻧﻘﺘﻞ ﺍﻵﻥ ؟ ﻗﺎﻝ” :ﺇﻧﻪ ﻟﻴﺲ ﺑﻘﺘﻠﻜﻢ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ،
ﻭﻟﻜﻨﻪ ﻗﺘﻞ ﺑﻌﻀﻜﻢ ﺑﻌﻀﺎ، ﺣﺘﻰ ﻳﻘﺘﻞ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺟﺎﺭﻩ،
ﻭﻳﻘﺘﻞ ﺃﺧﺎﻩ، ﻭﻳﻘﺘﻞ ﻋﻤﻪ، ﻭﻳﻘﺘﻞ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﻪ.” ﻗﺎﻟﻮﺍ:
ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ! ﻭﻣﻌﻨﺎ ﻋﻘﻮﻟﻨﺎ ؟ ﻗﺎﻝ” : ﻻ، ﺃﻻ ﺇﻧﻪ ﻳﻨﺰﻉ
ﻋﻘﻮﻝ ﺃﻫﻞ ﺫﺍﻙ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ، ﺣﺘﻰ ﻳﺤﺴﺐ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺃﻧﻪ ﻋﻠﻰ
ﺷﻲﺀ ﻭﻟﻴﺲ ﻋﻠﻰ ﺷﻲﺀ.
An karbo daga abi musa(Allah kara masa yarda) yace: ‘Manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana bamu labari, a gabannin tashin alqiyaama akwai haraj. Sai sukace meye Haraj ya manzon Allah? Sai yace karya da kisa, sai sukace fiye da yadda muke kashewa yanzu?? Sai yace a’a bawai kisa da kukewa kafirai ba. Sai dai kisa da zaku rinkayi wa juna, har mutum ya kashe makwabcinsa, ya kashe dan’uwansa, ya kashe baffansa, ya kashe dan baffansa, sai sukace subhanallah. Kuma muna tare da hankulanmu? Sai yace A’a. Ku saurara kuji, za’a zare hankulan mutanen wannan zamanin, har dayansu zaiyi tunanin yana kan wani abu amma baya kai!!!!
Hasbunallah! Hasbunallah! Hasbunallah!
Yaaa Allah Ka tserar damu. Alamun tashin Qiyaama dada bayyana suke, Kowa Yaji tsoron Allah Ya gyara ayyukansa. Mukoma zuwa ga Allah. Yaa Allah kajikanmu, Ka tsamar damu daga cikin wannan rikita rikita. Ameeeeen!
Wannan hadisin Ibn majah, Ahmad, Abu Ya’ala,dabaraani, nu’aim bin hammad duk sun rawaito.
Leave a Reply