Ayyamut-tashriq sune kwanaki uku bayan Ranar Sallar Idi babba.
- Anaso Musulmi ya yawaita ambaton Allah acikin wa’innan kwanaki, Musamman Kabbarori ” Allahu Akbar, Allahu Akbar La’ilaha illallah Wallahu Akbar Allahu Akbar Walillahil Hamd”
- Ranaku ne na ci da sha Sabida haka ba’a yin Azumi acikinsu, kamar yadda ba’a yin Azumi ranar Sallah.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Ayyamut-tashriq Ranaku ne na ci da sha
Sahih Muslim: 1141
Haka nan an rawaito daga Ibn Umar Allah ya ƙara masa yarda yace:
Ba’ayi rangwamen yin azumi acikin Wa’innan kwanaki ba, sai dai ga wanda bai samu Hadaya ba.
Sahihul Bukhari: 1998
Leave a Reply