Muslim ya rawaito hadisi Acikin Sahihinsa. Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) yace:
من صلى صلاة الصبح فهو في ذمة الله، فلا يطلبنكم الله من ذمته بشيء، فإنه من يطلبه من ذمته بشيء يدركه، ثم يكبه في نار جهنم .
Abinda Hadisin yake bayani a Jumlace shine: Duk wanda yayi sallan Asubahi. Ana nufin yayi ta a lokacin ta, kuma acikin Jam’i in ya zamto yana daga cikin wa’inda Jam’i ta hau kansu kuma bashi da wani uzuri. Toh yana ƙarƙashin kulawar Allah da Amincin sa. Kada ku yadda ku cutar dashi har Allah ya kamaku da laifin kun cutar da wanda ke ƙarƙashin Amincinsa da Kulawarsa. Domin duk wanda yayi haka Allah zai kamashi kuma ya kifar dashi a wuta.
Wannan hadisin yana daga cikin hadisan da suke nuna Falalar sallan Asubahi. Da kuma girmanta, domin babu mai kiyayeta sai mai ƙarfin imani, kuma itace sallah da tafi nauyi akan munafukai, da ita da Sallar Isha’i, ba kowa yake iya kiyayeta ba. Kuma da mutane sun san falalarta da koda da ja da ciki zasuje suyi ta.Read More…