Ahlussunnah na Hakikah 2(sheikh yakubu musa hassan)

Babu Shakka Ahalussunah
Na HAKIKA shine Wanda
Yayarda Cewa Dunkulewar
Al Ummar kMusulmi Wuri
Guda Da tab attar Da
Samuwar Haadin Kansu’
Bisa Gimshikannan Guda
Ukku Shine Babban Mabudin
Alkhairi Garesu Lau Kanu Ya
alamuun Domin Sanya Al
Ummar Musulmi Bisa Hanya
Guda Daya Tak Bisa
Alkuraani Da Hadisi Da
Ijmaai Bisa Fahimtar
Magabata Shine Asalin
MUSULMCI Kuma Babu
Shakka Makiyanmu Kuma
Abokanan Gabarmu Sunsan
Wannan Dan Suke Aiki
Badare Barana Dan Suga
Hakan Baisamuba Domin
Sunsan Wannan Shine
Karfinmu Da Daukakarmu ,
Kuma Tabbas Munsani
Manufa (ﻫﺪﻓﻲ) Mafi Girma
Bazaiyiwu A Tabbatar dashi
a Saita Hanyar Samsun
Wannan Cikakken Hadin
Kan Da Kuma Kakkarar Yan
Uwantaka Ta Gaskiya, Shin
Don Allah In Babu Kaunas
Da Yan Uwantaka Tayaya Za
A Samu Hadinkai? To Yan
Uwa Kafin Muzama
Ahalussunah Na HAKIKA sai
Mun Tabbatar Da Wannan ,
To Yaya Zaka Iya
Kuwa?

Ahlussunnah na Hakikah(sheikh Yakubu Musa Hassan)

Alhamdu Lillah wassalatu
wassalam ala RasulilLah.
Baya halarta ga dukkan malami
ahlussunnah na gaskia ya raba
kan mutane,ya jawo abinda zai
Sanya GABA da kiyaiya tsakanin
yanuwa Musulmi musamman
Malamai. Yin haka aikin yan Bid’a
ne.amma ahlussunnah
malamansu da mabiyansu kullun
suna nunawa mutane cewa
dukkan musulmai dole ne su
kasance Kaman yanuwa
wadanda suka fito Ciki daya. Su
kasance masu taimakon junansu
a wajen dukkan aiyuka na alkhairi
da na taqwa.
Sunnah bata yarda ba wani ya
jingina ga wani Shehi,wani
Malami Ko wata Kungiya, ya
daura kaunarshi Ko kuma
Gabarshi a kansu. A’a sunnah
abunda tace shine ka kaunaci
duk Wanda ya kasance ahalin
Imani ne, da Wanda aka sanshi
da tsoron Allah.a cikin dukkan
Malamai Ko kuma cikin kowace
Kungiya.
Kada ka yarda ka fifita wani da
wata kauna ta musamman, sai
Wanda Imanin shi da Taqwarsa
suka bayyana fiye da Sauran, Ko
da daga wace Kungiya Yake.
Watau dai ka fifita Wanda Allah
da Manzosuka fifita.
Wannan shine hakikanin akidar
Ahlussunnah na gaskia…