Ahlussunnah na Hakikah(sheikh Yakubu Musa Hassan)

Alhamdu Lillah wassalatu
wassalam ala RasulilLah.
Baya halarta ga dukkan malami
ahlussunnah na gaskia ya raba
kan mutane,ya jawo abinda zai
Sanya GABA da kiyaiya tsakanin
yanuwa Musulmi musamman
Malamai. Yin haka aikin yan Bid’a
ne.amma ahlussunnah
malamansu da mabiyansu kullun
suna nunawa mutane cewa
dukkan musulmai dole ne su
kasance Kaman yanuwa
wadanda suka fito Ciki daya. Su
kasance masu taimakon junansu
a wajen dukkan aiyuka na alkhairi
da na taqwa.
Sunnah bata yarda ba wani ya
jingina ga wani Shehi,wani
Malami Ko wata Kungiya, ya
daura kaunarshi Ko kuma
Gabarshi a kansu. A’a sunnah
abunda tace shine ka kaunaci
duk Wanda ya kasance ahalin
Imani ne, da Wanda aka sanshi
da tsoron Allah.a cikin dukkan
Malamai Ko kuma cikin kowace
Kungiya.
Kada ka yarda ka fifita wani da
wata kauna ta musamman, sai
Wanda Imanin shi da Taqwarsa
suka bayyana fiye da Sauran, Ko
da daga wace Kungiya Yake.
Watau dai ka fifita Wanda Allah
da Manzosuka fifita.
Wannan shine hakikanin akidar
Ahlussunnah na gaskia…

Click Here to Support our work

3 Comments

  1. Kaji gaskiya daga ma’abotanta
    Allah yatabbatar damu akan hanyar shugan halitta s.a.w
    Allah yasaka ya kara karfin guiwa malama

  2. Masha Allah sannu da kokarin yada sunna Allah yasaka da alkhari, kuma ina shawartanku da ku bude filin amsa tambayoyi da tarihin sahaban Annabi (s.a.w)

Leave a Reply

%d bloggers like this: