LABARI: zuwa ga masu son tabuka wani abu a rayuwa(Sheikh Zakariyyah Hassan Yakub)

Wani mutum ya kai ziyara gidan Zoo,
sai yaga wata qatuwar giwa an daureta
da karamar igiya, ba’da sarkoki ko
manyan igiya ba, Abin mamaki
wannan giwar idan taso zata iya
warware igiyar ba tare da matsala ba,
amma batayi ba.
sai mutumin ya hango mai lura da
wannan giwa, sai yaje wurinsa ya
tambayesa, ko meyasa wannan giwa
duk da karfin da take dashi, amma bata
kokarin ta gudu? ai wannan igiyar
bazai hana ta ba ko?
Sai mai gadin yace: Lokacin da irin
wadannan manyan dabbobi suke
kanana, mun saba daure su da sarkoki
da manyan igiya, ta yanda bazasu iya
warwarewa ba, saboda haka suna girma
DA WANNAN TUNANIN NE A
ZUCIYARSU, don haka wannan
tunanin shi ya gallebesu har suka yarda
cewa bazasu iya warwarewaba.
ABIN mamaki, Ace wannan Qatuwar
dabba mai karfi siya, amma ga karamin
igiya ta gagareshi? saboda yasa a
zuciyarsa cewa bazai iya ba, don haka
ya zauna guri guda?.
Abin lura anan shine: yawancin mutane
kamar giwa suke, sun gamsar da
zuciyarsu cewa bazasu iya wani sanaa
ba ko karantar wani course ba. cikin
sauki sun yarda cewa bazasu iyaba, don
wata kila sun taba gwadawa basuyi
nasara ba, shikenan sai su
hakura.wannan ba daidai bane.
Don haka ya yan uwana, kuyi kokarin
gabatar wa Al’ummarku wani abu mai
anfani, ku cire batun bazan iya ba a
zuciyarku, komai zaku iya inshallah,
Al-umma na jirarku. Allah ya
taimakemu.

GUJEWA HARAM DON KADA ZUCIYARKA TAKI HALAL(Sheikh Zakariyya Hassan Yakub)

YANA KYAMATAR MATANSA
NA AURE. ko meye dalili?
Wani bawan Allah ne ya kai korafinsa
ga wani malami, akan cewa ya auri
matarsa, shekaru kadan da suke wuce,
yana da yara biyu da ita, amma akoda
yaushe sai ya rika ganin tana dada
muni a idonsa, kuma baya sonta cikin
zuciyarsa.
sai malamin ya tambayeshi, matar
naka tayi qibace sosai, sai yace a’a,
tayi hasarine da ya sanja halittarta? sai
yace a’a, halayenta basu da kyau ne?
yace a’a, sai malamin yace, amma kana
yawan kallon mata ko? sai yace ey,
kana kallon finafinai na batsa ko? yace
ey, sai malamin yace dole haka ya
kasance, domin duk lokacin da zuciya
ta saba da haram, idan mutum yana cin
haram ya sha haram, ya kwanta a
haram toh dole ya kyamaci halal, don
haka mu guje wa haram don jin dadin
halal. Allah yasa mu dace.

BOKANCI CIKIN SABON SALO 2014(Zakariyya Hassan Yakub)

Yan uwa na masu albarka, kamar yanda muka sani ne annabi ya hanamu imani da bokaye, da kuma masu duba ko anfani da taurari, amma abin mamaki sai muna ganin wata irin sabon salo na fadin abinda zai iya faruwa a farkon ko wane shekara na miladiyya, har zuwa karshenta, a shekaru uku da suka gabata wato 2011,2012, 2013, wasu sun bayyana cewa zaa sami faduwar wasu shuwagabanni, da kuma tashin hankali da makamantarsu, gashi kuma hakan ya faru, to gashi wannan shekara ma 2014 ta shigo, sai gashi sun fito da cewa zaa ci gab na da samun tashin hankali a duniyar mu na musulmai, har ya kai da cewa zaa kashe mana gwarzo,kuma shuguba,adali muhd morsi na misra, da kuma wasu abubuwa marassa dadin ji da kuma ambato, toh a masayinmu na musulmai, bamu yarda da wannan ba,,sanna munyi imani cewa duk wani abu da ya faru damu daman Allah ya riga ya rubuta, muna fatan dacewa duniya da lahira, don haka ina rokon Allah da sunayensa wannan shekara da zamu shiga na 2014, dukkan alheri da ke cikinta ka hada al’umman annabi muhd da ita, haka kuma dukkanin wani sharri ka raba al’umman annabi da ita,don haka yan uwa kada irin wannan abubuwa su daga mana hankali, muci gaba da addua, Allah zai cika haskensa ko da kafirai sunki.

KALLON BALL TANA HAIFAR DA BALA'I UKU(Sheikh Zakariyya Hassan Yakub)

Abin mamaki kallon kwallon kafa ya shiga rayuwar musulmi, abin hauci ma har da masu addini, alhali suna mantawa cewa tana iya haifar da bala’i har uku manya.
1- MANUFURCI, babban abinda take haifarwa musulmi shine kaunar kafiri wanda Allah ya hanemu da kaunarsa, don kuwa zuciya daya, bazata iya hada kaunar annabi da na kafuri makiyinsa ba.
2-HASARAR LOKACI, Lura da cewa lokaci ita ce mafi tsada a rayuwar musulmi, annabi yace dan Adam zaiyi nadamar second guda idan bai ambaci Allah ba.toh yanzu awa nawa muke mudauka wajen kallon ball?
3-KIYAYYA, Wasu zasu ce ai wasa ne, amma abin mamaki shine Ball ya wuce yanda muke sammaninsa, don kuwa wani baya iya barci don murna ko bakin ciki, akan nasara ko rashinsa ga team nasa, sannan yana kaiwa da zage zage ko dake doke, akan wani wanda bai sanda kai ba, wata kila idan da zai ganka ma, sai ya rufe hancinsa don kyamarka.
Don haka yan uwa na masu albarka mu kaurace wa kallon ball ko zamu sami rabo a ranar qiyama, lura da cewa duk second a rayuwarmu zaa tambayemu shi. Allah ya sa mudace.

YANDA ZAKA GANE MAKARYACI CIKIN SAUKI(Zakariyya Hassan Yakub)

Lura da cewa karya tana daga cikin munanan abubuwa wanda Allah ya haramta, harma yakai da ya tsine wa mai karya amma yanzu abin mamaki karya ya zamo abin ado. Alhali kuwa itace tushen sharri a rayuwa.
1-zaka iya gane makaryaci daga ido, don kuwa baya so ya rika hada ido da kai yayin da ke magana, zaka gansa yana kalle kallen gefe.
2-zaka ganesa wajen yawan mutsi dake yi, kamar yin wasa da gashi, ko sosan fuskarsa ko balle kumbarsa da hakori, sannan baya iya zama cikin nutsuwa.
3-zaka iya gane sa wajen magana, ta yanda wani lokaci zaka ji yana magana yana inda-inda,sannan yana nisantan anfani da Kalmar Ni, so da yawa makaryaci yakan jingina karyarsa ga wasu ne. sannan kuma makaryaci yana da yawan mantuwa.
Amma abin mamaki ramin karya kurarriyace, wata rana asirinsa zai tonu. Allah ka karemu da karya.