Mai rubutu: Hamza Diso
Imamul Bukhari ya ruwaito hadisi da sanadinsa zuwa Abdullah bn Amr zuwa Annabi Salatin Allah da Amincin sa Su tabbata gare shi yace:
Cikakken musulmi shine Wanda musulmai suka kubuta daga harshen sa (baya cutar da mutane da magana), (suka kuma kubuta daga) hannun sa (baya cutar dasu da hannun sa), Cikakken mai hijrah shine Wanda ya guji Abinda Allah ya hana.
Ibn hibban da hakim sun ruwaito wannan hadisin tare da Karin jumlar ” Cikakken mumuni shine Wanda mutane suka kubuta daga gare shi (baya cutar da mutane).
Abun lura: wannan hadisin yana nuna haramcin Yin duk wani abu da zai cutar da mutane ( sai dai bisa hakki na Shari’a), saboda haka bai halatta a fadawa mutum maganar da zata bata masa rai ko ta munana masa ba sai dai idan shine ya Fara zalunci.
Allah yace:
لا يحب الله الجهر بالسوء من القول إلا من ظلم.
Haka bai halatta a cutar da mutum da duk wani nau’i na aiki ba komai kankantar sa.
Rashin cutar da mutane wani yanki ne daga cikin yankunan imani, wato mutum bazai taba zama Cikakken mumuni ba har sai ya guji cutar da Al’umma, don shi imani yanki-yanki ne har Sama da yanki sittin kamar yadda Annabi ya fada acikin hadisin Bukhari da Muslim.
Har wayau hadisin yana ishara kan cewar shi hakki fa Kala biyu ne akan kowanne musulmi.
- hakkin Allah akan sa
- hakkin mutane akansa
Shi Hakki na mutane yafi cutar da mutum, don lamarin bayi ana dora shine akan rashin yafiya, duk mutumin daya mutu yana cutar da mutane to yana cikin hatsarin gaske, wannan shiyasa ma wasu cikin malamai suke ganin idan zakka ta hadu da biyan bashi acikin dukiyar mamaci to za a fara biyan bashi ne kafin zakka( wato gabatar da hakkin Dan Adam) musamman idan Munce zakka hakkin Allah ne ba hakkin talakawa a cikin dukiyar masu kudi ba, Don mas’alar akwai saɓani.
Abun nufi Kawai shine wajibi ne akan musulmi yayi kaffa-kaffa da duk abinda zai kaishi ga cutar da mutane.
Leave a Reply