Zikiri yana daga cikin Ibada mafi girma da ake so Musulmi ya lazimce shi a kowani lokaci, sannan kowani zikiri yana da falalar sa, a yau zamuyi magana ne akan wani zikiri mai falalar gaske.
An Rawaito daga Abi Huraira Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
مَنْ قَالَ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ ؛ كَانَتْ لَهُ عَدْلَ عَشْرِ رِقَابٍ ، وَكُتِبَ لَهُ مِائَةُ حَسَنَةٍ ، وَمُحِيَتْ عَنْهُ مِائَةُ سَيِّئَةٍ ، وَكَانَتْ لَهُ حِرْزًا مِنْ الشَّيْطَانِ يَوْمَهُ ذَلِكَ حَتَّى يُمْسِيَ ، وَلَمْ يَأْتِ أَحَدٌ بِأَفْضَلَ مِمَّا جَاءَ ، إِلَّا رَجُلٌ عَمِلَ أَكْثَرَ مِنْهُ
Sahihul Bukhari: 3293 Sahihu Muslim: 2691
Fassara/Sharhi
Duk wanda yace "La'ilaha illallah Wahdahu la sharika lahu lahulmulku wa Lahul hamdu wa huwa Ala Kulli shai'in ƙadir" a yini sau ɗari zai samu lada kamar wanda ya ƴanta bayi goma, za'a rubuta masa lada ɗari, za'a share masa Zunubai ɗari, sannan zata zama kariya a gareshi daga Shaiɗan a wannan yini nashi har yammaci, kuma babu wanda zai zo da mafificin abinda yazo dashi sai dai wanda yayi fiye da wanda yayi
Fassarar Zikirin
Babu Abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaɗai bashi da abokin tarayya, Mulki duka nashi ne, Godiya duka nashi ne, Sannan shi mai iko ne akan komi
Wannan zikiri yana da falala sosai ya kamata Musulmi ya lazimce shi.
Shin dole sai an yi su lokaci guda ko za’a iya yin su a rarrabe?
A Nassin Hadisin Annabi bai ƙayyade cewa dole sai anyi su a jere har ƙafa ɗari ba, abinda akeso shine a yi su a yini ɗaya, Mutum zai iya rarrabe wa, yayi goma ya huta, anjima yayi ya huta, inkuma zaiyi duka lokaci ɗaya to hakan shi yafi falala Kamar yadda Imamun-Nawawy yayi bayani a sharhinsa na Sahihu Musulim: 17/17
Allah yasa mudace
Leave a Reply