Bismillahir Rahmanr Rahim
Ya ku bayin Allah!
Ba wata da’a ko ibada ko aikin lada
da Allah madaukakin sarki ya ba
shi muhimmanci a cikin Alkur’ani –
bayan kadaita Allah – kamar yadda
ya bada muhimmanci ga da’ar
iyaye.
ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ) :ﻭﺍﻋﺒﺪﻭﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﺗﺸﺮﻛﻮﺍ ﺑﻪ ﺷﻴﺌﺎ
ﻭﺑﺎﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﺇﺣﺴﺎﻧﺎ.(ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ 36:
Da’ar iyaye na nufin bayyana son
su, da darajanta su, da kiyaye
alfarmarsu, da kauce ma fushinsu
da biyan bukatarsu.
Idan mutum ya yi nazarin wahalar
da iyaye suka sha wajen tashinsa
da daure ma kuruciyarsa har zuwa
sadda zai yi hankali shi kadai ya
isa ya nuna masa girman
hakkensu a kan sa. To, ina ga
kuma an duba alhakin uwa na
daukar ciki wata tara tsakanin
lafiya da ciwo, laulayi da haraswa,
da kyamar abinci da raunin jiki da
nauyin ciki har zuwa ga nakuda
wadda wata ‘yar karamar lahira ce
mata suke zuwa a mafi yawan
lokuta!
Annabawa sun kasance masu
tsananin biyayya ga iyayensu:
– Isma’il da mahaifinsa Ibrahim sun
gina ka’aba
ﻓﻠﻤﺎ ﺑﻠﻎ ﻣﻌﻪ ﺍﻟﺴﻌﻲ ..
ﻭﺇﺫ ﻳﺮﻓﻊ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﺍﻟﻘﻮﺍﻋﺪ
– Isa (AS):
ﻭﺑﺮﺍ ﺑﻮﺍﻟﺪﺗﻲ ﻭﻟﻢ ﻳﺠﻌﻠﻨﻲ ﺟﺒﺎﺭﺍ ﺷﻘﻴﺎ
– Ibrahim (AS):
ﻳﺎ ﺃﺑﺖ ﺇﻧﻲ ﺃﺧﺎﻑ ﺃﻥ ﻳﻤﺴﻚ ﻋﺬﺍﺏ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ…
ﻳﺎ ﺃﺑﺖ … ﻳﺎ ﺃﺑﺖ
– Nuhu (AS):
ﺭﺏ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﻭﻟﻮﺍﻟﺪﻱ ﻭﻟﻤﻦ ﺩﺧﻞ ﺑﻴﺘﻲ ﻣﺆﻣﻨﺎ…
Annabi SAWW ya nuna mana
muhimmancin uwaye da da’arsu a
cikin hadisai da dama:
1. Yardar Allah tana tare da yardar
iyaye:
ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ﺭﺿﺎ ﺍﻟﺮﺏ ﻓﻲ ﺭﺿﺎ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ
ﻭﺳﺨﻄﻪ ﻓﻲ ﺳﺨﻄﻬﻤﺎ ( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻭﺻﺤﺤﻪ
ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ. ﺭﻗﻢ3507 : ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ .
2. Da’ar iyaye na daukaka
matsayin mutum a aljanna:
ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺃﻡ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
) ﺩﺧﻠﺖ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻓﺴﻤﻌﺖ ﻓﻴﻬﺎ ﻗﺮﺍﺀﺓ ﻗﻠﺖ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ ؟
ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ : ﺣﺎﺭﺛﺔ ﺑﻦ ﺍﻟﻨﻌﻤﺎﻥ ( ﻓﻘﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ﻛﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺒﺮ ﻛﺬﻟﻜﻢ ﺍﻟﺒﺮ
] ﻭﻛﺎﻥ ﺃﺑﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺄﻣﻪ ( [
ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ﻭﻭﺍﻓﻪ ﺍﻟﺬﻫﺒﻲ ﻭﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ. ﺭﺍﺟﻊ:
ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺑﺮﻗﻢ 913 ، ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ
ﺑﺮﻗﻢ 3371 ، ﻣﺸﻜﺎﺓ ﺍﻟﻤﺼﺎﺑﻴﺢ ﺑﺮﻗﻢ 4854
3. Da’ar iyaye tana gaba da jihadi
in ba ya zama fardu aini ba.
ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ :
ﺳﺄﻟﺖ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻱ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺃﺣﺐ
ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ؟ ﻗﺎﻝ) : ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻰ ﻭﻗﺘﻬﺎ(
ﻗﺎﻝ: ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ) : ﺑﺮ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ( ﻗﺎﻝ ﺛﻢ ﺃﻱ؟ ﻗﺎﻝ:
) ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ ﻓﻲ ﺳﺒﻴﻞ ﺍﻟﻠﻪ ( ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ــ ﻛﺘﺎﺏ
ﻣﻮﺍﻗﻴﺖ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﺑﺮﻗﻢ 496
4. Uwa tana da wani karin fifiko
saboda karin wahalarta wajen ciki
da nakuda da shayarwa da reno.
ﺭﻭﻯ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ – ﺭﺿﻲ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ – ﺃﻥ ﺭﺟﻼ ﻗﺎﻝ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺃﺣﻖ
ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﺤﺴﻦ ﺻﺤﺎﺑﺘﻲ ؟ ﻗﺎﻝ ” : ﺃﻣﻚ ” ﻗﺎﻝ : ﺛﻢ
ﻣﻦ ؟ ﻗﺎﻝ ” : ﺃﻣﻚ ” ﻗﺎﻝ : ﺛﻢ ﻣﻦ ؟ ﻗﺎﻝ ” : ﺃﻣﻚ ”
ﻗﺎﻝ : ﺛﻢ ﻣﻦ ؟ ﻗﺎﻝ ” : ﺛﻢ ﺃﺑﻮﻙ ” .
Ya ku bayin Allah!
Addinin musulunci ya wajabta
mana kyautata ma iyayenmu a
matsayin wani dan tukuici ga
kokarin da suka yi mana sadda
babu wanda zai yi mana in ba su
ba. Ba a matsayin biyan hakki ba.
Wani mutum ya hadu da sayyidina
Umar a lokacin shi mutumin yana
dauke da mahaifiyarsa yana
dawafi da ita. Sai ya ce ma Umar:
kana ganin ban bata hakkinta ba?
Sai sayyidina Umar ya kalle shi, ya
ce: a lokacin da take daukar ka
fatar take yi ka rayu. A yanzu kai
kuma jira kake yi ta mutu!!
Hakken iyaye bai kadaita kawai ga
iyaye musulmi ba.
ﻓﻌﻦ ﺃﺳﻤﺎﺀ ﺑﻨﺖ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻨﻬﻤﺎ ، ﻗﺎﻟﺖ: ﻗﺪﻣﺖ ﻋﻠﻲ ﺃﻣﻲ ﻭﻫﻲ ﻣﺸﺮﻛﺔ ﻓﻲ
ﻋﻬﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﻓﺎﺳﺘﻔﺘﻴﺖ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﻠﺖ: ﻗﺪﻣﺖ ﻋﻠﻲ
ﺃﻣﻲ ﻭﻫﻲ ﺭﺍﻏﺒﺔ ﺃﻓﺄﺻﻞ ﺃﻣﻲ؟ ﻗﺎﻝ)) :ﻧﻌﻢ، ﺻﻠﻲ
ﺃﻣﻚ(( ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ .
Kai, ba wai zaman su kafirai ba,
koda suna iya kokarinsu don su
kafirtar da kai. Hakken da’a da
kyautatawa gare su yana nan in ji
Allah:
( ﻭﺇﻥ ﺟﺎﻫﺪﺍﻙ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺗﺸﺮﻙ ﺑﻲ ﻣﺎ ﻟﻴﺲ ﻟﻚ ﺑﻪ
ﻋﻠﻢ ﻓﻼ ﺗﻄﻌﻬﻤﺎ ﻭﺻﺎﺣﺒﻬﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻣﻌﺮﻭﻓﺎ
ﻭﺍﺗﺒﻊ ﺳﺒﻴﻞ ﻣﻦ ﺃﻧﺎﺏ ﺇﻟﻲ ﺛﻢ ﺇﻟﻲ ﻣﺮﺟﻌﻜﻢ ﻓﺄﻧﺒﺌﻜﻢ
ﺑﻤﺎ ﻛﻨﺘﻢ ﺗﻌﻤﻠﻮﻥ( ﻟﻘﻤﺎﻥ 15-14
Ya ku al’ummar musulmi! mu gode
ma Allah da ya sa mu cikin inwar
addinin musulunci da
karantarwarsa mikakkiya. Daga
cikin abinda bature ke fama da shi
a yau mai tada hankali akwai
tanadin da kowane mutum yake
bukatar yi a can don tsufansa. Dole
ne mutum ya tara wasu makudan
kudade da zasu amfane shi idan
ya tsufa. Don me? Don babu
wanda zai kula da shi a wannan
lokaci. In ba haka ba kuwa lalle ne
zai kare rayuwarsa a gidan
nakasassu da gajiyayyu wanda
gwamnati ta tanada wanda kuma
ba shi da banbanci da zaman
fursuna a kurkuku. A lokacin
‘ya’yansa maza da mata na can
suna soyayya da abokai da
kawayensu ba wanda ya damu da
shi.
A kasashen turawa akwai kowace
doka har da ta hakken karnuka
amma babu wata doka akan
hakken uwaye. Don me? Don wai
kada a takura ma ‘ya’ya! Za a shiga
cikin ‘yancinsu!!
Musulunci ya banbantar da
‘ya’yansa da irin wannan
karantarwa ta Alkur’ani da Sunnah
da muka gabatar. Wata likita ta
bada labarin biyayya mai ban
mamaki. Tsohuwa ce wawiya da
ba a haife ta ma da hankali ba.
Danta ya zo da ita yana mai
tsananin kula da ita. Ba ya son
kome ya same ta. Saboda
mamakin irin kulawarsa gare ta
wannan likita ta tambaye shi, kuma
ya sanar da ita cewa tun a tashin ta
tana da tabuwar hankali kuma bata
san abinda take yi ba. An aurar da
ita ga mahaifinsa bayan ta samu
cikinsa sai mahaifin ya kasa
hakura da zama da ita. Tashin
hankalin da wannan matar ta shiga
shine, shi wannan ya kula da uwar
da cikinsa kawai ta dauka bata san
wahalarsa kowace iri ba yana ta
tarainiya da ita haka.. To, mu da
iyayenmu suka sha kowace irin
wahala a kanmu ya zamu yi
kenan?!
A cikin tarihin magabata akwai
labarai masu kayatarwa game da
bin wannan umurni na ubangiji.
1. Mis’ar bin Kidam (RH) ya taba
kawo ma mahaifiyarsa ruwa bayan
ta nemi haka amma ko da ya zo ta
yi bacci. Sai ya tsaya har gari ya
waye bai tashe ta ba kuma bai
tafiyarsa ba.
2. Muhammad bin Al-Munkadir ya
ce, na kwana ina murza kafar
mahaifiyata don ta ji dadin bacci,
kanena kuma ya kwana yana
sallah. Ba zan yi fatar ayi mana
musayar lada ni da shi ba.
3. Sayyidina Abu Huraira (RA) ya
ga wani mutum yana tafiya bayan
wani dattijo. Sai ya tambaye shi,
wane ne? Ya ce, mahaifina. Sai ya
ce: kada ka kira shi da sunansa,
kada ka zauna kafin sa, kuma kada
kayi tafiya a gabansa.
Bayan haka ya kai dan uwa
musulmi! Ka sani ba wani laifi a
wurin Allah wanda yake gaggauta
kama mai yinsa, ya debe masa
albarka, ya barkata masa rayuwa
tun a nan duniya kamar cuta ma
iyaye.
Sai ka ga mutum ya damu da
matarsa, ya kula da ‘ya’yansa
amma bai ko san halin da
mahaifiyarsa take ciki ba. Wani
kuma yana cikin ni’ima da jin dadin
duniya iri-iri amma yana nan birni
yana ma-sha’a mahaifinsa ko na
can kauye yana fama da nikar gero
da dawa. Ko ka tarar da ya gina
babban gida, yana hawan manyan
ababen hawa amma mahaifiyarsa
na cikin rubabben wuri kuma N100
suna ba ta shawa.
Mu gyara ya ku al’ummar musulmi.
Ga wasu shawarwari guda (20),
duk mutumin da Allah ya albarkace
shi da rayuwa tare da dayan
mahaifansa ko dukansu ya kamata
ya rike su:
1. Ka yi masu biyayya da da’a ga
duk abinda suke so in bai saba ma
Allah ba. Kuma duk abinda kake
idan sun kira ka ka karba.
2. Ka nisanci duk abinda zai
husata su ko ya tunzura su
3. Ka tsare mutuncinsu da
girmansu a idon jama’a.
4. Yi kokari kayi duk abinda ka san
yana faranta ransu koda ba su sa
ka ba.
5. Ka karba kiransu cikin
murmushi, ka je zuwa aikin da
suka sa ka cikin nashadi.
6. Kada ka yi jayayya da su koda a
cikin maganarsu ba su da gaskiya.
A maimakon haka ka samu wani
lokaci daban na lurar da su
kuskurensu a cikin ladabi da
hikima.
7. Ka saurare su idan suna
magana kuma kada ka daga musu
murya.
8. Ka tanye su aiki koda ba su
neme ka ba.
9. Idan dayansu ba shi da lafiya ka
himmatu wajen jinyarsa da kanka.
Kome kake yi ka tabbata ka ware
masu lokaci a cikin wannan hali.
Kada ka ce aiki ya yi min yawa. Ka
kaddara ciwon a kanka ne ya fada.
Zaka ba shi lokaci ko shagali zai
dauke ka?!
10. Bayyana ladabi gare su ko a
wurin zama ko wurin tafiya. Kada
ka saki jiki ko ka mike kafafu ko ka
haura sama da su ko ka yi tafiya
gabansu ta yadda zasu ji lalle ba
su da wani matsayi na girmamawa
gurin ka.
11. Kada ka taba damuwa ko jin
ciwon bayyana cewa uwayenka
ne. Kayi alfahari da su koda ba su
da wata daukaka wadda ake kuri
da ita.
12. Kada ka bari bukata ta kama su
har su kai ga rokonka. Ka wadata
su gwargwado da abinda zasu ji
dadin rayuwa har su taimaki wani
matukar kana da iko.
13. Nuna kulawa da su ta fuskar
ziyara koda a wuri daya kuke. Idan
kuma ba a wuri daya kuke ba to ka
ware wani lokaci da zaka rinka
tuntubar su, kana ziyartar su, kana
samun lokacin fira da su, kana
sauraren kokensu da biyan
bukatarsu.
14. Rinka nuna masu godiya, da
cewa duk abinda ka yi masu ba ka
biya su ba a kan renonka da suka
yi. Allah Ta’ala ya ce:
(( ﺃﻥ ﺍﺷﻜﺮ ﻟﻲ ﻭﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻚ ﺇﻟﻲ ﺍﻟﻤﺼﻴﺮ(( ﻟﻘﻤﺎﻥ14:
15. Kada ka bukace su da abinda
ba su son ba ka. Idan kuma sun ba
ka kayi godiya kamar ba a taba ba
ka abinda ka ji dadi kamar nasu
ba.
16. Kada ka fifita iyalanka ko
‘ya’yanka a kan su.
17. ka boye masu mafi yawan
kyautatawar da ke tsakaninka da
iyalanka domin gudun shedan ya
sa masu kishi a kan wannan.
18. Idan rashin jituwa ta shiga
tsakanin su da iyalinka kada ka
taba goyon bayan iyalinka a fili
koda su ke da gaskiya. Sai dai ka
lurar da su a asirce cewa, suna da
gaskiya amma matsayin mahaifa
abu ne ba na wasa ba.
19. Rinka neman addua a gurinsu
kana fada masu bukatunka tare da
sanar da su cewa, addu’arsu ta fi
ta kowa kima da saurin karbuwa a
wurin Allah.
ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ﻗﺎﻝ: ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ
ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ” : ﺛﻼﺙ ﺩﻋﻮﺍﺕ ﻣﺴﺘﺠﺎﺑﺎﺕ
ﻟﻬﻦ، ﻻ ﺷﻚ ﻓﻴﻬﻦ، ﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻤﻈﻠﻮﻡ، ﻭﺩﻋﻮﺓ
ﺍﻟﻤﺴﺎﻓﺮ، ﻭﺩﻋﻮﺓ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ ﻋﻠﻰ ﻭﻟﺪﻳﻬﻤﺎ .”
20. Kada ka taba yarda ka ja ma
su zagi. Annabi SAWW yana cewa:
“Yana daga cikin mafi girman
kaba’irai mutum ya la’anci
iyayensa. Aka ce, ya manzon
Allah! Ya haka zata faru? Ya ce,
zai zagi uban wani sai a zagi nasa.
Ko ya zagi uwar wani sai a zagi
tasa”.
Bayan haka. Ya kai wanda Allah
bai nufe shi da rayuwa da uwa ko
uba ba. Ko kuma ka riga ka yi
sakaci har sun wuce ba ka ba su
hakkensu ba. Kada ka samu
damuwa. Ko yanzu akwai yadda
zaka yi:
1. Yawaita yin addu’a gare su da
neman gafarar Allah. Babu laifi ka
yi sadaka don neman masu gafara
da sassauci daga ubangiji. Haka
kuma ya halalta ka ziyarci
kabarinsu don kayi masu addu’a ta
fatar samun dausayi a cikin
kabarinsu.
2. Ka zartar da duk wani abinda
suka yi wasici da shi. Idan babu ka
duba abinda suke sha’awa da duk
wani abin da ka san suna jin dadin
aikata shi na alheri musamman
wanda ya shafi kyautata ma
mutane, sai ka aikata shi.
3. Ka sada zumunci da yan
uwansu da danginsu da
masoyansu, kuma ka bi su gaba
daya da kyautatawa.
Daga karshe..
Ka sani, duk yadda ka yi haka za
ayi ma. “Kama tadinu tudanu..”
Uwaye kuma zasu iya taimakon
dansu wajen yi masu da’a idan
suna lallabawa da shi, suna
tausaya masa, suna sa masa
albarka. Kuma babu shakka
addu’ar iyaye tana da babban tasiri
ga shiriyar ‘ya’ya da sa suyi
albarka wadda iyayen su ne farkon
masu cin moriyarta.
Allah ya yi mana albarka. Ya
gafarta ma iyayenmu da suka riga
mu. Wadanda muke tare da su
Allah ya bamu ikon yin biyayya da
kyautatawa gare su. Allah ya yi ma
‘ya’yanmu albarka, ya sa su zama
masu biyayya gare mu.
ﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﻠﻪ،
)-ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﻠﺎﺋﻜـﺘﻪ ﻳﺼﻠﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﺻﻠﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳـﻠﻤﻮﺍ ﺗﺴـﻠﻴﻤﺎ-(
]ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ .[56/
ﻭﺃﻛﺜﺮﻭﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻳﻌﻈﻢ ﻟﻜﻢ ﺭﺑﻜﻢ ﺑﻬﺎ
ﺃﺟـﺮﺍ. ﻓﻘﺪ ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳـﻠﻢ » :ﻣﻦ ﺻﻠﻰ
ﻋﻠﻰ ﺻﻼﺓ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﺑﻬﺎ ﻋﺸـﺮﺍ .«
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞ ﻭﺳـﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳـﻮﻟﻚ
ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤـﻤﺪ ﺻﺎﺣﺐ ﺍﻟﻮﺟـﻪ ﺍﻷﻧﻮﺭ ﻭﺍﻟﺠﺒﻴﻦ
ﺍﻷﺯﻫﺮ، ﻭﺍﺭﺽ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﻦ ﺍﻷﺭﺑﻌﺔ ﺍﻟﺨـﻠﻔﺎﺀ ﺃﺑﻲ
ﺑﻜـﺮ ﻭﻋـﻤﺮ ﻭﻋـﺜﻤﺎﻥ ﻭﻋـﻠﻲ ﻭﻋﻦ ﺳـﺎﺋﺮ
ﺃﺻﺤـﺎﺏ ﻧﺒﻴﻚ ﺃﺟﻤـﻌﻴﻦ، ﻭﻋﻦ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻭﻣﻦ
ﺗﺒﻌﻬﻢ ﺑﺈﺣـﺴﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻭﻋﻨﺎ ﻣﻌﻬﻢ ﺑﻌﻔﻮﻙ
ﻭﻣﻨﻚ ﻭﻛﺮﻣﻚ ﻭﺇﺣـﺴﺎﻧﻚ ﻳﺎ ﺃﺭﺣﻢ ﺍﻟﺮﺍﺣﻤـﻴﻦ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﻋﺰ ﺍﻹﺳـﻼﻡ ﻭﺍﻟﻤﺴـﻠﻤﻴﻦ، ﻭﺃﺫﻝ ﺍﻟﺸـﺮﻙ
ﻭﺍﻟﻤﺸـﺮﻛﻴﻦ، ﻭﺩﻣﺮ ﺃﻋﺪﺍﺋﻚ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻭﺍﻧﺼﺮ
ﻋﺒﺎﺩﻙ ﺍﻟﻤﻮﺣـﺪﻳﻦ، ﻭﺍﺣﻤﻲ ﺣـﻮﺯﺓ ﺍﻟﺪﻳﻦ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﺎ ﻧﻌﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺭﻯ
ﻭﺍﻟﺮﺍﻓﻀﺔ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﺎ ﻧﻌﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭﻫﻢ ﻭﻧﺪﺭﺃ
ﺑﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻓﻲ ﻧﺤـﻮﺭﻫﻢ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺁﻣﻨﺎ ﻓﻲ ﺩﻭﺭﻧﺎ ﻭﺃﻭﻃﺎﻧﻨﺎ ﻭﺃﺻﻠﺢ ﻭﻭﻓﻖ ﻭﻻﺓ
ﺃﻣﻮﺭﻧﺎ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺃﺻﻠﺢ ﻗﻠﻮﺑﻬﻢ ﻭﺃﻋﻤﺎﻟﻬﻢ ﻭﺳـﺪﺩﻫﻢ
ﻓﻲ ﺃﻗﻮﺍﻟﻬﻢ ﻭﺃﻓﻌﺎﻟﻬﻢ، ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺷﻤـﻠﻬﻢ ﻭﺷﻤـﻞ
ﺍﻟﻤﺴـﻠﻤﻴﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻳﺎ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ .
ﺭﺑﻨﺎ ﺁﺗﻨﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﺣـﺴﻨﺔ ﻭﻓﻲ ﺁﺧـﺮﺓ ﺣـﺴﻨﺔ ﻭﻗﻨﺎ
ﻋﺬﺍﺏ ﺍﻟﻨﺎﺭ .
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏـﻔﺮ ﻟﻨﺎ، ﻭﻵﺑﺎﺋﻨﺎ ﻭﻷﻣﻬﺎﺗﻨﺎ، ﻭﻷﻭﻻﺩﻧﺎ
ﻭﻷﺯﻭﺍﺟـﻨﺎ، ﻭﻟﺠـﻤﻴﻊ ﺍﻟﻤﺴـﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺴـﻠﻤﺎﺕ،
ﻭﺍﻟﻤﺆﻣﻨـﻴﻦ ﻭﺍﻟﻤﺆﻣﻨﺎﺕ ﺍﻷﺣـﻴﺎﺀ ﻣﻨﻬﻢ ﻭﺍﻷﻣﻮﺍﺕ.
)-ﺳـﺒﺤﺎﻥ ﺭﺑﻚ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺰﺓ ﻋﻤﺎ ﻳﺼﻔﻮﻥ (180)
ﻭﺳـﻠﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠـﻴﻦ(181)ﻭﺍﻟﺤـﻢﺩ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ
ﺍﻟﻌﺎﻟﻤـﻴﻦ] -(ﺍﻟﺼﺎﻓﺎﺕ182-180/ ].
Leave a Reply