HUDUBA DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (R.A)(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A yau jum’ah 24/2/1435H na’ibi na 2 Sheikh Idris Garba ne ya jagoranci sallah a wannan masallaci bayan yayi huduba wadda ya mayar da karfi a cikinta wajen bayanin himmar sahabban manzon Allah (S) wajen kula da alkurani ta fuskar karatunsa da koyar da shi da zakulo asirrai da ilmummukan da ke cikin sa.
Manzon Allah (S) yana da marubuta daga cikin sahabbai wadanda yawansu ya kai 44.
Masallacin manzon Allah shi ne makarantar hardar kurani ta farko. A nan ne kuma aka yaye mahardata irin su Ubayyu bn Ka’ab da Ibn Mas’ud. Su ne aka yi hasarar 70 a cikin su a bi’ir ma’una. Ko bayan wafatin manzon Allah a yakin Yamama zamanin Abubakar an sake hasarar mahardata 70 abinda ya jawo aka tattara kur’ani daga hannayen mutane aka mayar da shi littafi. A zamanin halifancin Usman ne aka buga alkur’ani bugun farko ta hanyar wallafa kofi kofi nasa aka rarraba shi a wurare.
Saboda sanin girman kur’ani sahabbai sukan yi sadaki da karatunsa.
Sahabbai sune suka fara buda makarantun alkur’ani a Makka da Madina da Kufa da sauran garuruwa.
Daga cikin abinda ya taimaki sahabbai wajen rike kur’ani akwai kiyamullaili wanda ba ka iya samun wani sahabi da ba ya kashe dare yana yin sa.
A lokacin da yan Shi’a suka fara rade-radin an ba iyalan annabi wani kur’ani na musamman Abu Juhaifa ya tambayi sayyidina Ali ko an kebe ku da wani abu na wahayi daban da mutane? Sai ya ce masa a’a. Sai dai fahimtar da Allah yake ba mutum game da alkur’ani da kuma takardar bayanin diyya.
Bayan kammala sallar jumah mun wuce darud da’awa inda muka daura auren limamin namu da yar gidan abokinmu Alh. Muhtari Kamba. Allah ya sa albarka ya ba da zuria dayyiba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories