Bayan godiya da fadanci mai
kyawo mai dadi ga madaukakin
sarki, limamin ya yi kira ga
musulmi mu ji tsoron Allah, ya
tsoratar dangane da duniya da
rudinta. Ya karanto ayoyin alkur’ani
masu nuna muhimmancin tsoron
Allah da kasancewarsa shine
babban guzuri ga musulmi.
Kasancewr wannan huduba ita ce
ta karshe a wannan shekara,
limamin ya mayar da hankali ga
lura da tafiyar lokaci da wucewar
zamani. Ya karanto hadisin “ka
kasance a cikin duniya kamar bako
ko mai tsallake hanya”.
Dole ne musulmi ya wa kansa
hisabi, ya duba yawan zunubbansa
da yawan gafalarsa. Sau nawa ne
santsi ya ja ka zuwa ga sabo? Sau
nawa ne ka gafala ka ci amanar
mutane? Me kake jira wanda yake
hana ka tuba? “Ranar da kowace
rai za ta ga abinda ta aikata na
alheri an halarto da shi. Haka ma
abinda ta aikata na sharri, tana
gurin ina ma za a sanya shamaki
mai nisa tsakanin ta da shi”.
Mai hankali – ya ku yan uwa – shine
wanda ya lura da tambayoyin da
Allah zai yi masa a ranar alkiyama.
Tambayoyi ne guda hudu annabi
(S) ya ba mu labarin su.
1. Ya ka yi rayuwarka?
2. Ya ka karar da kuruciyarka?
3. A ina ka samo dukiyarka? Kuma
a ina ka karar da ita?
4. Ilminka ko ka yi aiki da shi?
Ya ku bayin Allah!
Akidarmu ita ce jarinmu. Babu
wani dalilin da zai sa mu kauce
daga gare ta. Addininmu addini ne
da yake kira zuwa ga haduwa da
samar da yanci da hana zubar da
jini. Duniyar yau tana bukatar mu
karantar da ita shiriyar addininmu.
Rashin kafuwar akidar musulunci
shi ne musabbabin duk fitinu da
bala’oin da duniya take ciki na
yakoki da talauci da tsarwatsewar
jama’a…
Kada ku yanke kauna daga
rahamar Allah don ganin halin da
kuke ciki. Ku sani taimakon Allah
yana nan tafe. Amma sharadin
guda daya ne.. Mu taimaki Allah.
Ya ku yan uwanmu a kasar
Falastin.. Ya ku yan uwanmu na
Syria.. Ya ku jama’ar musulmin
Burma.. Ya ku musulmin da ke
cikin wahala a ko ina a duniya..
Daga kan wannan mimbari mai
alfarma muna ba ku albishir cewa,
taimakon Allah yana nan tafe zuwa
gare ku. Kuma mu yan uwanku a
ko ina a duniya muna tare da ku.
A cikin hudubarsa ta biyu Sheikh
Sudais ya maimaita muhimmancin
kula da karewar rayuwa ta hanyar
karewar shekaru. Sannan ya
tunatar da musulmi dangane da
hijira da muhimman darussan da
ke cikin ta. Ya ce wallahi
darussanta darussa ne masu
girma.
Hijira ta karantar da mu cewa, dole
ne mu kyautata ma Allah zato. Mu
yi hakuri da duk halin da muka
shiga mu tabbatar taimakonsa
yana nan tafe. Duba yadda Siddiku
yake ce ma manzon Allah (S) in da
mushrikai sun duba karkashin
kafafunsu da sun gan mu. (S) yake
ce ma sa “me zaka ce ga mutane
biyun da Allah ne na ukunsu?”
Allah yana tare da masu gaskiya a
duk inda suke. Taimakonsa ba shi
yankewa daga gare su.
Liman ya rufe hudubarsa da
adduoi masu kyau ga al’ummar
musulunci baki daya.
Allah ya karbi abinda liman ya
roka.
Leave a Reply