Ina Kadiradawa? Ga sako na musamman zuwa gare ku(Dr Mansur Sokkoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ina Kadiradawa? Ga sako na musamman zuwa gare ku:
قال سيدي أبو صالح عبد القادر بن موسى بن عبد الله بن يحيى الزاهد بن محمد بن داود بن موسى الجون بن عبد الله المحضى بن الحسن المثنى بن الحسن بن علي بن أبي طالب رضي الله تعالى عنهم أجمعين في كتابه “الغنية لطالبي طريق الحق”:
واتفق أهل السنة على وجوب الكف عما شجر بينهم، والإمساك عن مساويهم، وإظهار محاسنهم وفضائلهم، وتسليم أمرهم إلى الله عز وجل على ما كان وجرى من اختلاف علي وطلحة والزبير وعائشة ومعاوية رضي الله عنهم على ما قدمنا بيانه، وإعطاء كل ذي فضل فضله، كما قال الله عز وجل:
((والذين جاؤوا من بعدهم يقولون ربنا اغفر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان، ولا تجعل في قلوبنا غلا للذين آمنوا، ربنا إنك رؤوف رحيم)).
وقال تعالى:
((تلك أمة قد خلت، لها ما كسبت ولكم ما كسبتم، ولا تسألون عما كانوا يعملون)).
وقال صلى الله عليه وسلم: “إذا ذكر أصحابي فأمسكوا”.
وفي لفظ: “إياكم وما شجر بين أصحابي، فلو أنفق أحدكم مثل أحد ذهبا ما بلغ مد أحدهم ولا نصيفه”
وسرد أحاديث كثيرة في فضائلهم.
انظر كتاب “الغنية لطالبي طريق الحق” ط. شركة مكتبة مطبعة مصطفى البابي الحلبي وأولاده بمصر، ص ٧٩
Sayyidi Abdulqadir Aljailani jikan sayyidi Al-Hasan dan Ali dan abu Talib yardar Allah ta tabbata a gare su ya fada a cikin littafinsa “Al-Gunya Li Talibi Tariq Al-Haqq” (ma’anar sunan littafin JAGORAN MASU NEMAN GASKIYA”. Ga abin da ya ce:
“Kuma Ahlus Sunnah sun hadu a kan wajabcin kamewa daga abin da ya gudana a tsakanin su, da barin fadin kurakuransu, da bayyana kyawawan ayyukansu da darajojinsu, da barin lamarinsu ga Allah madaukakin sarki, tare da duk abin da ya faru a tsakaninsu na sabani tsakanin Ali da Dalha da Zubair da Nana A’isha da Mu’awiyah, yardar Allah ta tabbata a gare su gaba daya bisa bayanin da muka gabatar. Kuma wajibi ne a bai wa kowane mai girma girmansa kamar yadda Allah buwayayyen sarki ya ce:
“Kuma wadanda suka zo bayan su suna cewa, ya Ubangijinmu! Ka yi gafara gare mu da kuma ga wadanda suka riga mu yin imani, kuma kada ka sanya jin haushi a cikin zukatanmu ga wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Hakika kai mai jinkai ne, mai tausayi”
Kuma ya ce:
“Waccan al’umma ce da ta shude, abin da suka aikata nasu ne, wanda kuka aikata ku ma naku ne, kuma ba za a tambaye ku game da abin da suka kasance suna aikatawa ba”.p
Kuma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Idan aka ambaci sahabbaina ku kame bakinku”.
A wani lafazin cewa ya yi: “Ku yi hattara da fadin abin da ya gudana tsakanin sahabbaina, domin da dayanku ya yi sadakar kimanin dutsen Uhud na zinari ba zai kai mudun dayansu ko rabinsa ba”.
Sannan ya ci gaba da kawo hadisai masu tarin yawa a kan darajojinsu.
Duba littafinsa: “Al-Gunya Li Talibi Tariq Al-Haqq”, bugun Kamfanin mustafa Al-Babi na kasar Masar, shafi na 79.
Ya Allah ka isar da rahamarka da jinkayinka da kyautatawarka zuwa ga kabarin sayyidi Abdulqadir Al-Jailani, ka yi jagora ga mabiyansa zuwa ga hanyar gaskiya.
Daga karshen karatunmu na ALKAKI da zai zo a yammacin yau in Allah ya so

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Ina Kadiradawa? Ga sako na musamman zuwa gare ku(Dr Mansur Sokkoto)”
  1. Umar Adamu faskari Avatar
    Umar Adamu faskari

    Allah yasaka da alkhairi

Leave a Reply

Categories
Latest updates