Mafificin Sigar Salatin Annabi

Danna nan domin shiga karatu Online

Allah maɗaukakin sarki yace:

Allah da Mala’ikunsa suna yi wa Annabi Salati, yaku Wa’inda kukayi Imani kuyi Masa Salati

Surat Ahzab ayah 56

Sahabban Annabi sun Tambayeshi kan yadda ya kamata suyi masa Salati sai ya koyar dasu kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta 6357 da Muslim a hadisi mai lamba ta 406

خرَجَ علينا رسولُ اللهِ صلَّى اللَّهُ علَيهِ وسلَّمَ، فقلنا: قد عَرَفْنَا كيف نُسَلِّمُ عليك، فكيف نُصَلِّي عليك؟ قال: قولوا: اللهمَّ، صلِّ على محمدٍ وعلى آلِ محمدٍ، كما صلَّيْتَ على آلِ إبراهيمَ إنك حميدٌ مجيدٌ، اللهمَّ، بارِكْ على محمدٍ وعلى آلِ محمدٍ، كما بارَكْتَ على آلِ إبراهيمَ إنك حميدٌ مجيدٌ.

Manzon Allah ya fito zuwa garemu sai mukace masa: Munsan yadda zamuyi maka Sallama, toh Yaya zamuyi maka salati? Sai Annabi yace kuce:”Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Ala Aali Muhammadin kama sallaita Ala Ibrahim innaKa Hamidun Majid, Allahumma Barik Ala Muhammadin wa Ala Aali Muhammadin kama barakta Ala Aali Ibrahim innaka hamidun majid.

Wannan Sigah ta Salati da ƴan’uwansa wanda ake kira Salatul Ibrahimiyyah sune wanda Annabi ya koyar, kuma shine mafificin Salati aban ƙasa. Duk wani nau’i na salati wanda ba shi ba toh bai kaishi falala ba.

Wata sigar Salatin Ibrahimiyyah:

اللهمَّ صلِّ على محمَّد ، وأزواجِه ، وذُريَّتِه ، كما صليتَ على آل إبراهيم

وبارِك على محمَّد ، وأزواجِه ، وذُريَّتِه ، كما باركتَ على آل إبراهيم ؛ إنَّك حميدٌ مجي

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates