MAULUDI BA ADDINI BANE!!! BID'AH CE

Danna nan domin shiga karatu Online

ASALIN MAULIDI DA WA’DANDA SUKA K’IRK’IRE SHI!!
MAGABATAN WANNAR AL’UMMA BA SU YI MAULIDI BA:
KAMAR YADDA KOWA YA SANI, K’ARNUKAN DA MANZON ALLAH (SAW) YA YABESU; WATO K’ARNI NA FARKO DA NA 2 DA NA 3. SUN GABATA, AMMA LITTATAFAN TARIHI BA SU KIYAYE MANA CEWA AN SAMU WANI DAGA CIKIN SAHABBAI KO TABI’AI KO MABIYA TABI’AI, DA MA WA’DANDA SUKA ZO A BAYANSU DA YA YI MAULIDIN ANNABI (SAW) BA. DUK TSANANIN SOYAYYARSU GARE SHI. KUMA DUK DA CEWA; SUN FI KOWA ILMI, WATO SANIN ADDININ MUSLUNCI, KUMA DUK DA CEWA; SUN FI KOWA KWA’DAYIN BIN SHARI’AR ANNABI (SAW).
FARKON WANDA YA K’IRK’IRI MAULIDIN ANNABI (SAW):
FARKON WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI SU NE BANU UBAID AL- K’ADDAH, WA’DANDA SUKE KIRAN KANSU DA ”FA’DIMIYYUNA’ ‘ MA’ANA JIKANUN FATIMA (RA). SABODA SUNA DANGANTA KANSU ZUWA GA ZURIYYAR ALIYU (RA). ALHALI A HAK’IK’ANIN GASKIYA WA’DANNAN MUTANE SU NE SUKA ASSASA ”DA’AWAR BA’DINIYYA”. WATO ‘YAN BA’DINIYYA MASU CEWA; ADDINI YANA DA ZAHIRI YANA DA BA’DINI, KUMA -WAI- SU NE SUKA SAN BA’DININ NASA. ASALIN KAKANSU SHI NE IBNU DISAN, WANDA AKA FI SANI DA ”AL- K’ADDAH”. YA KASANCE MAULA NE NA JA’AFARUS SADIK’. WATO ‘YANTACCEN BAWANSA. KUMA ‘DAN ASALIN GARIN ”AHWAZ” NE. ‘DAYA DAGA CIKIN WA’DANDA SUKA ASSASA MAZHABAR ”BA’DINIYYA” A IRAK’I. SA’ANNAN SAI YA YI K’AURA ZUWA MAGRIB. TO A WANCAN YANKIN NE YA DANGANTA KANSA ZUWA GA AK’ILU ‘DAN ABI ‘DALIB, YA RAYA CEWA; SHI DAGA TSATSONSA YAKE. TO A LOKACIN DA RAFIDA MASU GULUWI SUKA AMSA DA’AWARSA , SAI YA YI DA’AWAR CEWA; -WAI- SHI ZURIYYAN MUH’D BIN ISMA’IL BIN JA’AFAR AL- SADIK’ NE. KAWAI SAI SUKA YARDA DA HAKAN. DUK DA CEWA; SHI MUH’D BIN ISMA’IL YA MUTU BAI BAR ‘DA BA. DAGA CIKIN WA’DANDA SUKA BI SHI AKWAI HAMDAN K’URMU’D, WANDA ”K’ARAMI’DA” SUKE DANGATUWA GARE SHI. DA ZAMANI YA YI NISA SAI SA’ID BIN HUSAINI BIN AHMAD BIN ABDULLAH BIN MAIMUN BIN DISAN YA BAYYANA, SAI YA CANZA SUNANSA DA NASABARSA. SAI YA CE WA MABIYANSA: NI NE UBAIDULLAHI BIN HASAN BIN MUH’D BIN ISMA’ILA BIN JA’AFAR AL- SADIK’. TO HAKA SAI FITINARSA TA BAYYANA A MAGRIB.
DON K’ARIN BAYANI AKAN WANNAN BAYANI, DUBA WAFIYYATUL A’AYAN 3/ 118. ALBIDAYA WAN NIHAYA 11/ 202, FABHA’IHUL BA’DINIYYA SHAFI NA 11,6, ALFARK’U BAINAL FIRAK’ NA BAGDADIY SHAFI NA 266 – 267.
KHALIFOFIN DAULAR RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA TA FA’DIMIYYA DA KE MISRA NE SUKA FARA DUKKANNIN MAULIDI:
DON HAKA FARKO WA’DANDA SUKA FARA MAULIDI SU NE RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA WA’DANDA SUKA YI NUFIN CANZA WA MUSULMAI ADDININSU, TA HANYAR SHIGAR DA ABIN DA BA YA CIKINSA. UBAIDIYYUNA SUN SHIGA MISRA NE A SHEKARA TA 362 TA HIJIRA, A RANAR 5 GA RAMADAN, WANNAN NE FARKON LOKACIN DA SUKA FARA MULKINSU A MISRA. WASU SUN CE: RANAR 7 NE GA RAMADAN ‘DIN. TO DUKKANNIN MAULIDI NA ANNABI (SAW) DA NA WANINSA, WA’DANNAN MUTANE UBAIDIYYUNA NE SUKA FARASU. BABU WANDA YA TA’BA YIN MAULIDI KAFINSU. AL- MIK’RIZIY YA CE:
(ذكر الأيام التي كان الخلفاء الفاطميون يتخذونها أعيادا ومواسم تتسع بها أحوال الرعية ، وتكثر نعمهم. وكان للخلفاء الفاطميين في طول السنة أعياد ومواسم وهي: موسم رأس السنة، وموسم أول العام، ويوم عاشوراء، ومولد النبي صلى الله عليه وسلم، ومولد علي بن أبي طالب – رضي الله عنه – ومولد الحسن، ومولد الحسين عليهما السلام ، ومولد فاطمة الزهراء عليها السلام ، ومولد الخليفة الحاضر ، وليلة أول رجب ، وليلة نصفه ، وليلة أول شعبان ، وليلة نصفه ، وموسم ليلة رمضان ، وغرة رمضان ، وسماط رمضان ، وليلة الختم ، وموسم عيد الفطر ، وموسم عيد النحر ، وعيد الغدير ،وكسوة الشتاء ، وكسوة الصيف ، وموسم فتح الخليج ، ويوم النوروز ، ويوم الغطاس ، ويوم الميلاد ، وخميس العدس ، وأيام الركوبات..)
YA CE: AMBATON KWANAKIN DA KHALIFOFIN FA’DIMIYYA SUKA RIK’A A MATSAYIN RANAKUN IDI, DA RANAKUN TARO. WA’DANDA AKE YALWATAWA TALAKAWA DA YAWAITA MUSU NI’IMOMI. YA KASANCE KHALIFOFIN FA’DIMIYYA SUNA DA RANAKUN IDI DA NA TARO A TSAWON SHEKARA, GA SU KAMAR HAKA: BIKIN DAREN FARKON SHEKARA, BIKIN RANAR FARKON SHEKARA, RANAR ASHURA, RANAR HAIFUWAR ANNABI (SAW), RANAR HAIFUWAR ALIYU (RA), DA RANAR HAFUWAR HASAN (RA) DA RANAR HAFUWAR HUSAINI (RA). DA RANAR HAIFUWAR FATIMA AL- ZAHARA’U (RA), DA RANAR HAIFUWAR KHALIFA MAI CI A LOKACIN, DA IDIN DAREN RAJAB, DA DAREN TSAKIYAR RAJAB, DA DAREN FARKON SHA’ABAN, DA TSAKIYAN SHA’ABAN, DA BIKIN DAREN RAMADAN, DA NA RANAR KAMUWAN WATAN RAMADAN, DA DAREN KHATMAN K’UR’ANI NA K’ARSHEN RAMADAN, DA TARON IDIN SALLAR AZUMI, DA NA IDIN LAYYAH, DA IDIN GADEER, DA … DA IDIN NAIRUZ…
SA’ANNAN SAI AL- MAK’RIZIY YA ‘DAUKESU ‘DAYA BAYAN ‘DAYA YANA BAYANIN YADDA SUKE YINSU. DUBA AL- KHI’DA’DUL MIK’RIZIYYA 1/ 490.
YANAYIN MULKIN KHALIFOFIN RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA TA DAULAR FA’DIMIYYA, WA’DANDA SUKA K’IK’IRI MAULIDI:
SARAKUNAN DAULAR FA’DIMIYYA TA RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA SUN FISKANTAR DA SIYASARSU CE ZUWA GA MANUFA GUDA ‘DAYA, ITA CE: YIN DUKKAN IYA K’OK’ARINSU NA TILASTAWA WA MUTANE AKAN SU BI ADDININSU NA RAFIDANCIN BA’DINIYYA, DA SANYA SHI YA ZAMA SHI NE JA GABA A DUKKAN GARURUWAN MISRA, DA MA SAURAN GARURUWAN DA SUKE YI MATA MULKI. DA MAK’OBTA. SARAKUNAN WANNAR DAULA SUN YI MATUK’AR MU’AMALA DA YAHUDAWA DA NASARA, TA YADDA SUN NUNA MUSU SOYAYYA SOSAI, SUN BA SU MUK’AMAI MASU GIRMA A CIKIN WANNAR DAUALA.
DUBA ALBIDAYA WAN NIHAYA 11/ 358, AL- MUNTAZIM 7/ 190, ITTI’AZUL HUNAFA 1/ 297. AL- DAULAR FA’DIMIYYA SHAFI NA 202.
HAK’IK’A AL- UBAIDIYYUNA RAFIDA ‘YAN BA’DINIYYA SARAKUNAN DAULAR FA’DIMIYYA, SUN KAI MATUK’A WAJEN YA’DA TSINUWA WA KHALIFOFIN ANNABI (SAW) GUDA 3; ABUBAKAR (RA), UMAR (RA), USMAN (RA). DA MA SAURAN SAHABBAI. SABODA SUNA K’IRGASU A CIKIN MAK’IYA ALIYU (RA). TARE DA WATSA FALALOLIN ALIYU (RA) DA ‘YA’YANSA TA HANYAR ZANAWA A JIKIN MANYAN K’ARAFUNA DA RUBUTAWA A JIKIN KATANGUN MASALLATAI. KUMA MASU HU’DUBA SUN KASANCE SUNA TSINE MA SAHABBAI AKAN DUKKANNIN MINBARORIN K’ASAR MISRA GABA ‘DAYA. HAK’IK’A RAFIDA UBAIDIYYUNA, SUN TILASTA WA DUKKAN MA’AIKATANSU ‘YAN MISRA, DA SU RUNGUMI ADDININSU NA RAFIDANCIN BA’DINIYYA, KAMAR YADDA SUKA WAJABTA WA ALK’ALAI SU ZARTAR DA HUKUNCE – HUKUNCE A BISA DOKOKIN WANNAN ADDINI NASU. KAI, HAR YA KAI GA CEWA; SHARA’DI NE NA SAMUN MATSAYI A DAULAR, SAI MUTUM YA JUYA YA KOMA ADDININ RAFIDANCIN BA’DINIYYA. WANDA HAKAN YA SA DA YAWA DAGA CIKIN KAFIRAN AMANA SUN NUNA SHIGA MUSLUNCI TARE DA RUNGUMAR RAFIDANCI.
DUBA AL- DAULAR FA’DIMIYYA SHAFI NA 218.
WA’DANNAN MUTANE ‘YAN SHI’A BA’DINIYYA, WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI, YANA DAGA CIKIN GABARSU DA SUNNAR ANNABI (SAW), DA AHLINTA; AZEEZ SARKIN LOKACIN YA YI UMURNI DA A DENA SALLAR TARAWIHI A DUKKAN K’ASAR MASAR. WATO A SHEKARA TA 372. SA’ANNAN A SHEKARA 393 AN KAMA WASU MUTANE 13, AKA YI MUSU DUKA, SA’ANNAN AKA YI YAWO DA SU AKAN RAK’UMA A CIKIN GARI. AKA TSARESU TSAWON KWANA 3. DUK WANNAN SABODA KAWAI SUN YI SALLAR WALAHA. A SHEKARA 381, AN YI DUKA MA WANI MUTUM AKA ZAGA GARI DA SHI, SABODA KAWAI AN SAMU LITTAFIN ”MUWA’D’DA’A” TA IMAMU MALIK (R) A WAJENSA.
TSANANIN GABAR UBAIDIYYUNA (RAFIDA BA’DINIYYA) WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI GA SAHABBAI DA AHLUS SUNNA:
A SHEKARA TA 395H A CIKIN WATAN SAFAR, AN RUBUTA ZAGIN MAGABATA (SAHABBAI) DA TSINE MUSU A BABBAN MASALLACIN MISRA ”JAMI’UL ATIK”’ DA MA SAURAN MASALLATAN, TA CIKI DA WAJENSU, DA TA DUKKAN GEFE – DA – GEFENSU, DA K’OFOFIN SHAGUNA DA MAK’ABARTU. AKA ZANA SHI DA ZINARI. HAKA AKA YI A K’OFOFIN GIDAJE DA NA MANYAN ‘DAKUNAN TARO. KUMA AKA TILASTA MUTANE AKAN YIN HAKAN. TSINE MA AHLUS SUNNA ABU NE DA YA WATSU A BAKUNAN MUTANE, AKAN MINBARORI A DUKKAN FA’DIN MASAR TSAWON MULKIN UBAIDIYYUNA. HAR TA KAI GA SHI ABHID – SARKINSU NA K’ARSHE- SABODA TSANANIN SHI’ANCINSA, DA GULUWWINSA WAJEN ZAGIN SAHABBAI (RA) – IDAN YA GA MUTUM AHLUS SUNNA SAI YA HALATTA JININSA.
DUBA AL- KHI’DA’DA NA MAK’RIZIY, 2/ 341. DA TARIKHUD DAULATIL FA’DIMIYYA SHAFI NA 620. DA WAFIYYATUL A’AYAN 3/ 110.
KAFIRCIN UBAIDIYYUNA (RAFIDA BA’DINIYYA) WA’DANDA SUKA K’IRK’IRI MAULIDI:
WANI ABU DA YA FI DUKKAN ABIN DA MUKA AMBATA A BAYA SHI NE; AL- HAKIM SARKIN DAULAR FA’DIMIYYA, YA YI DA’AWAR CEWA; SHI ALLAH NE. SUBHANALLAH!! SAI YA UMURCI MUTANE DA SU TASHI SU TSAYA DA K’AFAFUNSU A CIKIN SAFUN SALLAH, A LOKACIN DA MAI HU’DUBA YAKE HU’DUBA IDAN YA KIRA SUNANSA. DON GIRMAMA AMBATONSA DA SUNAN NASA. KUMA HAKA YA SA AYI A DUKKAN MASARAUTAR TASA. HAR A HARAMAINI (MAKKA DA MADINA). AMMA YA WARE MUTANEN MISRA YA UMURCE SU DA SUNA FA’DUWA K’ASA SU YI SUJADA, IDAN AN KIRA SUNAN NASA. HAR YA ZAMA MUTANEN DA SUKE KASUWA MA WA’DANDA BA SA ZUWA JUMA’A SUKAN FA’DIN SU YI SUJADA IN NA CIKIN MASALLACIN SUN FA’DI, IN MAI HU’DUBAN YA AMBACI SUNAN NASA, A RANAR JUMA’A. HAR AN SAMU WASU JAHILAN IDAN SUN GAN SHI SAI SU CE: YA WAHIDANA, YA AHADANA, YA MUHYI, YA MUMITU. SA’ANNAN YA UMURCI BAK’AK’E DA SU K’ONA MASAR, SU WAWASHE DUKIYOYINTA, DA KAYAYYAKI, DA MATA. KUMA SUKA BI UMURNIN NASA, SUKA KAMA MATA SUKA YI TA ALFASHA DA MUNANAN AIYUKA DA SU. SUKA K’ONA ‘DAYA BISA 3 MISRA SUKA WAWUSHE RABINTA.
DUBA AL- BIDAYA WAN NIHAYA (12/ 10 – 11), DA AL- MUNTAZIM (7/ 298).
A BIYOMU AKWAI CIGABA, INSHA ALLAHU.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “MAULUDI BA ADDINI BANE!!! BID'AH CE”
  1. Ahmad Yusuf Assqalaini Avatar
    Ahmad Yusuf Assqalaini

    Malam, ba dai mauludi ba? To “KADAN KENAN” (is just the biginning)

Leave a Reply

Categories
Latest updates