Ramadan(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe

Danna nan domin shiga karatu Online

Ramadan Mai Yawan Albarka
MA’ANAR AZUMI MA’ANAR azumi
a yaren Larabci, shi ne kamewa
daga barin ko mene ne, kuma akan
yi amfani da kalmar a kan kowane
irin kamewa, kamar yadda (SWT)
ke bada labari a kan Maryam (AS),
inda take cewa, lallai ni na yi
alwashi ga Allah mai rahama zan
yi azumi (Suratul Maryam 26).
Ma’anar azumi a shari’a, shi ne
kamewa daga abubuwan da suke
sanya cin abinci ko karya azumi
daga bullowar alfijir zuwa fa]uwar
rana tare da niyyar bautar Allah
mai girma da ]aukaka.
Azumi yana daga cikin mafi girman
da’a da kusaci da Allah mai tsarki,
kuma Allah Yana bada lada wanda
ba shi da iyaka ga mai yin shi, da
shi (azumi) ake yin gafarar
zunuban da suka gabata, kuma
Allah Yake nisanta fuskar mai yin
shi daga barin wuta, kuma yake
cancantar da shigar shi aljanna.
FALALAR AZUMI DA
FA’IDOJINSA
1. An karbo daga Abu Huraira
(Allah Ya yarda da shi) ya ce, lallai
Manzon Allah (SAW) ya ce, Allah
mai girma da daukaka ya ce,
dukkan ayyukan ]an Adam nasa
ne, amma ban da azumi, domin
azumi nawa ne, kuma ni ne zan yi
sakayya domin azumi garkuwa ne,
duk ranar da mutum yake yin
azumi baya zina, baya daga
murya, kuma ba ya yin wauta don
idan wani ya zage shi, ko ya neme
shi da fa]a lallai ya ce, ni ina yin
azumi (sau biyu) Manzon Allah
(SAW) ya ce, na rantse da wanda
raina yake hannunsa, warin bakin
mai azumi ya fi kamshi a wajen
Allah ranar kiyama daga kamshin
turaren Almiski, kuma mai azumi
yana da farin ciki guda biyu da zai
yi farin ciki da su, lokacin da yake
yin buda baki, zai yi farin ciki da
lokacin da zai hadu da Ubangijinsa
zai yi farin ciki da azuminsa.
(Bukhari ya ruwaito hadisi na 1904
da Muslim Hadisi 1151).
2. An karbo daga Sa’ad dan Sa’ad
(Allah Ya yarda da shi) ya ce,
Manzon Allah (SAW) ya ce, lallai a
cikin aljanna akwai kofofi guda
biyu ana kiransu da suna Arrayyan,
babu wanda zai shige su sai mai
azumi, babu wani wanda zai shige
su sai su (wato masu azumi). Za a
ce ina masu azumi? Sai su mike,
sai a ce babu wanda zai shige ta
wanda basu ba, idan suka shiga
sai a rufe kofar aljannar. Ba mai
shiga wannan }ofa ta Arrayyan sai
masu azumi, (Bukhari ya ruwaito
hadisi na 1896 da Muslim Hadisi
1152).
3. An karbo daga Abu Huraira
(Allah Ya yarda da shi) ya ce,
Manzon Allah (SAW) ya ce, duk
wanda ya azumci watan
Ramadana yana mai imani, yana
mai neman lada, to, an gafarta
masa zunubansa wanda ya
gabatar (Bukhari ya ruwaito hadisi
1900 da Muslim 760).
AZUMI YA KASU KASHI BIYU
* Akwai azumi na wajibi (dole ke
nan).
* Akwai azumi na nafila.
Azumi na wajibi wanda yake dole
shi ma ya rabu kashi uku.
* Akwai wanda yin shi dole ne, a
wani lokaci ayyananne, shi ne
watan Ramadana.
* Akwai wanda yake dole ne
saboda wani (illa), wato dalili
wanda yake wajabta, kamar
kaffarar zihari, ko na kisan kai a
kan kuskure, ko na rantsuwa da
sauransu.
* Akwai wanda yake wajibi ne
mutum ya lizimta wa kansa yin
azumi (kamar alwashi).
AZUMIN WATAN RAMADANA
Hukuncin yin azumin watan
Ramadana wajibi ne kowane
Musulmi baligi, mai hankali
lafiyayye mazaunin gida, kuma
rukuni ne daga rukunen Musulunci,
littafin Allah (Alkur’ani) da sunna
sun tabbatar da haka, har da
ijima’in malamai.
Allah mai girma da ]aukaka ya ce,
ya ku wa]anda suka yi imani, an
wajabta azumi a kanku kamar
yadda aka wajabta wa wa]anda
suka gabaceku ko kwa ji tsoron
Allah. (Suratul Bakara 2 aya ta
183).
Manzon Allah (SAW) ya ce, an
gina Musulunci a kan abubuwa
guda biyar, Shaidawa babu abin
bautawa da cancanta sai Allah,
kuma Annabi Muhammadu (SAW),
Manzon Allah ne da tsayar da
Sallah da bayar da Zakkah da
kuma aikin Hajji da Azumtar watan
Ramadana. (Bukhari ya ruwaito shi
Hadisi na 8, da Muslim Hadisi na
16 daga Abdullahi ]an Umar, Allah
Ya yarda da shi).
Wani Balaraben }kauye ya zo
wajen Manzon Allah (SAW) kanshi
a cukurku]e, ya ce, ya Manzon
Allah (SAW) bani labarin abin da
Allah ya farlanta a kaina na azumi,
sai Manzon Allah (SAW) ya ce
azumin watan Ramadan, sai dai
kuma in ka so ka yi azumin nafila
(Bukhari ya ruwaito shi Hadisin na
50 da Muslim Hadisi na 9, daga
dalhatu ]an Abdullahi, Allah Ya
yarda da shi).
Lallai Ha}i}a malaman Musulunci
sun yi ijima’i a kan cewa, azumi
rukuni ne daga cikin rukunen
Musulunci, sanannu a cikin addini,
to, inda suka ce ana iya kafirta
wanda duk ya yi musun azumtar
watan Ramadan, kuma azumin
baya fa]uwa a kan kowane
balagagge mai hankali, sai dai da
wani uzuri daga uzurorin shari’a,
wacce take abin lura (Al-Ifsah na
Ibnu Hubaira) Mujalladi na 1 shafi
na 232 da Al-Mugny na Ibnu
{uddama, mujalladi na 3 shafi na
285 da Al-Majmu’u na Imamun-
Nawawi, mujalladi na 6 shafi na
252).
FALALAR WATAN RAMADANA
DA YIN AIKI A CIKIN WATAN
An karbo daga Abu-Huraira (Allah
Ya yarda da shi) ya ce, Manzon
Allah (SAW) ya ce, idan watan
Ramadana ya shigo, ana bude
kofofin sammai, kuma ana rufe
kofofin wuta, ana kuma daure
Shaidanu (Bukhari ya ruwaito shi
Hadisi na 1899 da Muslim Hadisi
na 1079).
Daga Abu Huraira (Allah Ya yarda
da shi) ya ce, salloli biyar, daga
Juma’a zuwa Juma’a, da kuma
Ramadana zuwa Ramadana, suna
kankare abin da ke tsakaninsu,
idan sun nisanci manyan zunubai.
(Muslim ya ruwaito shi Hadisi na
233).Daga Abu-Huraira (Allah Ya
yarda da shi) ya ce, Manzon Allah
(SAW) ya ce, dukkan ayyukan dan
Adam na shi ne sai dai azumi
nawa ne. Kuma ni zan yi sakayya
da shi (Bukhari ya ruwaito shi
Hadisi na 1904 da Muslim Hadisi
na 1151)
Babban Malami Abu Amr Ibnu
Abdulbarri Almaliyy (Allah Ya yi
masa rahama) ya ce, fadin Manzon
Allah (SAW) azumi nawa ne ni zan
yi sakayya da shi ya ce, wannan ya
isa falala ga azumi a kan sauran
ibadoji, sai dai ya ce malamai sun
yi sabani a kan abin da Allah
(SWT), yake nufi da azumi nawa
ne, ni zan yi sakayya da shi tare da
cewa, kowane aiki nashi ne (wato
Allah SWT), kuma shi ne yake yin
sakayya da shi, sun yi sa~ani mai
yawa (wato manyan malamai) na
farko, sun ce domin azumin riya ba
ta shiga cikinsa, kamar yadda yake
a cikin ayyuka. Imamul kurdubi
(Allah Ya yi masa rahama) ya ce,
da yake ayyukan riya tana shiga
cikinsu, to, amma azumi babu riya
a cikinsu. Domin shi aikin ana yin
shi ne tsantsar shi ga Allah (SWT)
shi ya sa Allah Ya jinginashi zuwa
gareshi (wato shi ne ya ce azumi
nawa ne, ni ne zan yi sakayya da
shi) (daga Asarabul Muhibbina Fi
Ramadan na Muhammad Hussaini
Yakub shafi na 18).
* Alhafiz Ibn Rajab Alhambali
(Allah Ya yi masa rahama), ya ce
malamai sun yawaita maganganu
a kan ma’anar fadin Manzo (SWA),
inda ya ce Allah (SWT) ya ce
azumi nawa ne zan yi sakayya da
shi.
Ya ce, malamai sun ce, lallai azumi
shi ne barin raba zuciya da
sha’awoyinta na asali, wacce Allah
Ya dabi’anceta a kan karkata zuwa
ga Allah (SWA) ya ce, ba a samun
wannan a sauran ibadoji sai dai
azumi kawai.
* Na biyu suka ce, lallai azumi sirri
ne tsakanin bawa da Allah (SWA)
babu wata ibada da ke da wannan,
kuma niyya ce ta boye, kuma ba
mai iya tsinkayar wannan sai Allah,
kuma ya bar sha’awarsa wacce a] abi’ance na al’ada, shi ya sa babu
riya a cikinsa ta inda mutum yana
barin abin da zuciyarsa take
kiransa zuwa gareshi na son
sha’awa babu wanda ke iya
tsinkayar wannan sai Allah (La] a’iful Ma’arif Na Ibnu Rajab
Alhambali shafi na 209-212).
Allah ya taimake mu tare da fatan
ya karbi ibadun mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

7 responses to “Ramadan(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe”
  1. Mal. Muhammad Haruna Kabiru Gombe, mun gode Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, ya kare mana kai amin.

  2. Nura senior Avatar
    Nura senior

    Slm don Allah kabiru gombe ka zama malamin sunnah na gaskia ba mai zagi da bata wasu ba sunnar annabi ba bu cin mutun ci acikinta

  3. usman saleh Avatar
    usman saleh

    Allah ya taimaki mallam, da fatan Allah ya baku ikon karfafa hadin kan musulmi ahlus sunnah….amin

  4. Idrismuhammad Avatar
    Idrismuhammad

    KABIR HARUNA,Allah yabada ladar niyya, Toyanzu dama kasan Qa’idojin musulumci biyarne kuma kuke qarawa da IZALA?, Tokasani madamar baka tubaba akan wannan mugunyar aqeedar taqaryar sunna to zaka tozarta tun’anan duniya. Kuma kasandai tunkamin kufara qaryar sunna malamanmu suke Qara shaidamana riqo da sunnar Annabi S.A.W,Kamar irinsu SHEIKH.JUNAID R.A,S.SAHL R.A,S.USMAN D/FODIO R.A,S.A.JIJJANI R.A KAIHARMA DA SHEIKHUL ISLAM MAULANMU SHK.IBRAHIM NIASS R.A.
    ALLAH YAKARYA MUNAFUKAN ADDINI BAKI DAYA.
    AMEEEN.

  5. rabiu alto Avatar
    rabiu alto

    asssalmu alaiukm Allah yaaimaki malam Allah yabar mana ku kuma akoda yaushe muna yi muku fatan Alkhairy akan Allah ya kara muku tsawon rai ku kara yada mana sunna

  6. Wlh good

  7. AHMAD ZUBAIRU Avatar

    aslm malam kabiru gombe muna fahinta yada kake yin wa’azi sosai mun san kanada makiya wamda basuson wa’azinka amma muna tayaka adu a..

Leave a Reply

Categories
Latest updates