RAYUWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA A CIKIN WATAN AZUMI → 06( Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Wallafar:
SHeikh Faisal Bn Ali Al- Ba’adani
Fassarar:
Dr. Mansur Ibrahim Sokoto da
Mal. Aliyu Rufa’i Gusau.
RAYUWAR ANANBI SALLALLAHU
ALAIHI WASALLAMA TSAKANINSA DA
UBANGIJINSA A LOKACIN AZUMIN
RAMALANA (2)
Babban abin da ya kamata musulmi ya
lura da shi a cikin wadannan nassosa
da suka gabata, shi ne kasancewar
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na
matuqar kwadayin jinkirta yin sahur da
kuma gaggauta yin budin baki, tare da
yin su da duk abin da ya sawwaqa
gare shi Sallallahu Alaihi Wasallama
komai qanqantarsa. Kamar yadda Anas
Raliyallahu Anhu ke cewa: “Ban taba
ganin Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi Sallar magariba kafin
ya buda baki ba; ko da kuwa da
kurbin ruwa guda ne sai ya yi.” Haka
kuma Abdullahi dan Amru Raliyallahu
Anhu ya ce, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Ku yi qoqari
ku yi sahur ko da da kurbin ruwa guda
ne.” Kaga kenan, ashe Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi
amfani ne da duk abin da ya tari
gabansa, don ya tabbatar da ganin ya
ba wa wannan ibada haqqinta, ba tare
da ya tsaya wata inda-inda ba. Don ya
qara samun fada ga Ubangijinsa mai
girma da xaukaka.
Yin nazarin wadannan bayanai da
suka gabata, na tabbatar wa mai
karatu da cewa, abin da wasu
musulmi ke yi yau, na yin “tazarce,” ko
yin sahur tun talatainin dare bai dace
ba, don ya saba wa koyarwar Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama, da abin
da gaba dayan Sahabbansa ke a kai
bayan sa. Kuma hakan na cutar da
rayuwa matuqa. Amru dan Maimun ya
bayar da labarin cewa: “Sahabban
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama
sun fi kowa gaggauta budin baki da
jinkirta sahur. Kuma hakan na qara
tabbatar da cewa, abin da wasu
mutanen ke yi a yau, na dibar girki da
shan gara a yi maqil lokacin sahur ko
budin baki, shi ma ya saba ma
wannan koyarwa ta Ma’aiki Sallallahu
Alaihi Wasallama. Domin kuwa irin
haka na haifar da kasala da dibgewar
jiki, ta yadda mutum ba zai sami
sukunin yawaita ibada a wannan wata
mai albarka ba. To, fita batun ma duk
wannan matsala. Babban bala’i duk,
bai fi irin wannan gara da ake
shiryawa ta zama an shirya ta ne da
dukiya ta haramun ba. Mutum yana ji
yana gani ya yi sahur da haramiya ya
kuma bude baki da ita, wal iyazu
billahi. Allah shi kiyashe mu.
Abin na da matuqar ban mamaki,
ganin irin yadda musulmi ke jefa
kansa cikin halaka; yana ganin hanyar
Aljanna ya kama ta Wuta. Maimakon
ya dage a kan cin halaliya da yawaita
ayyukan alheri da da’a a cikin wannan
wata, sai ya buge ga abubuwan da za
su kawai nisanta shi daga rahamar
Allah; su tara masa zunubbai su kuma
cika shi da rashin lafiya, irin wadda a
qarshen rayuwarsa ba abin da zai yi
sai nadama.
Da wannan muke kiran duk musulmi
mai hankali, da ya yi qoqari ya ja
lizzamin zuciyarsa, ya yi mata
dabaibayi, ya rage kwadayi da zama
kamar dabba. Ya tuna fa rayuwar
duniya mai qarewa ce, kuma yau da
gobe ba ta bar komai ba. Musulmi na
gari kuwa shi ne wanda ya gudanar da
rayuwarsa bisa koyarwar Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama
gwargwadon hali. Kuma kamar yadda
muka fada a baya, ba abin da qawace-
qawacen duniya da son jin dadi ke
haifarwa baya ga rafkana. Saboda
haka a rage kwadayi, a kuma riqe
ayyukan da’a da alheri, tare da
yawaita su, musamman a cikin watan
Azumin Ramalana.
2.2.1 Wasu Sigogi:
Tsakanin sahur da budin baki kuma
Azumin Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama na Ramalana ya qunshi
wasu sigogi kamar haka:
i- Addu’a: Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama kan yi addu’a a duk
lokacin da zai yi budin baki. Dan Umar
Raliyallahu Anhu ya ce: “A duk lokacin
da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama zai yi budin baki yakan ce:
“Qishirwa kuma sai ta gobe, ga kuma
abinci za mu ci, Allah ka ba mu ladar
da ke ciki.”
Amma abin takaici a yau, qanshin
abinci ya sa mutane da yawa,
musamman uwaye mata mantawa da
su yi addu’a, a lokacin budin baki.
Alhali kuwa babu wata addu’a da
musulmi zai yi a wannan lokaci face
Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya karbe
ta. Muna fatar za a kula a gyara.
ii- Asawaki: Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama kan yi asawaki a lokacin
Azumi. An riwaiyo daga Amiru dan
Rabi’ata Raliyallahu Anhu wanda ya
ce: “Na ga Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ban san iyaka ba yana
asawaki, yana kuma dauke da Azumi.”
Ba mamaki ko kadan a kan haka.
Domin kuwa ta tabbata cewa Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya
kwadaitar da musulmi yin asawaki
kusan kodayaushe, ta hanyar nuna
masu falalarsa, yana mai cewa:
“Asawaki na tsaftace baki ya kuma sa
mutum ya sami yardar Ubangiji.”
Sannan kuma shi ya ce: “Haqiqa an
umurce ni da yin asawaki, har na zaci
sai an saukar mani da aya ko wani
wahayi a kansa.”
Wadannan nassosa da suka gabata,
da wadanda za su biyo baya, na nuna
cewa Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama kan yi asawaki a kowane
lokaci a cikin yini, ba tare da
kebancewa ba, balle ya qi yin sa da
marece. Shi da kansa Sallallahu Alaihi
Wasallama yana cewa: “Ba don kada
in tsananta wa al’ummata ba, da na
umurce su da yin asawaki a lokacin
kowace arwalla.” Ya kuma ce a wani
Hadisin: “Ba don kada in tsananta wa
muminai ba da na umurce su da yin
asawaki a lokacin kowace Sallah.”
Malam Ibnu Abdilbarri ya ce:
“Wannnan Hadisi na nuna halaccin yin
asawaki a kowane lokaci. Saboda
cewa Annabi ya yi Sallallahu Alaihi
Wasallama, “……a lokacin kowace
arwalla da kowace Sallah.” Sallah
kuwa na iya kamawa a kowane lokaci,
ko da safe ko da rana ko da marece.”
Shi kuwa Imamul-Buhari qarfafa
wannan magana ya yi da cewa:
“Wannan halacci na yin asawaki a
kowane lokaci, ya hada har da mai
Azumi.” Bayansa kuma Ibnu Huzaima
ya qara da cewa: “Hadissan na nuna
cewa yin asawaki ga mai Azumi a
lokacin kowace Sallah abu ne da ke da
falala kamar yadda yake ga wanda ba
mai Azumi ba.” Saboda haka ya
kamata kowane musulmi ya kiyaye
wannan Sunnah ta Shugaban
Manzanni Sallallahu Alaihi Wasallama,
saboda lada da fai’da da ke cikinta ba
su qidayuwa.
Hadisin da ya tabbata Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a
cikinsa: “Warin bakin mai Azumi ya fi
soyuwa a wurin Allah, a kan qanshin
turaren Almiski.” ba zai tayar da
wancan hukuncin ba. Domin kuwa
ma’anar Hadisin ita ce bayyana cewa,
wannan doyi na bakin mai Azumi,
wanda mutane ke qyama, yana da irin
wannan matsayi a wurin Allah
Subhanahu Wa Ta’ala ta yadda har
qanshinsa a wurinsa ya kere na
almiski, turaren da ko a cikin mutane
sai wane da wane. Kuma doyin bakin
na mai Azumi ya sami wannan matsayi
ne a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala
saboda kasancewarsa sakamakon
biyayya ga umurninsa da neman
kusanta gare shi. Ba wai shi kansa
doyin ne ke da waccan daraja da
daukaka ba, balle hakan ta sa mutum
qoqarin samarwa da tabbatar da shi.
Iyakar abin da wannan Hadisi ke nufi
ke nan. Allah kuma shi ne mafi sani.
Sannan kuma babu wani nassi
ingantacce da ke nuna cewa Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallama ya
banbanta danye da busasshen itace a
cikin yin asawaki. Saboda haka da
yawan su, suka dauki nau’o’an itacen
daya, har Malam Ibnu Sirina ke cewa
wani mutun: “Babu laifi a cikin yin
asawaki da danyen itace.” Mutumin ya
ce masa: “Tsumagiyar dabino ce fa,
kuma tana da dandano.” Malamin ya
karba masa da cewa: “To, ai ruwa na
da dandano amma kuma kake kurkura
shi.” Shi kuwa Malam Ibnu Ulayyata
ya ce:” Yin asawaki Sunnah ne ga mai
Azumi, kamar yadda yake Sunnah ga
wanda ba Azumin yake yi ba. Kuma
danyen itace da busasshe duka daya
ne a ciki.”

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates