Siyasa ita ce fannin shugabanci,
shi kuma shugabanci ba a iya yin
sa sai cikin hikima da wayo da
dabara. Kuma mutane ba a iya
jagorantar su da zafi da kuma
tsanani. Saboda haka Allah –
sunhanahu wa taalah- ya gayawa
manzonsa tsira da amincin Allah
su tabbata a garesa:
ﻓﺒﻤﺎ ﺭﺣﻤﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻨﺖ ﻟﻬﻢ ﻭﻟﻮ ﻛﻨﺖ ﻓﻈﺎ ﻏﻠﻴﻆ
ﺍﻟﻘﻠﺐ ﻻﻧﻔﻀﻮﺍ ﻣﻦ ﺣﻮﻟﻚ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻬﻢ ﻭﺍﺳﺘﻐﻔﺮ
ﻟﻬﻢ ﻭﺷﺎﻭﺭﻫﻢ ﻓﻲ ﺍﻷﻣﺮ ﻓﺈﺫﺍ ﻋﺰﻣﺖ ﻓﺘﻮﻛﻞ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﻤﺘﻮﻛﻠﻲﻥ (159) ﺇﻥ ﻳﻨﺼﺮﻛﻢ
ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻏﺎﻟﺐ ﻟﻜﻢ ﻭﺇﻥ ﻳﺨﺬﻟﻜﻢ ﻓﻤﻦ ﺫﺍ ﺍﻟﺬﻱ
ﻳﻨﺼﺮﻛﻢ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻩ ﻭﻋﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻠﻴﺘﻮﻛﻞ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻮﻥ
(160) ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ .
“Sabõda wata rahama ce daga
Allah ka yi sanyin hali a gare su.
Kuma dã kã kasance mai hushi
mai kaurin zuciya, dã sun wãtse
daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu
laifinsu, kuma ka nẽma musu
gãfara, kuma ka yi shãwara da su
a cikin al’amarin. Sa’an nan kuma
idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka
dõgara ga Allah, lalle ne, Allah
Yana son mãsu tawakkali. (159)
Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu
marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya
yarɓe ku, to, wãnẽ ne wanda yake
taimakon ku bãyanSa? Kuma ga
Allah sai mũminai su dõgara.
(160)”
Idan ya kasance Manzon Allah
wanda yake zababbe ne kuma
horrarene daga wurin Allah aka ce
ma sa idan ya kasance mai zafin
rai da rashin tausayi, sahabbansa
duk za su tarwatse su gudu su bar
shi, ashe ke nan wadanda ba su
kai gare shi ba sun fi cancanta da
su saukaka wa kan su su bi
mutane da laluma da taushin hali.
Ba ya cikin hikimar da’awa da
kiran mutane zuwa ga alheri, nuna
dagawa, da isa da nuna
tsageranci da aikata wani abu da
sakamakonsa zai kai ga matsa wa
mutane da salwantar da dukiya da
ra sa rayukka. Wannan shine halin
da wadansu jama’a su ka tafi
akansa da sunan su masu gyara
ne
ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ، ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ، ﻗﺎﻟﺖ ﺍﺳﺘﺄﺫﻥ
ﺭﻫﻂ ﻣﻦ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻓﻘﺎﻟﻮﺍ ﺍﻟﺴﺎﻡ ﻋﻠﻴﻚ ﻓﻘﻠﺖ ﺑﻞ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﺎﻡ ﻭﺍﻟﻠﻌﻨﺔ
ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﻓﻴﻖ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺮﻓﻖ ﻓﻲ ﺍﻷﻣﺮ
ﻛﻠﻪ ﻗﻠﺖ ﺃﻭﻟﻢ ﺗﺴﻤﻊ ﻣﺎ ﻗﺎﻟﻮﺍ ، ﻗﺎﻝ : ﻗﻠﺖ ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ .
Wata rana wadansu yahudawa
suka ziyarci manzon Allah – Tsira
da Aminci su tabbata a garesa- da
suka shiga wurinsa sai suka ce:
Saamun ‘alaika (watau, mutuwa
akan ka) sai Aisha ta basu raddi
tace: Aa Mutuwar dai akanku da
kuma la’ana. Sai manzon Allah
yace: Ke Aisha, Allah mai laluma
ne kuma ya na son laluma ga
abubuwa dukkansu. Sai tace shin
ba kaji abin da su kace ba ne? Sai
ya ace: ai nace: kuma akanku.
Albukhari ya ruwaitu shi. A wata
Riwayar Monzon Allah yace:
ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺭﻓﻴﻖ ﻳﺤﺐ ﺍﻟﺮﻓﻖ . ﻭﻳﻌﻄﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺮﻓﻖ
ﻣﺎ ﻻ ﻳﻌﻄﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻨﻒ . ﻭﻣﺎ ﻻ ﻳﻌﻄﻲ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ
ﺳﻮﺍﻩ
“Lalle Allah mai tausayi ne kuma
ya na son laluma da tausayi.
Kuma ya na bayarwa ta hanyar
laluma da tausayi abin da baya
bayarwa tahayan sa karfi ko ta
wata hanya ba ta laluma ba.”
Ma’ana idan mutane na son wani
abu to su ne me shi ta hayan
laluma ba ta hayan sa karfi ba
balle ace ta hanyar ta’addanci da
zubar da jinni ko salwanta kudiya.
Sai mu roki Allah da Ya nuna
muna hanya mafita kuma ya hada
kanuwanmu. Amin.
Leave a Reply