Mai Rubutu :Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Date:November 6 2016
Ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah’, kamar hadithin Murrah wanda Ahmad da Haakim suka ruwaito, da hadithin Uthman Bin Abil Ass. Da kuma maganganun Malamai, kamar maganar Imam Ahmad Bin Hanbal, da Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah, da Imam Ibnul Qayyim dukkansu suna nuna yiwuwar maganar mutum da aljani ta harshen mara lafiya.
Babban Malami Sheikh Abdul Aziz Bin Baz shugaban majalisar Malamai ta kasar Saudiyya a lokacin da yake raye ya ce cikin lattafinsa mai suna Iidhaahul Haqqi Fii Dkhuulil Jinniyyi Fil Insiyyi shafi na 6-7 ((Aljani ya cakuda da sashin Mata Musulmai a Riyadh, sai sashin Malamai ya karanta (Alkur’ani) domin fidda shi, ya kuma tunatar da Aljanin (girman) Allah, ya yi masa wa’azi, ya kuma ba shi labarin cewa zalunci haramun ne, kuma zunubi ne babba, ya kuma kira shi zuwa ga Musulunci ya musulunta. Daga nan sai suka zo gurina da matar, na tambaye shi (shi Aljanin) dalilin da ya sa ya shiga cikinta, ya ba ni labarin dalilan, ya yi magana da harshen matar amma maganar maganar na miji ne ba maganar mace ba. (Hakan ya faru ne) alhalin tana cikin wata kujera da ke kusa da ni, dan’uwanta, da ‘yar’uwarta, da wasu sashin Malamai suna shaidar hakan, suna jin maganar Aljanin a lokacin da yake tabbatar da musuluncinsa a fili, na yi masa nasiha, na yi masa wasiyyar takawar Allah, da kuma cewa ya fita daga wannan matar, ya nisanci zaluntarta, ya kuma karba mini hakan ya ce: Ni na gamsu da Musulunci. Na yi masa wasiyyar ya kira jama’arsa zuwa ga Musulunci. Ya bar matar da aka ambata, karshen kalmar da ya hurta ita ce: Assalaamu Alaikum, daga nan sai matar ta yi magana da irin harshenta da aka saba (ji), ta kuma ji lafiyar jikinta da samun hutu daga gajiyar da ya sanya mata. Daga nan sai ta sake dawowa gurina bayan wata ta kuma ba ni labarin cewa tana cikin alheri da lafiya)).
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya taimake mu. Ameen.
Leave a Reply